A cikin kowace irin computer ko mai tsufanta komai sabuntar ta, ko da babu komai a cikinta, to akwai waɗansu application ko software da Operating system yake zuwa da su waɗanda suke da amfani matuƙa ga wanda ya san computer da ma wanda yake sabon shiga. A wannan ɗan takaitacce bayani za muyi ƙoƙarin nuna wa masu karatu yadda su waɗannan application suke, da kuma amfanin su, domin z aka ‘iya tsintar kanka a wata computer da ba a saka mata software da da ka saba amfani da su ba, ga shi kuma aiki ya kama ka to, waɗanne application kake buƙata domin ka gabatar da wannan aikin naka?
1. ADDRESS BOOK

Address Book shi ne na farko da zamu yi bayani a kanshi, domin kasancewar shi application ne da ake samu a cikin Windows Xp da Windows Vista da kuma Windows 7 wanda amfanin sa shi ne, ka sami damar da za ka tattara sunayen abokan hulɗarka da kuma kasuwancinka, kama daga sunayensu, da kuma adireshinsu da dai makamantansu.
2. NOTEPAD
Notepad wannan application ana kiranshi da ‘non editable text’ wato shi application ne da zai baka damar ka yi rubutu zalla ba tare da ka iya sa ka wani tsarin rubutu ba, ko kuma ka saka gyaran rubutu kamar ka saka shi ya yi kauri, ko ya lanƙwashe, ko ka saka layi a ƙasan shi. Shi ya sa shi wannan application ɗin ya ke da ƙarfin gudanar da dukkanin wani irin programming. Wato shi wannan application saboda ƙarfin da yake da shi programmer suke yin amfani da shi wajen yin programming ko kuma rubuta scripting language. Sannan kuma shi wannan application bayan ka gama rubutu a cikinsa idan ka zo ajiye shi, sai ka zaɓi wani application ka ke son ka buɗe da shi a nan gaba.
3. WORDPAD

Shi wannan ɗan ƙaramin application da yana a matsayin “word processing software” domin kusan shi ne yake wakiltar MS Word a lokacin da babu shi a cikin computer. Ana amfani da shi kamar yadda kasan yadda ake amfani da word, zaka iya kaurara rubutu (bold), za ka iya lanƙwasa shi (italics) za ka iya saka layi a ƙasan rubutu (underline) haka zaka iya ƙara girman rubutu da canza wa rubutu launi da kuma canza tsarin yin rubutun. Haka kuma idan ka zo ajiye shi (saving) ka na da zaɓi, imma dai ya buɗe maka shi a Microsoft Word ko kuma ya buɗe a kowane irin word processing software.
4. PAINT

Shi kuma wannan application ana amfani da shi wajen yin zane-zane wanda a ƙarshe za a ajiye shi a matsayin hoto, wanda ya iya zane ‘drawing’ zai iya amfani da wannan ɗan ƙaramin software domin yin zanen hotuna na fure, yara da dai makamantansu. Sannan kuma za ka iya ajiyarsa da format kamar kala biyar.
5. WINDOWS MEDIA PLAYER

Ga wanda yake son ya saurari sauti ko ya kalli video a computer wannan application ana samun shi a kowace computer domin jin sauti (music) ko kuma kallon video. Sannan shi wannan application ana iya shirya ‘playlist’ wanda kake son ka saurara kamar idan kana son ka saurari karatun Alkur’ani daga farko zuwa ƙarshensa wanda ba ka son karatun ya yanke, ba kuma ka son a ce sai ka sake kiran sura ta gaba kafin ya ci gaba.
Comment:Allah yakara basira da nisan kwana mai amfani malam,gaskiya ina matukar jin dadin wannan page domin nakaru da abubuwa marasa iyaka har sai da takai ga nasami nasarar karbar babbar hp computer kyauta daga wajen yayana.