23.5 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

2021: Aiki Gida da Ofis wuri daya da karancin Silicon – Abubuwa 10 mafi shahara a shekarar 2021

Shekarar 2020 ta kasance shekara mai cike da juyin juya hali a fannin fasahar sadarwa da bayanai, inda annobar COVID-19 ta tilasta duniya komawa ga fasahohin dijital cikin gaggawa. Daga amfani da manhajar Zoom, wacce yawan masu amfani da ita ya haura daga miliyan 10 zuwa miliyan 300, zuwa haɓakar amfani da Microsoft Teams da Google Classroom, an samu gagarumin sauyi a yadda ake aiki da koyarwa daga gida.

Haka zalika, amfani da sabis na Cloud Computing irin su AWS da Azure ya karu, yayin da Cybersecurity ta zama babban abin damuwa sakamakon yawaitar hare-hare. Kasashe kamar China da Korea ta Kudu sun ci gaba da shimfiɗa 5G, yayin da AI da Automation suka taka muhimmiyar rawa wajen gano cututtuka da sarrafa bayanai. Siyayya da biyan kuɗi ta intanet da kuma lura da Harkar Lafiya ta intanet (Telemedicine) sun kara samun karbuwa, duk kuwa da matsalar banbanci wajen samun ingantaccen intanet – musamman a yankunan karkara.

Wadannan canje-canje na 2020 sun zama tubalin da aka gina sabbin dabaru da ci gaba a kansu a shekarar 2021, kamar yadda fasahar hybrid work, karfafa tsaro, ingantaccen amfani da girgije, da kuma faɗaɗa 5G suka ci gaba da bunƙasa cikin sabon salo.

Ga yadda shekarar 2021 ta kasance da abubuwa da suka fi daukar hankali a cikin shekarar

AI & Automotion: ayyuka sun koma hadaka tsakanin gida da ofis a wannan shekarar kasancewar kowa zai iya aiki a duk inda yake so, saboda karin samun kayan aiki masu amfani da fasahar AI kamar irin su Salesforce Einstein da kuma kananan manhajoji irin su Bubble da Retool.

A gefe guda kuwa ‘yan dandatsa da masu kutse (Hackers) suna kara samun karfi kasancewar mafi yawan ayyuka a lokacin ana yin su ne a intanet, kuma mafi yawan ayyukan da ake yi ajiye sune a cikin manya manyan servers saboda haka ake samu yawan farmaki irin na Ransomware (masu garkuwa da na’urorin mutane) domin a biya su kudi, wanda hakan ya sanya manyan kamfanoni suka kirkiro da tsarin Zero Trust a wannan shekarar.

A bangaran Hadware a wannan shekarar ta 2021 kamfanoni da suke kirikirar na’urorin kwamfutotci musamman kwamfutoci da ake musu zubi mai karfi wacce ake kira da Gaming PC suka baza komarsu wurin kirkirar sababbin na’urori masu karfi, kamar kamfani Dell ya kirkiri kwamfuta da ake kira da PS5 a wannan shekarar.

Haka shima kamfanin Samsung ya kirkiri tashi mai suna XPS 13 haka a wannan shekarar ta 2021 ya fito da wayar Galaxy S21 Ultra mai karfin 108MP a daukar hoto. Saboda haka karancin kayan da ake kirkirar irin wadannan hardware ya sanya sai da kamfanoni suka tashin farashin har zuwa $210B.

A cikin wannan shekarar ne aka samu habakar Green Computing wanda hanya ce kamfanonin da suke kirkiran kayayyakin kwamfuta suka bi wurin ganin sun rage dumamar yanayi da kuma rage jan wutar lantarki da kashi 4% inda suka samar da hanyar amfani da ruwa domin sanyaya kayansu da kuma amfani da hanyar samar da wutar lantarki ba tare bata yanayi ba (renewable energy).

Ga jerin abubuwa masu muhimmanci guda 10 da suka faru a shekarar 2021

2021 – Gawurtar Digita da Canjin Tsari na Aiki

  1. Gina Tsarin Aiki na Hade (Hybrid Work Infrastructure) – Kamfanoni sun koma tsarin aiki daga gida da ofis lokaci guda.
    Misali: Microsoft ta kara sabbin hanyoyi masu amfani da hadin gwiwa a Microsoft Teams domin tallafa wa aikin gida da ofis a wuri guda.
  2. Cybersecurity Prioritization – Hare-haren yanar gizo kamar SolarWinds sun nuna raunin tsaron bayanai da ake da su a duniya.
    Misali: Hare-haren ransomware sun hana aiki a kamfanin bututun mai na Colonial Pipeline, sun jawo karancin mai.
  3. Bunkasar Girgijen Intanet (Cloud Maturity) – Kamfanoni sun zurfafa amfani da tsare-tsaren na ma’ajiyar intanet (Cloud Storage).
    Misali: Netflix ta faɗaɗa cibiyarta don sauƙaƙe isar da fina-finai da shirye-shirye.
  4. Sabbin Dabarun Haɗin Gwiwa daga Nesa (Remote Collaboration 2.0) – An inganta kayan aiki domin ci gaba da aiki daga ko’ina mutum yake a fadin duniya.
    Misali: Slack ta ƙara sababbin abubuwa kamar kiran bidiyo da na murya.
  5. Ci gaba da Fadada Sadarwar 5G (5G Expansion Continues) – Faɗaɗar cibiyar sadarwa ta 5G ta inganta ayyukan wayoyin salula da na’urorin IoT.
    Misali: Verizon ta faɗaɗa sabis ɗin 5G Ultra Wideband a Amurka.
  6. Ci gaban Biyan Kuɗi ta Intanet tare da Bunkasar Fintech (Digital Payments & Fintech Growth) – Mutane suka aminta da amfani da kudaden dijital da walat na intanet.
    Misali: Kamfanonin Square (Block) da Stripe sun samu gagarumar riba.
  7. Aikin Atomatik da RPA (Automation & RPA) – Kamfanoni sun fara amfani da mutum-mutumi na bots don yin ayyukan ofis da suke bukatar maimaituwa.
    Misali: UiPath ta zama shugaba a fannin RPA (Robotic Process Automation).
  8. Yarda da Harkar Lafiya ta (Telehealth and eHealth Adoption) – An haɗa bayanan marasa lafiya da tsarin AI don tantance lafiyarsu.
    Misali: Babylon Health suna amfani da fasahar AI wurin duba marasa lafiya.
  9. Faɗaɗa Amfani da IoT a Masana’antu (IoT Growth in Industry) – Amfani da IoT wajen sa ido da kula da ayyukan masana’antu.
    Misali: John Deere na amfani da IoT cikin taraktoci domin inganta nomansa.
  10. Karancin Kwararru a Fannin IT (Tech Talent Gap Emerges)
    – A shekarar an samu karancin kwararru a fannin IT saboda bukatuwarsu ta yi yawa.
    Misali: Kamfanonin Google, Amazon da Apple sun gudanar da gagarumin ɗaukar ma’aikata.
  • Kirkirar Shekara: kayan aiki daga gida
  • Mafi Kyawun Waya: Samsung Galazy S21 Ultra.
  • Mafi Kyawun Kwamfuta: Dell XPS 13
  • Mafi kyawun Manhaja: Microsoft Team
  • Mafi kyawun Programming Language: JavaScript tare da Next.js.

Wadannan shine a takaice abinda zamu iya kawo muku, akwai abubuwa dama da suka faru a wannan shekarar ta 2021, amma a harkar IT lallai wadannan sune abubuwa guda 10 mafi shahara.

Da fatan an karu! Se mun hadu a shekarar 2022

4 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img