23.5 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

Abubuwa muhimmai guda 10 da suka kubucewa mai karatu a shekara 2023 – Generative AI Ta Zama Tauraruwa

Shekarar 2022 ta kasance shekara mai cike da ci gaba a fannin fasahar zamani, musamman wajen amfani da Artificial Intelligence (AI) a ayyukan yau da kullum. Manyan kamfanoni sun haɗa AI cikin tsarin kasuwanci da tallace-tallace. Haka kuma an fara amfani da Edge Computing, wato sarrafa bayanai a kusa da inda ake bukata don rage jinkiri, musamman a masana’antu da masana’antun kere-kere.

Tsarin Cloud-Native da amfani da containers kamar Kubernetes sun bai wa kamfanoni damar girka ayyukansu cikin sauki da sassauci. A bangaren tsaro kuwa, Cybersecurity Mesh Architecture ya taimaka wajen kare bayanai a cikin hadadden tsarin girgijen yanar gizo.

A 2022 ne kuma aka ga yawaitar amfani da SaaS (Software as a Service) a fannoni kamar noma, lafiya da kudi, tare da amfani da blockchain wajen tabbatar da gaskiya da bin diddigin kayayyaki. Low-code da No-code tools sun bai wa marasa fasahar coding damar gina aikace-aikacen su cikin sauki.

Daga karshe, fasahar kare muhalli (Green Tech) da ci gaban Smart Cities sun karfafa matsayin fasaha a gina birane masu kaifin basira da inganta rayuwar jama’a.

Wannan ci gaban ne ya dora mu kan hanyar shekarar 2023 wadda ta kawo sabbin kalubale da karin kirkire-kirkire a duniyar ICT.

AI Ko’ina: ChatGPT-4 ta zama app ɗin da ta fi kowacce sauri in da ta samu masu amfani da ita fiye damiliyan 100 cikin watanni biyu kacal. A wani bangaren, GitHub Copilot ya rubuta kusan kashi 40% na surkullen kirkirar software na coders. Sai dai, kamfani Microsoft ya fuskanci suka yayin da cibiyoyin da yake kirkirar AI suka kara gurbata yanayi da kashi 30%.

Sabbin Kayan Aiki Masu Kyau: NVIDIA H100 GPUs sun bunkasa AI (LLMs) ƙarfi, yayin da Google Pixel 8 Pro ta nuna fasahar ta a wurin daukar hoto ta AI. A gefe guda kuma, dokar DORA ta Tarayyar Turai (EU) ta tilasta kamfanonin kamfanoni masu hada-hadar kudi da su gwada kwanjinsu domin tabbatar da karfin kariyarsu akan abinda ya shafi hare-haren intanet.

Fasahar Lafiya: Na’urorin agogon hannu kamar Apple Watch 9 suna iya gano matsalolin bugun zuciya, sannan AI ta ragewa likitoci wahala da 50% na gane cututtuka a bangaran hoton cututtuka (radiologists).

📅 2023 – Daukakar Generative AI

  1. Dauakakr Generative AI – – Ayyukan kirkirar, zane zane, da software sun sauya gaba daya.
    🧠 Misali: A cikin watanni biyu kacal sai da sama da mutane miliyan 100 suke amfani da manhajar ChatGPT .
  2. AI a Aikin Masana Ilimi – Ya taimaka wajen rubuce-rubuce, coding, nazarin shari’a da aikin zane.
    🧑‍💻 Misali: GitHub Copilot yana taimakawa masu kirkirar manhajoji wajen rubuta code cikin sauri.
  3. Abubuwa na gaskiya da kuma Deepfake – – Sababbin kayayyakin aiki sun bayyana wanda ake iya gane abu mai inganci ko mara inganci.
    📷 Misali: Adobe Content Credentials na amfani da tambarin dijital (digital watermark), domin gane cewar wannan abun na asaline ko anyi amfani da manhaja ne wurin kirkirar shi.
  4. Kwarewar Keɓantaccen Abubuwan Zamani – Wannan tsarin na taimakawa mutane wurin fahimtar abubuwa da kuma basu shawarwarin akan abu.
    📺 Misali: Netflix na amfani da AI don tsara hoton fim da rabon jinsin fina-finai.
  5. Noman Fasaha (Smart Agriculture)—Tace ruwa kaitsaye da AI, feshi da jirgi mara matuki, da kuma yin kididdiga nan take.
    🌾 Misali: CropX na hade da na’urori da AI don inganta noma.
  6. Nazari ta hanyar AI (AI-Driven Analytics) – Kamfanoni na hango al’amura da yanke shawara ta hanyar amfani da AI.
    📊 Misali: Tableau da Power BI sun hade AI don fitar da hasashe.
  7. Bayyanar Digital Twins – Kwafin na’ura na ainihi a duniyar dijital don yin gwaji kafin aiwatarwa.
    🏭 Misali: Siemens ta kirkiro digital twins don tsara masana’antu.
  8. Manhajojin Rarraba Bayanai (dApps)—Aikace-aikacen Web3 sun baiwa masu amfani iko akan bayanansu.
    💱 Misali: Uniswap yana baiwa mutane damar yin musayar kudin crypto ba tare da wani a tsakiya ba.
  9. Augmented Reality (AR Tools)
    – Ana amfani da su a bangare ilimi, lafiya da kasuwanci.
    🛋️ Misali: app din IKEA Place yana nuna kayan daki yadda za su kasance a gida kafin saye.
  10. Hadin gwiwar kayan aiki tsakin su (Cross-Platform Integration)
    – Na’urori na aiki tsakanin junansu koda basu kasance iri daya ba.
    📱💻 Misali: Apple Continuity na baiwa masu amfani da su juyawa tsakanin na’urori ba kowane lokaci.

Kirkira Mafi Girma na Shekara: ChatGPT + Generative AI
Mafi Kyawun Waya: Google Pixel 8 Pro
Mafi Kyawun Kwamfuta: MacBook Pro M2
Fitaccen Software: ChatGPT
Salon Shirye-shiryen Kwamfuta na Shekara: Manhajojin AI da suke taimakawa wurin rubuta surkullen kwamfuta sun dama gamagari

Wadannan sune a takaice abinda zamu iya kawo muku. Akwai abubuwa dama da suka faru a wannan shekarar ta 2023, amma a harkar IT lallai wadannan sune abubuwa guda 10 mafi shahara.

Da fatan an karu! Se mun hadu a shekarar 2024

4 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img