Kowane irin dandalin sada zumunci (Social Network) yana da yadda ya tsara mutane su riƙa yin amfani da shi, sannan kuma yana da hanyoyin da ya tsara domin jin ɗaɗin masu amfani da shi. Twitter dandalin sada zumunci ne wanda ya banbanta da sauran dandali kamar su facebook. Domin Twitter ana danganta shi da microblogging. Microbologging shi ne duk wani dandalin da ake amfani da shi domin aikawa da ɗan ƙaramin saƙo da ba bai wuce haruffa 140 ba. Sannan kuma shi Twitter yana buƙatar lokaci na zahiri domin faɗa wa waɗanda suke biye da kai halin da kake ciki ko kuma wani abu da yake faruwa da dumi-duminsa.
Shi ya sa twitter wuri ne da yake baka damar sadar da zumunci ta hanyar sanar da mutanen da suke biye da kai halin da ake ciki domin tabbatar wa da mabiyanka da kuma abokan huldanka abubuwan da kake ciki ko kuma kake buƙatar ka sanar da su, ko kuma suke buƙatar ka sani.
Yin amfani da twitter abu ne mai ban sha’awa, kuma ka sani cewar twitter kyauta ake amfani da shi, sai dai idan mutum bako ne, to zai samu cewar twitter yana da ɗan rikitarwa ko kuma yana da wahalar yin amfani. Amma kada ka damu, da ɗan ƙaramin bayanin da za mu yi maka zai taimaka matuka wajen warware maka zare da abawa a kan abin da ya shafi wannan dandali na twitter. Wanda a ƙarshe idan Allah ya yarda kai ma za ka zama gwani a wurin amfani da shi, ko kuma ka zama ka san shi daidai da yadda kai ma za a iya kiran ka a matsayin gwani.
Wannan karatu mun tsara shi mataki bayan mataki tare da hotuna ta yadda idan mai karatu ya bi su za mu nuna mishi hanya ta farko zuwa ta ƙarshe da ya kamata ya sani a wurin yin amfani da twitter.
Mataki na 1: Kirkirar Gida (Account) a Twitter
Buɗe burausarka (browser) ka rubuta www.twitter.com sannan ka cike shafin farko da ya buɗe maka inda aka rubuta ‘sign up’ domin yin haka shi ne zai baka gida a cikin twitter da kai ma za ka riƙa aikawa da sakwanninka zuwa ga abokan huldanka.
Abin da ake buƙata ya kasance kana da shi lokacin da za ka buɗe account da twitter shine Sunanka, imel ɗinka, kalaman sirri domin shiga (password). A waɗannan ramukan da ka samu a lokacin da ka buɗe wannan shafi.
FAHIMCI SURKULLEN TWITTER DOMIN YIN AMFANI DA SU INDA SUKA DACE
Kafin mu tsunduma a mataki na gaba yana da kyau mu yi wa mai karatu bayani akan kalaman da ake amfani da su a twitter da kuma wurin da ake amfani da su domin mai karatu ya fahimce su ya kuma san inda ya dace ya yi amfani da su.
Tweet – Idan ka ji an ce tweet shi ne sakon da ka rubuta a ramin Twitter bayan ka buɗe shafinka na twitter. Shi wannan tweet yana daukar harrufa 140 wanda za ka iya haɗawa da kowane irin harafi ko alamomi. Sannan za ka iya haɗawa da sunan wani da kake son ka yi magana da shi kai tsaye ta yin amfani da alamar @ sannan ka saka sunan shi misali @DuniyarKwamfuta. Yin haka yana nuna cewar wannan maganar kai tsaye kana yin ta ne da shafin Duniyar Kwamfuta da ke dandalin Twitter.
Retweet ko “RT” – Wannan wata hanya ce da ake bi idan kana son ka kwafi abin da wani cikin masu biye da kai ya yi kai ma ka saka a cikin naka shafin. Yin haka zai ba waɗanda suke biye da kai damar ganin abin da ka ɗauko daga wurin wani zuwa naka shafin. Yin haka kuma na kara jawo mabiya ga shafinka na Twitter. Koda yake idan mutum ya yi Retweet zai nuna wa sauran mutanen sunan wanda yake da asalin rubutu da kuma hanyar da za su bi idan suna son su shiga asalin rubutu.
Trending Topics (TTs) – ‘Trending topics’ na nufin kalamai ko kuma darussa da aka fi yin tweet na su. Su ana ganinsu ne a jere a gefe. Lokacin da Twitter suke farko Trending Topics kamar bayanai ne na waɗanda suka fi kowa amfani da twitter a makon da ya wuce. Amma a yanzu ana amafani da Trending Topics wurin sanin mene ne abin da mutane suka fi tattaunawa a kansa, ko kuma maudu’in da mutane suka fi bi. Trending Topics a yanzu shi ne abin da dubunnan mutane suke magana a kanshi a lokaci guda. Idan kuwa ka latsa kalmar TTs ɗin zai buɗe maka shafi na daban wanda zai bijiro maka da wannan kalmar da kuma inda aka sakata har guda uku. Za ka ga guda uku a sama sannan kuma ka ga kamar 150 wanda waɗansu suka yi retweet dinsu.
Lists – Lists wata hanya ce da mutum yake bi a twitter domin tsara mutanen da yake son ya danganta su da wani abu guda. Kamar mutum zai iya shirya list na mutanen da yake son su riƙa bin abin da yake magana wanda ya shafi wani abu na daban. Kamar ka shirya list na waɗanda za ka turawa maganar da ta shafi Kwamfuta da dai makamantansu.
Promoted Tweets – Shi ne hanyar da kamfanoni suke bi domin a watsa musu abin da suka yi tweet na shi. Shi ‘Promoted Tweets’ biya ake yi domin a kai shi sakon nasu lungu-lungu na dandalin twitter. Yin hakan (biya) zai kara wa shi shafin nasu mabiya masu yawa a duniya baki ɗaya.
MATAKI NA 2: Yin Rubutu a Twitter
Tweet. Idan kana son masu biye da kai su san abin da kake ciki sai ka yi rubutu a wurin da aka rubutu ‘What’s happening’. Bayan ka gama rubutawa sai ka latsa maɓallin da aka rubuta tweet. Yin hakan zai ba mabiyanka damar sanin me kake ci. Amma kamar yadda muka faɗa a baya cewar haruffa 149 kawai wannan ramin yake iya ɗauka. Idan ka yi rubutun da ya wuce 140 to ka sani sakonka zai je a gutsire.
A daidai lokacin da kake rubutu akwai daga kasan shi wannan gida zai riƙa rubuta adadin haruffa da ka zuba mishi. Haruffan da aka yarda da su za ka ga launin shi kidayar yana kirga su da ruwan toka, da zarar haruffa sun rage saura 10 zai koma launin ja, idan kuwa ka wuce haruffa 140 zai sa maka alamar cirewa (- minus).
Mataki na 3: Amfani da Hash (#)
Yin amfani da alamar Hash (#). Duk kalmar da ka ga an haɗata da alamar ‘Hash’, to kalma ce da aka bata mahimmanci ko kuma ta zama darasin da a ke magana akai. Saboda haka idan kana son ka ayyanar da wata kalmar a cikin rubutunka wanda kusan kowa yana magana a kansa, to kai ma za ka iya rubuta alamar Hash a jikin shi. Misali kamar kana son ka yi magana a kan Economy kuma kana son idan mutum ya shiga dakin bincike na twitter yana son ya san me mutane suke cewa game da Economy to sai ka sa Hash a like da shi ka rubuta Economy (#Economy).
Waɗansu muhimman darussan (Trending Topics) ana ganin alamar Hash tare da su, yin hakan shi ke kawo sauƙi ga wanda yake son ya bi wannan darasi samun sauƙi.
Mataki na 4: Samun Mabiya (Followers)
Samun Mabiya. Ya danganci manufar da kake da ita a lokacin da ka buɗe account a twitter. Idan ka buɗe account na twitter domin ka sami mabiya masu yawa to dole ka kiyaye abubuwan da za ka saka musu. Abubuwan da za ka saka musu ya kasance abu ne mai jawo hankali da kuma son kowa ya ji shi. Kada ka raina bin wani domin sau tari duk wanda ka bi shi ma zai biyo ka. Da yin haka zai sa ka tara mabiya. Yadda ake yi kuwa shi ne za ka ga kalmar ‘Follow’ idan ka shiga shafin mutum, wannan maɓalli shi za ka latsa domin ya gaya wa shi wancan mai shafin cewar wane yana son ya riƙa bin ka. To, da haka duk abin da ka tweet ɗin shi wancan zai gan shi, kuma mutanen da suke biye da shi za su gan ka. To, idan ya so shi ma zai latsa maɓallin da yake gefen rubutunka wanda aka rubuta Follow to shi ma daga nan zai fara bin ka. Wani lokaci za ka iya yekuwa ga waɗanda suke bin ka ta yin amfani da twitter kai tsaye ko kuma ta yin amfani da shafinka ko kuma ta hanya mai sauƙi ta yin amfani da abin da ake kira (#FollowFriday). Wannan wata hanya ce da za ka tweet wasu da ga cikin manyan mabiyanka ta amfani da #FF domin tunanin cewar mutane ka iya yin sha’awar bin su su ma. Yin haka zai kara daukaka sunanka domin zai kai tsawon mako guda sunanka na zagaya shafuka daban-daban.
A wani lokaci yin retweet (RT) shi ma yana kara kawo mabiya a cikin shafin mutum, domin yin retweet kamar yadda muka faɗa a baya hanya ce da ake amfani da ita wajen sake watsa abin da wani ya rubuta ya koma shafinka.
MATAKI NA 5: BAYAR DA AMSA A KAN ABIN DA AKA YI MAKA
Yana da kyau a koda wane lokaci ka riƙa duba abin da mabiyanka suka aiko maka da shi kai tsaye zuwa gare ka. Ka latsa maɓallin @Suna domin ka gani idan akwai wani wanda ya aiko da magana kai tsaye zuwa gare ka domin ka ba shi amsa. A lokacin da za ka yi tweet sai ka yi amfani da alamar @ sannan ka lika sunan mutum a jikin shi (ba tare da ka raba su ba), to wannan saƙo zai je kai tsaye zuwa ga mai sunan.
Misali ka rubuta @DuniyarKwamfuta wannan tweet da ka yi zai tafi kai tsaye zuwa ga duniyar Kwamfuta tare da wannan sunan da ka ambata.
MATAKI NA 6: ZABAR ADON DA YA DACE DA KAI
Yana da kyau kafin ka tsunduma cikin harkar twitter ka sani cewar sh ima twitter ɗaya yake da sauran shafukan sada zumunci, yana da cin rai da kuma cinye lokaci. Yana da kyau tun farko ka cire wa ranka son a ce kowa na biye da kai domin yin haka zai iya kawo maka matsala ta yadda za ka bi mutane da yawa amma kuma kai ka samu babu kowa mai bin ka.
Abin da kawai ya fi dacewa da kai ka damu da shi shi ne ka mayar da hankalinka wajen su wane ne ya kamata a ce kake bi. Haka kuma yana da kyau ka san su wane ne za su bi ka. Sannan kuma yana da kyau ka sani cewar yawan mabiya a twitter wanda suka wuce 150 zuwa 200 zai kasance kai kanka ka rasa inda za ka saka su mutukar dukkansu sun damu da tayin abin da kake rubutawa.
Allah ya kara basira ya biya bukata
Gaskiya duniyarkwanfuta naji dadin wanna bayani naku nadade ina amfani da tweet aman bantaba gamsuwa da jindadi ta kamar yanzu ba da nakaranta cikakken bayanin da kukayi nagode Allah ya karamaku fasaha.
Gskyane mungode sosai
Hakika wannan bayanin ya kara wayar mun da kai sosai. Allah ya saka da alheri.
Allah ya qara basira da ilimi. Ameen
Allah Ya saka da alheri.
Nagode Allah ya saka da alheri,
Tambaya me ya kamata mutum ya rubuta a inda aka sa, URL da BIO, a Twitter??
Inda aka saka BIO ana nufin Biography wata takaitaccen tarihinka zaka rubuta a wurin. Wurin da aka rubuta URL ya nufin Uniform Resource Locator wato idan kana da wani shafi da kake rubuce-rubuce ko website ana son ka saka layinsa. Wannan ba a twitter kadai ba duk inda ka ga irinshi a internet abin da ake nufi ke nan.
Duniyar Computer nagode kwarai da gaske, naga amsar tambayoyi na, Allah ya kara daukaka
Comment: thanks you much
Aslm,, tambaya ta a nan ita ce, Kamar nine nayi following din wani amman shi (wanda nayi following din) bai yi following back ba to idan nayi posting a twitter zai ga posting din koko sai idan har yayi following back? dan Allah ina bukatar amsa. NAGODe.