Symbian ta samu karbuwa ga mutane da dama, amma yanzu abin ba haka bane. Ayanzu na’uran Android suka ji ana yawan magana a kansu. Me karatu na iya tambaya me yasa haka? Meye dalilin da zai sa na sayi Android? Nakan ga irin wannan tambayoyin daga mutane daban-daban a yawancin lokuta. Amma har yanzu ban ji ko ganin wata kwakkwarar amsa ba da ta yi cikakken bayani game dalilin da ya sa Android suks fi Simbian.
Zan karfafa kan abubuwa guda biyu
a) Cewar akwai na’urorin Android Iri daban-daban a Kasuwa, amma ni zan yi magana ne akan irin waɗanda ake kiran su da suna High-end phones.
b) Su ma Symbian suna da nasu dalilan da za su iya bayarwa game da darajar wayoyin nasu da suka tura a dandalin su.
Saboda haka a nawa ra’ayin ga hujjojin da na ga Android na da shi.
- Saurin sarrafa kanta, saboda abin sarrafawa na zamani suke da shi (modern processor). Android tana amafani da processor Cortex- A8 wanda ya fi irin wanda Symbian ke dauke da shi wato Arm11 CPUs. Misalin hakan ana iya gani ga HTC snapdragons da kuma Samsung Humming birds,dukkansu na amfani da 1 GHz wajen saurain sarrafa bayanai akan na Synbian da ke tafiya a kan 680MHz. Kuma wannan tazaran nasu yama karo a kan irin Android da aka yi yanzu masu dual-core CPUs mai Cortex-A9 na wayar Motorola Atrix. Hakan ya sa suka bar Symbian a baya.
- Fitar da launi (screen resolution) Android na ammfani da 800(854)x480 idan ka haɗa da na Symbian wanda ke amfani da (640×540). Wannan yana sa ka iya jin ɗaɗin browsing da ganin bayanai da hotuna da kyau. Fitowar Atrix sai ta zo da karin hakan wato qHD resolution (960×540). Tana zitan kala fiye da Symbian sau ninki 2.25 (pixels.
- Yawan Kwakwalwa (Memory (RAM). Sau da yawa akan damu idan ka nishadu da browsing sai wayar ta ce maka low memory lokacin da Android ke zuwa 512MB RAM Symbian kuwa na dauke da 256MB ne. Duk da cewa Nokia na ta ƙoƙarin fadada nasu memory hakan ya ci tura a Symbian domin wasu Androids har sun kai ga suna zuwa da RAM(768MB in Desire HD, 1GB a Artrix).
- Graphics (zane) da kuma Games. Symbian na dauke da Broadcom BCM2727 GPU, da ake ganin ci gaba a kan shi a kan Andreno 200 chips (Nexus one) iran da amma ta koma baya saboda zuwan Android GPUs, da kuma irin na zamanin, wato Adreno 205 (Desire HD) ko kuma powerVR SGX540 cores.Nvidia Tegra 2 ta zo da fage (zone ) inda masu anfani da Nvidia da ake kira Tegra kan iya buga games.
- Mabudin Yanar gizo (Web browser) da yawa an fi ji da bowser na Android saboda ta fi sauri da kuma bada abin da ake so. Misali Android 2.2 da ke iya daukan Adobe 10.1 da ake amfani da shi a yawancin websites. Yana baka damar kallon video da games daga websites mai nauyi kamar Kongregate. Amma Symbian sai ta sa maka ciwon kai kafin ta buɗe. Idan ma ta iyakenan, a inda ya sa yawancin mutane sun fi so su yi amfani da Opera duk da ita ma ba ta iya ɗauka.
- Nishaɗi (Multimedia). Maraba da applications na nishaɗin wakoki na sauti da na hotuna (music and videos). Kalon video, jin sauti ko sarrafa hotuna (pictures) abin nishaɗi ne a Androids device. Faɗin fuska (screen 4.3”) karfin kala da haske (super Amoleds), samun media players cikin sauƙi da ke taimakawa waje buɗe kowanne irin video/ sauti, shiga yanar gizo ta HDMI (connectivity) sauko da hotu ko sauti da DLNA media streming duk na daga cikin fifita Andorids a kan Symbian.
- Tarin application (application store) lokacin da Symbian Ovi store ya kai (258% a shekarar 2010) tuni Androids ta keta ta a kasuwa da (544% a shekarar 2010). Ta ɓangaren applications ma abin ya wuce yadda ake tsammani. Android na da (200,000) ya yin da Ovi ke da (40,000). Kodayake mukan duba shine yadda waɗannan applications ɗin ke tafiyar da wayoyin mu. Inda Ovi ke gazawa wajen saukar da abubuwa (downloading) ita ko Android takan gaya maka idan sabon updates ya fito kai tama yi maka updates idan ka so. Applicaion kamar AppBrain zai iya baka damar ka haɗa na’urar taka da kwanfutar ka domin ka yi installing bayan ka dirje irin wanda kaka so.
- Game da maganar application da na yi a sama ina mai tabbatar maka cewar akwai applications da dama na Android fiye da na Symbian a cikin kasuwanni. Kai ita kana iya yin abubuwa da dama da baka iya yi da Symbian. Alal misali ina amfani da 5 Dutch Android apps wanda babu irin kwatankwacinsa da za ka iya haɗawa da Symbian. A Android akwai applications na sautuka (music kai har ma da na kiwon lafiya (medical).Idan ma kadu ba abin ta wata fuskar, daban ba ma ta application store ba, za ka ga cewar applications na Symbian ba su da dadi ko saurin shiga (installing) kamar na Androids.
- Custom ROMS and Modding (tsangayar wayarka). Wannan tafarki na musamman inda Android ta keta kowa (platforms). Gwanayen irin wannan tsangayar kamar usuCyanogen, XDA-world ko kuma Modaco sun yi fice wajen yin amfani da sabo ko kuma tsohon OS (firmware) da kuma iya yin updates a kan lokaci. A gaskiya Androids ta wuce yadda ake tsammani.
- OS updates. A takaice duk wata shida (6) za ka ga sabon OS na Androids ya fito. Makera wayoyi aya yin da suke tunanin yadda za su yi updating nasu, za ka samu tuni HTC sun wuce wannan wurin ta hanyar amfani da custom ROMS da na bayyana a sama.
- Juyin-juya halin kasuwanci, ana iya ganin hakan ta yadda kasuwar Symbian ke kara yin kasa kullum, amma ta Android sai kara tashi take yi da samun karbuwa. Wasu da yawa masu kera wayoyi suna ta barin Symbian gaba ɗaya (Kamar Samsung da SE) kai abin ya zama kamr tsakinin mutun ɗaya da sauran, inda Symbian take ita kaɗai (Nokia) tana fama da taron dangi (Google, Samsung, HTC, Motorola, SE, LG da sauran su). A watan Janairu ya yin da CES a 2011 suka fito da bayanai game da ci gaban da aka samu ba ma a maganan Symbian a wajen. Hakan ya faru saboda fitowar wato Tablets da ta ci kasuwa da yaki. Daukar lokaci mai tsawo wajen bayyana sabuwar waya da fito da ita na daya daga cikin abubuwan da suka ja ma Symbian ta kara komawa baya (misali Nokia N8 da E7). Sabanin haka ga Androids da suke nasu tsakanin wata ɗaya zuwa uku ( 1- 3 months). ( ka duba DHD ko Nexus S ko kuma LG Optimus 2x)