Idan ka buɗe shafi a website a Intanet na san kana kallon shafuka ne kamar yadda kake ganin rubutu da hotuna a jikin takarda. A mataki na farko bayyanar da shafin Intanet abu ne mai sauƙi domin mutum ya kiran shafin da yake so ne ta hanyar amfani da abin da muke kira da browser. Za ka umarci kwamfutarka ta bayyanar maka da shafi a Intanet ta hanyar amfani da adireshin da shafin yake (URL). Ita kuma browser ta fito maka da shafin a jikin majigin Kwamfuta. Idan bayanan da kake son ka buɗe suna cikin kwamfutarka ne, to duk abin da ka kira zai fito da sauri, amma idan bayanan suna cikin wata kwamfutar ne to za ka ga bayyanar shafin ya ɗan tsawo kaɗan.
Akwai abubuwa da dama da shafukan Intanet suke yi wanda ko kaɗan shafukan da muka saba gani na takardu da mujallu ba bu yadda za a yi a ce suna yi. A misali babu yadda za a yi ka ga an yi rubutu a ƙarƙashin rubutun an rubuta cewar sauran maganar ko cikakkiyar maganar za a same ta a shafi na 57, kawai da ka taɓa hannunka a jikin wannan lamba ta 57 sai shafin ya buɗe. Babu wannan abu a takardunmu kuma ba kuma a yin tunanin haka za ta yiwu a nan gaba. Haka idan ka buɗe wani ‘fom’ wanda ake son mutum ya cike ya aika da shi zuwa wata ma’aikata, a ce da ya cike shi nan take, form ɗin da kansa ya kai kansa wannan ma’aikata ba tare wani ɓata lokaci ba. Haka na san ba mu taɓa ganin hotuna suna motsi ba a cikin littafi ko kuma mu ji magana tana fitowa daga cikin littafi. Amma duk wannan abubuwan da na lissafa da ma waɗanda suka fi su ana samunsu a jikin shafukan Intanet.
Amma akwai banbanci mai nisa tsakanin shafukan Intanet da kuma shafukan takarda. Domin akwai abubuwa da dama da muke ganin su a shafukan intenet wanda a zahiri muke ganin su amma a ɓoye ba haka suke ba. A misali ba kamar yadda duk abin da ka gani a cikin shafin takarda ba yana cikin wannan shafin ne, da hotuna da rubuce-rubucen da suke cikin shafi duk a shafin yake. To, shafukan Intanet ba haka suke ba, domin akwai abubuwan da yake faruwa a bayan shafukan (backend) wanda kai wanda ka buɗe shafin ba ka sani, sannan kuma ba komai ba ne za ka gan shi a jikin shafin da ka buɗe ka yi tsammanin yana cikin shafin ne gaba ɗaya. A misali zai iya yiwuwa ka kira shafi wanda asalin shafin yana cikin wata Kwamfuta ne a kasar Amurka, hotunan da suke cikin shafin kuma ya kasance suna cikin wata kwamfuka ne da take kasar Jamus, sannan kuma sautin da muke ji yana kasar Brasil, sannan kuma majigin da muke gani ya kasance yana kasar Saudi ne.
Aikin da browser suke yi ya wuce su bayyanar mana da rubutu da hotuna da sauti da muke ji ko gani a jikin talabijin na kwamfutocin mu ko kuma Wayoyinmu. Waɗannan browser suna yin waɗansu ayyuka da suka wuce hankali ga wanda bai san abin da ke faruwa a bayan shafi ba (backend). Domin su browser su suke da alhakin lura da sharuɗɗa da dokoki da wanda ya tsara shafin ya ce haka yake son su bayyana, da kuma abin da yake son masu shiga shafin su gani. Irin waɗannan sharuɗɗa da dokoki su ne wanda su browser kowace iri ce take lura da su. Su kuwa irin waɗannan dokoki wani ilimi ne na musamman da ake koyan shi kuma ake rubuta shi domin ita browser ta iya karanta shi. Shi wannan ilimi da browser take iya karantawa ana kiran shi HTML wato HyperText Markup Language.
To, a nan za mu iya cewar browser wani program ne na Kwamfuta wanda yake iya fassara rubutun da aka yi da dokokin na HTML.
Waɗannan Browser da ake da su suna da yawa amma waɗanda suka fi shahara a wannan lokaci wanda kusan kowa yana amfani da su, sune: Opera, Opera mini, Google Chrome, Intanet Explorer, Mozilla Firefox da kuma UC Browser. Akwai daruruwan brower amma waɗannan sune waɗanda suka fi shahara. To, dukkanin waɗannan program aikin su shi ne su fassarawa Kwamfuta dokoki da ƙa’idojin da wanda ya tsara shafin yake son mutane su gani.
Kamar yadda mai karanta wannan muƙalar yake gani (idan a mujalla kake karantawa) yana ganin akwai waɗansu rubutu waɗanda suke an ɗan kaurara su, wasu kuma na lankwasa su, wasu kuma sun fi wasu girma, duk waɗannan abubuwan da muke gani a takarda idan an yi amfani da MS Word ne aka yi su, bai wuce a ce an saka bold ko italic ba. Amma a wajen tsara shafukan Intanet ba haka abin yake ba, domin su ba italic ko bold ba ne, wasu surkulle na daban ake yi.
Shi wannan ilimin sanin yadda ake shirya shafin Intanet (web design) ilimi ne mai zaman kansa wanda ake koyar da shi a matakai daban-daban da kuma matsayi bayan matsayi. Wanda kowane ɗaya daga cikin waɗannan matakai ana son mai karatu ya san shi sosai kafin ya tsallaka zuwa wani ɓangare.
Ga duk wanda yake son ya ga ya wannan ilimi yake da kuma wani irin ƙoƙarin masu shirya shafukan da kake buɗewa a cikin Intanet suke yi, za ka iya buɗe kowane irin shafi a Intanet sannan ka latsa ɗan yatsan dama na Mouse ‘right click’ sannan za ka ga ‘view source’ sai ka zaɓe shi, zai buɗe maka wani shafi da zai baka bayan shafin abin da ke faruwa a shafukan Intanet.
Wasu shafukan an gina su da babban ilimin shirya shafuka saboda haka ba komai mutum zai gani ba a wancan shafin da ya buɗe, domin akwai ilmomi da dama da ake ɗaurawa a lokacin da ake buɗe shafukan Intanet waɗanda suke taimaka wa shi HTML wajen inganta aikin gina shafukan.
Akwai ilimi da dama waɗanda suke taimaka wa wannan ilimi na HTML domin yauƙaƙa shafin waɗanda suke haɗa XHTML, XML, JAVA Script, PHP, ASP, ASP.Net da ColdFusion. Irin waɗannan ilimin suna da yawa amma kuma waɗannan su suka fi shahara.
Kodayake kowace browser tana da irin yadda take ganin abubuwan da suke ƙunshe na dokoki da kuma ƙa’idojin rubutun shafukan Intanet. Shi ya sa idan mutum ya koyi ilimin yadda ake shirya shafukan Intanet, to yana da kyau duk lokacin da ya zo zai gwada shafukan ya gwada su aƙalla a browser iri huɗu waɗanda suka haɗa da Intanet Explorer, da Mozilla Firefox, da Google Chrome, da kuma Safari.
Darasi na gaba da yardar Allah za mu faɗi hanyoyi da kuma matakai da ake bi domin a shirya shafukan Intanet.
asssalam alaikum, dafatar kuna lafiya, hakika munji dadi da irin yadda kuke kokari akan jama,a. allah yasaka da alheri, kuma ayi ta hakuri damu nsaboda zamu dameku da tambaya kunsana komi saida hakuri. Allah yabiyaku. Haza wassalam