
A waccan mujalla da ta gabata mun yi alƙawarin kowane ffitowa za mu riƙa kawo tsokaci na musamman a kan waɗansu mutane da suka bayar da gudunmuwa domin ci gaban al’umma. Mujallar Duniyar Computer ba ta yi ƙasa a gwiwa ba, domin a wannan fitowar ta zaƙulo muku wani bawan Allah wanda mutane suka sansa a wani fage na musamman da matsayi har suna ganin cewar ai ya yi nisa da mutane saboda haka ma ba a ma tunanin cewar za a sami eata alaƙa ta taimakawa tsakaninsa da al’umma, akasin wancan tunani sai ga shi mu kuma muka duba muka ga ashe wannan bawan Allah yana kusa da mutane da kuma yana taimaka musu ta fannoni da dama.
A karon farko mun yi nazari mai zurfi a kan shin wa ya kamata mu fara da shi, kasancewar dukkan wanda wannan mujallar za ta fara da shi dole ya kasance ya tattara waɗansu abubuwa masu dama da za a fada wa al’umma. Shin wannan ayyukan yayi su ne a bayyane ko kuma ya yi su ne a ɓoye. Sannan kuma daga cikin abubuwan da muka duba har muka ɗauko wannan bawan Allah shine, cikin jerin ƙa’idar da Mujallar Duniyar Computer ta gindaya shi ne, dole duk wanda za mu fara da shi ya kasance dattijo ne mai shekaru da yawa, sannan ya kasance mutum ne wanda ya yi ayyuka aƙalla biyar waɗanda suka sha banban da irin ayyukan da mutane suka saba ji ko suka saba gani. Sannan kuma dole wannan mutum ya kasance ya taimaka wa harkar ilimi wacce ita ce ginshikin rayuwar al’umma, sannan wannan taimakon da ya yi shi ma ya kasance ya saɓa wa mutane da irin yadda suka saba ji wajen taimaka ilimi. Sannan ya kasance ya kawo ci gaba mai girma ga al’ummarsa ya kawo ya kawo shine ga mutanen sa da kuma yankinsa ko kuwa wannan ci gaban da ya kawo ya kawo shi ne domin jama’ar baki ɗaya. Daga ƙarshe kuma duk wanda zamu fara da shi dole ya kasance yana yin wani irin taimako ga al’umma wanda wannan taimakon ya saɓa wa al’umma ta fannoni da dama.

Irin waɗannan ƙa’idoji da muka saka sai muka gano cewar wannan bawan Allah da za mu yi magana a kansa ya tattarasu har da ma ƙari a kan waɗannan. Wannan dalili ya sanya muka haɗu a kan cewar lallai idan muna son mu yi wa kanmu a dalci to lallai mu fara da shi.
Da yawa mutane suna ganinsa ne soja sannan kuma mutumin da ya zama mai bai wa shugaban ƙasa shawara a harkar tsaro har sau uku, sannan kuma mutum ne wanda ko a soja da ya yi sunansa ya yi fice, haka kuma idan aka zo ta harkar jama’a sai ka ji mutane suna mamakin idan sun gansa a gidan biki ko mutuwa ko wani taro sai su yi ta mamakin daman wannan shi ne Janar Ali Gusau? Ba ma wannan kaɗai ke baiwa mutane mamaki ba sai irin yadda muka zaɓe shi a matsayin gwarzon mu wanda ya zama mutum na farko da za mu fara magana a kansa.
To dai na mamaki, lallai mutane iri biyu ne, akwai mutanen da Allah ya yi su, babu abin da ya dame su shi ne idan sun yi ayyuka babu abin da suke so sai a yi ta banbaɗanci da ƙaraji a kansu a gidajen yaɗa labarai. Sannan akwai waɗansu waɗanda duk abin da za su yi suna yinsa ba tare da hannun hagunsu ya san abin da na damansu ya yi ba. Janar Aliyu Muhammad Gusau yana ɗaya daga cikin waɗanda suke yin ayyukan ci gaban Al’umma amma kuma ina tabbatar muku da cewar mutane da yawa ba su sani ba. Mun kasa ayyukan da yayi manya kashi huɗu domin mu sauƙaƙewa mai karatu bibiya.
ILIMI
Mu fara da matakin gina al’umma ingantacciya, dukkanin wani aiki da mutum zai yi to babu kamar gina al’ummar sa, shi kuwa gina al’umma ya dace ya zamanto wani abu ne wanda idan har za ka yi to ka ɗauki matakin farko na ‘koyar da mutane yadda ake kama kifi ba ka zamanto mai ba su kyautar kifin ba’.
Janar Aliyu Muhammad Gusau, ayyukan ci gaba da ya yi wa al’umma a fannin ilimi ya sha banban da irin wanda mutane su ke zato, domin a nashi irin salon babban abin da ya fi mayar da hankalinsa matuƙa shi ne harkar ilimi. Kowa yasan cewar ilimi shi ne abin da yake fitar da al’umma daga cikin duhu zuwa haske, sannan kuma ilimi shi ne ginshikin al’umma duk al’ummar da takasance iliminta ya yi ƙaranci to haƙiƙa wannan al’ummar ko mu daɗe ko a kusa watan wata rana zata zama maƙasƙanciya abin wulaƙantawa.
Da farko dai Janar Aliyu Muhammad Gusau ba wai gini kaɗai na makaranta shi ne a gabansa ba, domin idan ana maganar ilimi to zamu duba mu gani cewar akwai gudunmuwa ta musamman da kuma mayar da hankali na haƙiƙa da ya yi wajen ganin ya fitar da al’ummar sa a cikin duhu zuwa haske.
Ba mu da lokacin da za mu ɗauki aiki ɗaya bayan ɗaya muna yi wa mutane bayani amma kuma yana da kyau mu ɗauki kaɗan domin mu fitar da zahirin abin da muke magana a kai. Koma mahaifar Janar Aliyu Muhammad Gusau, za ka samu wata makaranta a garin Gusau gaba kafin gidan gwamnati a hanyar zuwa garin Sakkwato wacce ake kiran da College of Islamic Studies babu ko shakka wannan makaranta ba mallakin kowa ce ba illa Janar Aliyu Muhammad Gusa. Wannan makaranta ta sha banban da irin makarantu da mutane su ka sani, baya da zubi na gini da ta sha sannan kuma ga shi an saka mata kaya na garari wanda ko makarantun gwamnati to a yanzu ba ka samun irin waɗannan kaya.
Tana da manyan ɗakunan bincike na kimiyya da fasaha wanda ake kira a Turance da Labrotary manya guda uku wanda kayan da ke ciki ba ka buƙatar komai a wurin wasu
Ba wannan kadai Janar ya yi a wannan makaranta ba, ya kasance yana lura da sha’anin albashin malamai na wannan makaranta da dukkanin abin ita makarantar take buƙata. Wannan shi ne farkon sakayyar da Janar ya yi wa al’ummarsa da su ke Jihar Zamfara wanda hatta mutanen wannan garin sun ɗauka cewar wannan makaranta mallakin gwamnatin tarayya ne, to wannan ke nan wanda akwai irin wadannan makarantu da ya yi musu haka wanda ba su kidayuwa.
Idan kuwa muka dawo garin Kaduna ita ma za mu ɗauki makaranta guda wacce ita wannan makaranta ta isa abin alfahari da kuma abin nuna wa jama’a. Idan kana tafiya kan Layin Ali Akilu daga garin Kaduna ka shiga layin Dendo akwai wata makarantar kwamfuta mai suna Legacy Computer Institute wanda ta fara yin aiki tun shekarar 2005 wacce wannan makaranta ta shahara matuƙa a cikin garin Kaduna da kewaye wacce ita ma Janar Aliyu Muhammad shine wanda ya gina ta kuma ya ke tafiyar da harkokinta.
A Legacy Computer Institute abubuwan da janar ya ke yi ya sha banban da sauran taimakawa ilimi da sauran al’umma suke yi. Domin a Legacy Computer ce kaɗai dukkan waɗansu kwasa-kwasai da ake yi shi janar da kansa ya ke bada tallafi domin ganin kowa ya samu wannan ilimi cikin sauƙi. Kasancewar idan dambu ya yi yawa baya jin mai, shi a wurin janar ba haka abin ya ke ba domin babu wani kwas da ake gabatarwa a wannan makaranta wanda bai bayar da tallafi ba.

Ba a maganar irin kayan aiki da aka zuba a wannan makaranta, domin baya da samar mata matsuguni ƙasaitacce da kuma tabbatar da ita a wurin da kowa zai iya zuwa, Janar ya sanya kayan karatu na zamani wanda duk wanda yake buƙatar karatu to zai same su. Daga cikin irin wannan gudunmuwa da yake bayarwa, ni ina ɗaya daga cikin wadanda suka amfana da arzikin wannan bawan Allah ta hanyar kwas da muka yi a wannan makaranta. Shi wannan kwas da ake kira da IT MASTER wanda mutane suke yin min laƙabi da Salisu Webmaster ya samo asali ne daga wannan makaranta. Wannan wani kwas ne da duk Najeriya babu inda ake yinsa sai a Legacy kwas ne wanda duk wanda ya yi sa daga farko zuwa ƙarshe zaka zama ƙwararre a fannonin kimiyya da fasahar kwamfuta, ba a nan abin ya ƙare ba, wannan kwas makarantu manya na Duniya suke bayar da takardar shaida, daga cikin makarantun akwai New Jersey Institute of Technology da ke kasar Amurka wanda idan mutum ya gama wannan kwas yana son zai ci gaba to akwai makaranta a ƙasar Kenya wacce mutum zai je ya yi digiri a kansa. To wannan kwas a lokacin da muka yi shi ana biyan dubu hamsin wanda ake yin watanni tara amma kuma wani abu da mutane ba su sani ba wannan kwas asalin kuɗinsa naira dubu ɗari ne, kai ka biya rabi janar ya biya maka rabi. Wannan abu haka yake domin gani ba daidai yake da labari ba.
Idan muka duba sake inganta wannan makaranta da janar ya yi na sauya mata babban wuri za mu ga cewar an sami nasarar ƙara haɓɓakata da abubuwa da yawa, misali a yanzu haka akwai kwas na Cisco wanda a sauran makarantu ana biyan kuɗi da bai gaza dubu saba’in ba amma a Legacy Computer Institute ana biyan dubu talatin. A cikin irin nashi taimakawa da yake yi shi ke cika wa al’umma wannan kuɗaɗe. Idan muka ce za mu tsaya mu ɗauki aiki ɗaya bayan ɗaya da ake yi a wannan makaranta ta Legacy Computer to sai mucike takardu da rubutu ba tare da mun tsallaka wani sashe ba.
Har ila yau ta ɓangaren ilimi domin kowa ya san cewar idan aka bai wa al’umma ilimi an gama gina ta, janar ya samar da wani irin ɗakin bincike da karatun wanda a halin yanzu zai yi wahala ka sami wani ɗakin bincike da karatu a cikin garin Kaduna da ya fi shi yawan littafai, wanda ake kira da Aliyu Muhammad Library.
Wannan ɗakin bincike kusan yana da komai da dalibi yake buƙata domin ya yi bincike, da farko dai dukkan wani littafi da kake jin ya shahara a duniya akwai shi a ciki, aƙalla a yanzu akwai sama da littafai zalla ba mujalladai ba, sama da dubu ɗari da ashirin wadanda a yanzu kawai an shirya sama da dubu tamanin a kantocinsu.
Ga kuma wata irin kwamfuta ta musamman ga waɗanda ba sa son karatu a littafi su yi amfani da ita. Ita wannan kwamfuta mai manhaja ta e-granery yana ɗauke da duk wani rubutu na littafai da jaridu da mujalla a cikinsa.
Shi wannan ɗakin bincike na kyauta ne ga dukkanin ɗalibai masu karatun gaba da sakandare da masu yin bincike na addini da sauran karatuka. Duk a daidai lokacin da na ke rubuta wannan tsokaci ba a buɗe wannan ɗakin karatu ba, amma dai mutane da dama a hakan suna ta zuwa domin yin bincike. Wannan ɗakin bincike ya samu kula ta musamman domin a halin da muke ciki kusan dukkanin littafan da suke cikin wannan ɗakin an shigar da su a cikin kwamfuta wanda da zarar mutun yana son littafi ba sai ya sha wahalar nema ba, sai dai ya shiga kwamfuta ya tambaya ita kuma ta faɗa masa a wane kanta za ka samu.
A cikin ƙoƙarin ganin an daidaita matsalar ilimi da harkokinsa na Legacy Computer da College for Islamic Studies da kuma Aliyu Muhammad Library mutane basu yi aune ba kawai sai muka samu labarin cewar akwai wata jami’a ta gani ta fada da janar ke gina wa al’umma a garin Abuja. Idan har Allah ya sa an kammala wannan jami’ar to za ta share wa mutane da yawa hawaye, sannan kuma kamar yadda ya saba ita wannan jami’ar za a bata kulawa ta musamman yadda za a bai wa ‘ya’yan marasa ƙarfi damar yin karatu.
Jami’ar da za ta riƙa ɗaukar dalibai daga ko’ina na sassan ƙasarnan, sannan a wannan jami’ar za a mayar da hankali wajen karatu da manhajoji na zamani waɗanda za su taimaka wa ɗalibai domin samun ingantaccen ilimi da za su zama jagorori nagari ga al’umma baki ɗayanta.
Ta bangaren ilimi ke nan.
TALLAFI DA GURABEN KARATU
Duk da irin waɗancan tallafi da muka bayyana Janar bai tsaya a cika kuɗin karatu da yake yi ba a makarantunsa ba, akwai kuma ƙarin kuɗaɗe da yake ware wa domin taimaka wa mutanen da ba su da ƙarfi amma kuma suna karatu a waɗansu wurare ko kuma gurbin ilimi da yake cika musu domin su ƙaro karatu ko kuma su je su yi shi.
Ba za mu iya sanin adadin mutanen da shi janar ya ba su guraben karatu ba tun daga matakin Firamare har zuwa jami’arsu ba, adadinsu baya ƙididdiguwa. Ba a wannan kaɗai abin ya ƙare ba, domin akwai tallafi da yake baiwa dalibai domin su tafi ƙasashen waje domin su ƙaro karatu ko kuma ilimi da ake da shi a waccan ƙasar wanda a wannan ƙasar ta mu ba mu da shi.
Ba a maganar waɗanda suke zuwa suna karɓar kuɗin makarantar yaransu na sakandare ko jami’a. Idan muka dawo ga fannin bayar da tallafi har ila yau a daidai wannan lokacin da muke rubuta wannan muƙala akwai sama da mutane hamsin waɗanda Janar ya basu tallafin yin karatu a ƙasashen waje, tun daga farawa zuwa karewa.
Ta fannin gidan soja kuwa a cikin gurabun da janar ake ba shi a lokacin da za a ɗauki sababbin sojoji, Janar Aliyu Muhammad Gusau ya na bai wa duk wanda yake so ba tare da ya san waye shi ba. Duk da yake mutane masu yawa sun kawo ƙoƙon bararsu, tun daga gidan ‘yan sanda, da kwastam, da imagination da makamantansu. Waɗanda suka samu wannan gurabu za su iya faɗa maka cewar ba su taɓa ganin wannan bawan Allah ba, waɗansu ma gani suke yi an ce su kawo takardar neman shiga soja, kuma su ga an samu, da shi da ya samu, da gurbin wanda ya shiga duk ba wanda ya taɓa ganin ɗaya daga ciki.
SAMAR DA AIKIN YI
Duk mutumin da aka lissafa irin waɗancan ayyuka kuma ya tabbata cewar waɗannan ayyuka an yi su, to ba shakka samar wa mutane aikin yi a wurin wannan bawan Allah ba abin wahala ba ne. Ayyukan yi da janar ya samar ga al’umma yana da yawa. Ko da za mu tsaya kawai ga ma’aikatunsa, kama daga Gusau, mutane da dama suka samu aikin yi, haka mu dawo garin Kaduna, mu ɗauki inda muka yi magana Legacy Computer Institute shi ma mutane da dama suka sami aikin yi. Haka mu ɗauki wannan jami’a ta Gusau Institute da ake ginawa a garin Abuja mutane nawa za su sami aikin yi.
Daga cikin irin gina al’umma da Janar Aliyu Muhammad yake ƙoƙarin samar wa al’umma shi ne samar da kafafen yaɗa labarai na zamani wanda kuma suke yin kafaɗa da kafaɗa da sauran gidajen yaɗa labarai na duniya. Mu ɗauki gidan radiyon Nagarta, wannan gidan radiyo na ɗaya daga cikin gidajen da suke ƙoƙarin wayar da kan al’umma wajen abin da ya shafi tarbiyya da kuma ilmantarwa da nishadantarwa.
Kamar yadda mutane da dama suke sha’awar shirye-shiryen da wannan gidan radiyo yake gabatarwa, a ƙarin ƙoƙarinsa, a yanzu haka an kusan kammala shirye-shiryen buɗe gidan talabijin wanda zai fuskanci ƙalubalen da Arewacin Najeriya ta ke fama da shi.
WAƊANSU AIKACE AIKACENSA
Kamar yadda muka faɗa tun daga fari cewar ba ma son mu tsawaita a kan ayyukan da wannan bawan Allah yake aiwatarwa, ba za mu iya ba saboda yawansu.
Waɗansu daga cikin ayyukan da ya shahara wajen yinsu kodayake mutane da yawa ba sani ba, shi ne aikin taimaka wa Addinin Musulunci, Janar yana ɗaya daga cikin mutanen da suke yin aiki da ya shafi Addini wanda ba su misaltuwa. Kama daga ginin makarantun Islamiya a garuruwa da dama, da gyaran masallatai da ake salloli biyar da kuma gina masallatan Juma’a da buga littattafai ana raba wa mutane.
Da na yi maganar masallatan Juma’a sai na ga ya dace mutane su sani cewar akwai wurare da dama a cikin ƙauyuka da birane da Janar ya gina wa masallatan Juma’a wanda mutane da yawa sai dai suga an kawo musu gudunmuwa ko kuma a zo a tambayi mutane a ina kuke son a gina shi.
Ba a maganar taimaka wa gajiyayyu wajen matsalolinsu, kama daga marasa lafiya da wanda suka gaza wajen biyan kuɗin magani a asibitoci, da mafi yawan wadanda ake yi wa aiki ko kuma suke neman taimakon fitar da su ko kuma suke neman taimako domin yi musu aikin da sai an haɗa da ƙasar waje. To, a zahirin magana mutane da dama sun sami wannan tallafi ko dai ta hannun masu tafiyar da harkokin taimakawarsa, ko kuma ta hannunsa.
Janar mutum ne wanda kusan duk ayyukan da ya yi a rayuwarsa, a boye ake yin su, duk taimakon da zai bayar baya tara ‘yan jarida da watsa labarai, shi yasa da zarar wani ya bada waɗansu maƙuden kuɗaɗe ga wata makaranta sai ka ji mutane suna cewar to ina na mu Janarorin suke. Irin tallafi da Janar ya ke baiwa da za a tattarashi a shekara sai kun riƙe baki. Akwai waɗansu aikace-aikace da ya ke yi wanda mu kanmu da muka samu labari sai da muka girgiza. An faɗa mana cewar kada mu kuskura mu faɗi adadin kuɗaɗen da muka gani domin ba zai so ba, amma jimillar taimako da yake kaiwa na abinci da Ramdan kawai na garuruwa huɗu kacal kuɗin ya fi ƙarfin tunanin mai tunani. Haka manyan ɗakunan taro da ya ke kinawa wa cikin waɗansu jami’o’i da ke Arewacin Najeriya shima abin ya yi yawa. Haka lokacin aikin Hajji tallafin abin da ake ci a garin Makka shima da muka ga kuɗin kan mu ya ɗaure.
Daga nan ne muka ƙara fahimtar cewar lallai wannan bawan Allah Janar Aliyu Muhammad Gusau ya yi nisa a harkar taimaka wa al’umma sannan kumu baya son kwakwazo. Muma kanmu da muka yi wannan rubutu ba mun yi domin mu tona masa asiri ba ne, sai dai domin yawan ƙorafi da mutane suke yi na cewar ba su san irin waɗanna ayyuka ba.
Da wannan ne nake ganin ya kamata in rufe wannan rubutu nawa da faɗa mana yadda Janar yake, mutum ne wanda baya ɗaukar raini kuma mutum ne wanda baya son shisshiga da katsalandan a cikin rayuwarsa. Mutum ne wanda yake tafiya a kan kaifi guda, idan e to e ne kawai, idan kuma aka ce a’a to a’a din ce. Ya na kuskure kamar kowa kuma ya da sauƙin kai da hatta ma’aikatansu suna masa gyara kuma ya karɓba, ya na da tsare alƙawari idan ya ce same ni a wuri ƙarfe ka za zaka same shi.
An haife shi a garin Gusau da ke Jihar Zamfara a yanzu a 18 ga Mayun shekarar 1943, ya yi ritaya a gidan soja a watan Satumbar 2010 ya na da matsayin Lutanal Janar. Ya riƙe matsayin shugaban sojoji na wani ɗan lokaci, haka ya zama mai baiwa shugaban ƙasa shawara a harkar lokacin mulkin Obasanjo da Shugaba Goodluck. Allah ya azurta shi da iyalai, maza da mata da kuma jikoki.
Allah ya ƙara masa lafiya da tsawon kwana, ya sanya irin wannan ayyuka na alkairi da yake yi a ɓoye da bayyane ya saka masa da alkairi, ya kuma tsare shi daga duk wani irin sharri da ya sani da wanda bai sani ba.
Haƙiƙa ba mu bada wata shaida a kan shi ba, sai da abin da muka sani, sannan kuma a kan abin da ya ke ɓoye mu bamu zamanto masu sanin gaibi ba.
Wannan shi ne kaɗan daga cikin ɗin bin ayyuka da Janar Aliyu Muhammad Gusau ya ke gabatarwa.
Assalamu alaikum ya ma’abuta son karuwar al’umma, musamman Hausawa a wannan duniya da take neman ta yi wa Hausawan nisa. Lalle tun a ranar da na bukaci kwafen wannan mujalla a shafina na imel, a kullum sai kara so da kauna nake yi wa mujallar. Allah ya taya ku kiwon wannan al’umma a ilimance.
Shawarwarina guda biyu da nake son bayarwa su ne game da yanayin fassare-fassarenku na kalmomi masu tsauri da suka danganci wannan fage da kuka dauka, wato Duniyar Kwamfuta. A fagen ilimi na jami’a, muna da wani darasi da ya jibanci irin wannan fassara, da ake kira da ‘Technical Translation,’ wato ‘Kebabbiyar Fassara.’ Da zan so ku yi iya kokarinku ku hada karfi da karfe da manyan malaman jami’o’i da suke bangaren nazarin Hausa, domin su bayar da tasu gudunmuwar, alal akalla ta fuskar fassara wadannan kalmomi domin a sami daidaito, kamar yadda ake da su a Ingilishi da sauran harsunan Turai.
Shawara ta biyu ta danganci bin ka’idar rubutu ne, wato ka’idar da manazarta Hausa suka yi daidaito a kai na yadda ya kamata a rubuta wasu kalmomi na harshen. Idan mutum ya yi wa rubutunku karatun ta-natsu, wani lokaci akan dan iske wasu matsaloli dangane da saba ka’idojin rubutun. Amma dai a gaskiya kuna iya bakin kokarinku. Ni ma a nan, sai a yi mini uzurin domin na gaza yin amfani da bakake masu kugiya da ya kamata na yi amfani da su. Wannan kuwa matsala ce ta manhajar kwamfutar tawa da kuma shafin bai yarda na shigo da su ba. Allah ya kara buda mana kirazanmu, mu tafi daidai da zamani.
Malam Shuaibu Hassan muna godiya da jinjina a gare ka. Amma kuma wani hanzari ba gudu ba wannan al’amari somashi a kayi, kuma muna kokarin tsaftace shi, mun lura idan mun jira Editocin mu kafin mu yi posting zai dauki lokaci kafin mu sanar da al’umma ilimin da muke son mu sanar da su. Amma ala kulli hal! za mu ci gaba da kiyaye ka’idodin da yakamata. Mun gode Allah Ya bar zumunci Amin.