Gabatawar.
Ko babu kamai idan ka haɗa Kwamfuta da kanka za ka samu ragi na kuɗi sosai. Haka kuma idan ka haɗa Kwamfuta da kanka zai zamanto ta yi ƙarfi fiye da wacce mutum zai siya a kasuwa wacce haɗaɗɗiya ce, domin Kwamfuta da mutum ya haɗa da kansa yana da cikakkan zaɓi wajen zuba mata dukkan abubuwan da yaga dama da kuma abubuwan da yaka so. Sannan ko babu komai idan ka haɗa kwamfuta da kanka zai taimaka maka matuƙa wajen sanin dukkanin kayan da suka haɗa kwamfuta.
Shi yasa a wannan lokaci ake samun ma’aikutan injiniyoyi, ‘yan makaranta, mata auren kowa yana haɗa Kwamfuta cikinta da wajenta.
Kodayaka Kwamfutocin da suka kasance sun zo a haɗe daga kamfanonin da suke haɗa Kwamfuta a yanzu suna da ɗan sauƙi ba kamar a da ba. Shi yasa a wannan lokaci ya ke da kyau ka sani cewa in haɗa Kwamfuta ta da kaina ko kuma in sayota a haɗenta ta fi? Za mu yi cikakken bayani a kan haka.
Wani lokaci ba za ka iya haɗa Kwamfutar da aka sayota da kuma Kwamfuta da mutum ya haɗa ta da kansa ba, kamar misali sararin samaniya ne launinsa shuɗine ba kuma wanda zai iya canzawa, ko ya yi maka ko bai yi maka ba, ba za ka iya canzawa ba domin haka mahalicci makaɗaici ya halitta kayan shi.
To ita ma Kwamfuta da wani kamfani suka haɗata, dole ka amince da abubuwan da ita Kwamfutar za ta zo da su, kama daga motherboard, da RAM da CD ko DVD duk sai wanda ita Kwamfutar ta zo da shi kaɗai za ka yi amfani da shi.
Amma idan kaine za ka haɗa Kwamfutar da kanka to ka na da cikakken zaɓi kan dukkan abin da za a saka a cikin wannan kwamfutar. Haka kuma sai in da ƙarfi ya ƙare, sannan kuma duk abin da ka saka da kanka, to kana da masaniya a kansu, sannan kuma ga fa’idan zama gwanin dukkanin kayan cikin kwamfutar domin za ka sansu kuma za ka san aikin da suka yi
Haka kuma duk mutumin da zai haɗa Kwamfuta da hannunsa ya je kasuwa ya siyo wannan da wancan ya haɗa ya kunnata ya ga takawo wuta ta tashi ta yi aiki, to, sai ya fi kawo farin ciki da murna. Kuma har ila yau, kai ma ka shiga sahun waɗanda suka san zamanin su kuma ko babu komai ka sauƙaƙawa kanka wajen kuɗi domin duk kwamfutar da ka sayota a kasuwa baya da cewar sai abin da ka gani haka kuma suna da ɗan karan tsada.
Kodayake suma kanfanonin da suke haɗa Kwamfuta a wannan zamani su na ƙoƙarin haɗa Kwamfuta masu sauƙi da kuma rahusa domin masu saya su sami sauƙi. A shekarun baya babu yadda za ka iya kamanta haɗaɗɗiya domin a da duk kwamfutar da wacce za ka haɗa da kanka wajen inganci domin ada duk Kwamfuta da ka sayo kayan cikinta masu inganci, sannan kuma suna da tsada matuƙa. Amma a yanzu sai ka samu Kwamfuta wacce ta zo kai staye da ga kanfani kuma ka samu cewar kayan cikin ta ba masu inganci bane. Suma suna yin haka ne domin a samu sauƙi wurin siya.
Sannan mutane ba sa yin la’akari da mene ne ita Kwamfutar ta ƙunsu, kodayake waɗansu a lokacin da suke son su haɗa Kwamfuta za su gayawa mai haɗa mu su cewar ga irin abubuwan da suke son ace ita Kwamfutar ta su ta na da shi. Domin mutane da suke aiki da Kwamfuta wani lokaci basu cika damuwa da mene ne su nan waɗanda suke yin Kwamfuta ba sa da muwa da shin ita wannan kwamfutar za ta yi min aikin da na ke son ta yi mini ko kuma ba za ta iya ba?
Saboda haka, idan har ita wannan kwanfutar za ta yi musu aiki bai dame su da kowane kamfani ne ya yi ta ba. Idan kuma ta wani ɓangare muka duba zamu ga cewar kwamfutocin da mutum ya siya haɗaɗɗiya zata fi tashi sauƙi wani lokaci, domin idan kayi la’akari da lokacin da su waɗancan kamfanonin za su yi su, suna yin su da matuƙar yawa ne, amma kai kuwa bai wace ace kai guda kawai za ka haɗa ba. Sai dai kamar yadda muka yi bayani a farko, idan kai za ka haɗa kwanfutar ka to dukkanin waɗansu hardware da za ka zuba kana da zaɓi.
Misalin da zan baiwa mai karatu shine, da za ace ana son ka haɗa kwanfuta wacce ake son ta yi zahirin aiki na gyaran hotuna ko kuma gyaran bidio sannan kuma ana son ka haɗa mata abubuwan da suka dace da ita, to, ina tabbatar maka da cewar sai kayi kamar kaɗaura hannu a sama ka ce wayyo saboda kayan da ta ke buƙata suna da matuƙar tsada.
Haka kuma idan ka yi la’akari da lokacin ka idan kasan baka da cikakan lokaci, ko kuma lokacin ka kuɗi ne gare ka, to gara ka daure ka siyo haɗaɗɗiyar kwanfuta a kasuwa. Amma idan ka na da cikakken lokaci to ka tsaya ka haɗata da kanka a kawai daɗi a ciki.
Wata tafkekiyar matsala kuma shine duk lokacin da ka sayi kwanfuta a wurin masu sayarwa to za su iya baka ‘warranty’ da kuma ‘garanty’ amma idan kaine ka haɗata da kanka to idan wani abu ya faru da ita babu wanda za ka yi wa ƙorafi a kan cewar abu kaza baya yi. Shi ya sa ya ke da kyau ka san cewar idan za ka haɗa kwanfuta da kanka yana da kyau ka ɗau matakin kiyaye lalacewar kaya sannan kuma kayi takatsantsan wajen haɗa abubuwan cikinta ka tabbatar da komai ya shiga ya zauna daidai wa daida.
Kodayake idan ka shiga intanet ka na neman shawara a kan matsalar da kwamfutarka ta samu bayan ka gama haɗata za ka samu rubuce-rubuce masu matuƙa yawa waɗanda al’ummomi da dama suka zauna su ka rubuta domin taimakawa irin ka waɗanda suke da burin suga cewar suna haɗa kwamfuta da kan su. Wani abu kuma shine idan mutum ya sayo kwamfuta wacce wani kamfani ya haɗa za ka samu takan zo da ‘operating System’ nashi kuma mai lasisi na asali to, amma idan kaine ka haɗa ta dole sai ka je ka sayo su waɗannan software da za ka zuba musu da kuma waɗansu manhajojin da kake buƙatar ka yi aiki da su.
A cikin wannan rubutu, idan kai mai sha’awar yaga ya haɗa kwamfuta ce da kasa, to ka sani ka zo wurin da zaka koya, domin da taimakon Allah za mu yi cikakken bayani dalla-dalla da kuma hotona, waɗanda za su taimaka wa mai karatu ya iya haɗa irin wannan kwamfuta. Wanda ko da ace kai mai karatu ba ka taɓa haɗa kwamfuta ba ko kuma baka ma san kwamfuta ba, amma ka bi wannan karatu daki-daki to in Allah Ya so za ka samu dacewa.
Saboda haka mun kasa wannan darasi kashi-kashi saboda mai karatu ya fahimta da farko za mu gabatar da mahimmanci haɗa kwamfuta da kanka, sannu mu lisafin abubuwa da ka ke buƙata ka sayo, sannan mu nuna maka mataki bayan matakin haɗa ita kwamfutar sannan mu faɗa maka waɗansu ‘yan matsaloli da idan ka gama haɗawa bata kawo wuta ba ko kuma ta kawo amma wani abu ki yin aiki ya za ka yi ka gyara shi?
Sannan kuma daga bisani mu nuna maka yadda za ka zuba mata manhajoji da ka ke son ka ɗaura mata. Sannan kuma mu nuna wa mai karatu yadda zai shiga ita kwamfuta shi zuba mata abubuwan da zai yi aiki da ita. Da fatar Allah maɗaukakin sarki Ya yi mana jagora, Amin.
Yadda za ka zaɓi kayan hardware
Idan kana son ka haɗa Kwamfuta da kanka abu na farko da za ka fara da shi shi ne hardware da za ka yi amfani da su wajen haɗa ita wannan Kwamfuta. Yana da matuƙar mahimmanci ka san wace irin Kwamfuta zan haɗa, me da me na ke buƙata wajen haɗa ta domin sanin hakan shi zai sauƙaƙa maka wajen kashe kuɗi da kuma sanin ingantattun ababen da ka ke buƙata kafin ka haɗa ta.
Sau tari waɗansu idan suka je kasuwanin domin sayo kayan Kwamfuta sukan bi kyale-kyale, ko kuma su sayo abubuwan da ba su buƙata wajen aikinsu. Misali mutun ne yaka son ya haɗa Kwamfuta da zai riƙa rubuce-rubuce da ita, ko kuma ya riƙa yin aikin lissafi da ita, ko kuma yana son ya riƙa yin aikin bincike a intanet to kaga baya buƙatar ya sayi Advance 3D graphic card, domin graphic card da ya ke cikin motherboard ɗin shi ya wadatar da shi.
Saboda haka, mu ɗauka a halin yanzu mutum ya na son ya shiga kasuwa ya siyo kayan Kwamfuta, to kamar dame-dame ya ka buƙata. A ƙarshe zamu lissafa dukkan abubuwan da aka sakawa kwamfuta sannan kuma dama wadanda ake iya saka wa Kwamfuta amma ko kuma kai ba za ka yi amfani da su ba. Mun yi haka ne domin ka sani zahiri a kan abubuwa da ka ke buƙata
Abubuwan da za ka nema a kasuwa
1. ATX CASE
2. MOTHER BOARD
3. PROCESSOR
4. MEMORY
5. GRAPHICS CARD
6. SOUND CARD
7. HARD DRIVE
8. CD/DVD ROM
9. CD/DVD WRITER
10. BLU-RAY WRITER
11. SPEAKERS
12. LCD MONITOR
13. MODEM
14. FLOPPY DRIVE
15. TV CARD
16. SATELLITE CARD
17. CABLE TV CARD MOUSE KEYBOARD
Waɗanna sune ataƙaice abubuwan da za ka saya a kasuwa ka sakawa Kwamfuta domin kayi aiki da ita. Sannan mai karata ya sani ba komai da muka lissafa ba ne za ka saya a cikin abubuwan da muka lissafa ba, akwai abun da kwamfuta take buƙata wanda dole sai da shi za ta yi aiki, akwai kuma abin da za a saka mata domin ƙara mata armashi ne kawai.
Bayanan da zai zo a gaba za muyi bayani filla-filla ne na kowane abu da muka saka da kuma aikin da yake yi a cikin Kwamfuta, to bayan ka gama karanta shi idan ka tashi shiga kasuwa to ka san me da me kake buƙata domin haɗa taka kwamfutar.
DESKTOP KO TOWER CASE
Idan a ka ce Desktop Case ana nufin gidan da za a zuba mishi dukkanin kayan da ka siyo a kasuwa sannan kuma a cikin wannan case ne za ka haɗa sauran kaya da za ka haɗa mata domin ta yi aiki.
Su kuwa case na kwamfuta ko kuma ka ce ɗakin kayan kwamfuta iri biyu ne, akwai na kwance, wada aka kira da desktop wanda ya ke a shinfiɗe ko ka ce a kwance ake ɗaura shi a kan teburi, sanna a ɗauko monitor a ɗaura a kan shi. Sannan kuma na biyun ana kiranshi da tower shi na tsaye ne, wanda aka ajiyeshi a ƙasan teburi ko a gefen monitor. To wuri sayan case na Kwamfuta kana da zaɓi shin kwantaccen zan sayo ko kuwa na tsaye? Ya danganta da in da za ka saka ita kwamfutar da kuma mene ne da kuma me ye za ka zuba mata.
Mafi shaharar case da ake da su a wannan lokaci shine tower case, wanda ake samun mini case wato shi ne wanda ya fi kowanne daga cikinsu ƙanƙanta da kuma sirantaka, wani lokaci kuma a kan samu mini case mai faɗi. Sannan akwai Midi Tower Case- wato matsakai ne wanda ya fi mini tsawo sannan kuma ya fi shi yawan kayan da za a iya saka masa. Sannan akwai full tower case wato dogo ko cikakken gida, wanda yana da matuƙar tsawo sannan kuma yana da damar da za a saka mishi dukkanin waɗansu yakayyakin kwamfuta fiye da guda ɗaya. Misali Mini Case shi za a iya saka mishi Hard Disk guda ne da kuma CD-Rom ko Floppy guda. Amma Midi Case shi zai iya ɗaukan daga sama da ɗaya zuwa abin da bai wuce uku uku ba. Shi kuwa Full Tower kusan zai ɗauki daga sama da uku zuwa bakwai har wani lokaci ya kai goma. To kaga a nan zaɓi ya rage gare ka. Duk wanda ka ke buƙata a yanzu ka sani, idan kana buƙatar kaya kaɗanne, to ka san wanda za ka sayo, idan kuwa kana buƙatar kaya masu yawa ne, shima kasan wanda ya kamata ka saya.
Sannan kusan dukkan waɗannan a gidajen kwamfuta suna zuwa da tsari na ATX CASE sannan kuma za ka samu dasign iri-iri domin buƙatar ka, sannan kuma kusan dukkanin case da ake siyarwa a kasuwa suna zuwa da PSU (Power supply unit) wato matatar wuta. Ana kuma iya samun wasu irin case waɗanda babu PSU ajikinsu sai ka siya ka saka.
Idan aka zo maganar Case to ka sani idan za ka yi amfani da Mini ne to dole sai dai ka yi amfani da MICRO ATX MOTHERBOARD ko da ya ke akwai abin lura guda, ita kwamfuta da kayanta suna buƙatar sarari, saboda haka amfani da Midi ko Full tower ya fi.
ATX MOTHERBOARD
Motherboard ana kirenshi Print Circuit Boad (PCB) wato shine allon da ake shinfiɗa shi a cikin Case wanda ake saka mishi abubuwan da ka siyo da waɗanda za su taimaka mishi wajen aiki da shi. Shi wannan allo wanda a wannan lokaci ake samun mai tsarin ATX. Shi ATX Motherboard shine motherboard a jikin shi ake samun abubuwan da suka haɗe da shi, wanda ya haɗa da PS/2 port a jikin shi, haka kuma ake samun USB port, a sami Serial Port, da Parallela Port, sannan ake samun Graphics Card da Sound Card duk a tare da shi. Duk allon da ake samun waɗannan kaya a jikinshi, to allo ne wanda zai sauƙaƙa ma ka so sai wajen kayan da za ka haɗa ita Kwamfuta.
A wannan hoto da muka nuna, ka ga ya nuna abubuwa masu yawa da motherboard ya ke zuwa da su wanda a jikin shi akwai (Input/Output). Ga shi kuma yana zuwa da expansion slot .Shi PCI slot shine expansion slot da aka iya ƙarawa ita kwamfutar wasu alluna na daban kamar allo sauti “sound card” ko kuma a saka mata “Intranet modem” ko a saka TV card da dai makamantansu.
Shi kuwa PCI expansion slot wuri ne da ya ke ba ka damar ka ƙarawa kwamfutarka kuzari da ƙarfin fitar da hotona na PCI-E graphics card. Irin wannan motherboard zaka samu damar saka mashi graphics Card har Irin biyu na SLI ko kuma Crossfire Configuration.
Har ila yau, duk a jikin wannan motherboard za ka samu yana haɗe da Processor amma mai ramuka wanda ake kira da Intel 1366 Socket sannan kuma akwai wurin saka memory DDR3, ga wurin haɗa wutar da ta fito da ga PSU wanda ake kira da ATX 2.0 24 Pin power connector. Sannan kuma ana samun wurin da zaka saka Hard Disk ko CD/DVD irin biyu ga SATA (Serial ATA) ko kuma IDE.
PROCESSOR (CPU)
Processor ko kuma ka ce mishi CPU (central Processing Unit) shine ƙwaƙwalwar Kwamfuta, shi ne ya ke da alhakin sarrafa dukkanin abubuwa da ake umartar Kwamfuta da ta yi. Kamfanonin da suka fi shahara wajen yin shi wannan processor sune Intel da AMD. Duk wanda aka zaɓa cikin ɗayan wannan processor to ka tabbatar da cewar zai yi aiki da motherboard da zaka siya.
A wannan lokacin waɗannan kamfanoni guda biyu Inter da AMD sun daina yin processor mai tsarin GHz sun raja’a a kan kera processor biyu a cikin processor guda (Dual-Core). Domin idan a wannan lokacin aka ce kwamfutarka tana da processor ɗaya tare da 3.0GHz ta ke da shi, to wacce ta ke da Dual Core da 2.0GHz wannan tafi taka ƙarfi kuma sai tafi taka sauran yin aiki.
Amma yana da kyau kafin ka shiga kasuwa siyan processor ka fara tambayar kanka shin idan na haɗa wannan kwamfutar wane irin aiki zan yi da ita. Domin ka da kawai ka shiga kasuwa siyan kwamfuta, ka siyo babban processor alhali kai abin da za ka yi da kwamfutar bai wuce rubutu da bincika a Intanet ba. To duk wanda ya ke son ya yi rubutu ne ko ya rinƙa shiga Intanet to yana do kyau yasan cewar intel Celeron ko AMD Athlon X2 sun wadatar da shi.
Amma idan kwamfutar za a riƙa yin babban ayyuka ne kamar yin lissafi ko manyan aiki Database ko aiki Graphics ko kuma zai yi anfani da kwamfutar shi wajen buga ƙananan games to ya fara tunanin neman intel i3 da AMD PhenomX2 dukkan su dual-core ne, wanda ya ke nufin cewar kowanne processor yana ɗauke da wani processor ne da ban a jikin shi wanda kuma ko wane processor yana aiki shi na daban ne. Tunda haka ne, duk processor da ya kasance dual ne zai iya ɗaukar manyan ayyuka iri biyu lokaci guda, ba tare da kwamfutar tana ɗan maƙalewa ba. Misali ka kunna kwamfuta ka fara aiki da Microsoft Word sannan kuma kana aiki da CorelDraw ko Photoshop to tun da dual-core ne sai processor ɗaya ya tafi da matsalar binciken Virus, ɗaya kuma kana aiki Graphics da shi.
Amma idan kasan cewar wannan kwanfutar da zan haɗa zan yi manyan aiki da ita ne, kamar zan yi aikin gyaran hotuna masu motsi Vidao Editing, ko kuma irin aikin 3D ko aikin zane da manhaja ta CAD, ko kuma za ka rinƙa buga manyan Games masu tsari 3D to lallai sai ka shirya siyan manyan processors waɗanda ake kira da quad-core, ko kuma multi-processor kamar AMD FX, ko Intel i5 ko Intel i7.
AMD FX 400 da Intel i5 suna da processor huɗu-huɗu ne a jikinsu, shi kuma AMD FX 8120 suna da processor takwas ne a jukinsu amma shi intel i7, processor huɗu ne a jikin shi amma kuma ko wane ɗaya daga ciki yana aiki biyu ne, shi yasa operating system ɗin mutum yake ganin shi a matsayin processor 8 sannan dukkan irin waɗannan processor na zamani suna da tsarin 64-bit ne sannan Operating System da zai hau kansu, dole ya zama to 64-bit.
Mu tara a fitowa ta gaba In Sha Allah
Comment makranta nakeso inyi