Sama da dakuna miliyan biyu a Facebook da Gmail da Twitter ‘yan dandatsa (hackers) suka kwace ragamar gudanarwar su.
Bayan da wani kamfani mai lura da tsaro a harkar giza-gizan sadarwa (internet) mai suna Trustwave ya bankado da gano cewar masu dandatsar sama da wata biyu da suka gabata suka fara karbar bayanan sirri da kuma maballan da mutane suke latsawa a kwamfutocinsu.
Wadannan ‘yan dandatsa wadanda aka gano cewar uwar garken kwamfutarsu (Computer Server) wacce ta ke kasar Netherlands ta fuskantar da hankalinta zuwa ga wasu manyan gidaje na internet bayan da suka sani wata ‘yar karamar manhaja mai wuyar sha’ani mai suna Key-logger.
Adadin yawan gidajen sun hada da :-
318,000 Facebook accounts
70,000 Gmail, Google+ da YouTube accounts
60,000 Yahoo accounts
22,000 Twitter accounts
9,000 Odnoklassniki accounts (dandalin sada zumunci na kasar Rasha)
8,000 ADP accounts
8,000 LinkedIn (LNKD)accounts
Kamfanonin ADP da Facebook da LinkedIn harda Twitter sun sanar da cewar tuni suka gane haka kuma sun dauki mataki na canzawa mutanen da abin ya shafa mabuden sirrinsu (password). Ko da yake kamfanin Google ya ki yarda ya ce komai a kan batun. Su kowa kamfani Yahoo sun yi kunnen uwar shegu da lamarin.
Daya daga cikin ma’aikata a wannan hukuma ta TrustWave mai suna Miller ya tabbatar da cewar har yanzu babu wanda zai iya fadin yadda wannan virus ya shiga cikin kwamfutocin mutane ba. Ana tsammanin wadannan ‘yan dandatsa sun yi amfani da wannan manhaja ta Key Logger suka daura ta a kan uwar garkensu a hanyar da bayanai a Internet su ke bi (Proxy Server), saboda haka ya na da matukar wahala a gane adadin kwamfutocin da suka kamu da wannan cuta.
Ana ganin cewar sama da bayanan sirri da aikawa da manyan data 41000 (FTP Account) shima sun sami nasarar dandatse shi. Duk da cewar ba a da takamaiman yaushe ‘yan dandatsan suka fara wannan ta’adi, amma Miller ya na ganin cewar tun ranar 21 ga watan Oktoba na 2013 suka fara wannan karbar wannan sako a cikin sirri.
Duk da cewar kamfanin TrustWave ya samu nasarar gano uwar garken wadannan ‘yan dandatsa, ya tabbatar da cewar wannan ba ita kadai bace Server da ake shirya irin wannan almundahana da ita ba.
Ba ta hanyar yin scanning na kwamfutarka ba kadai zaka iya gane cewar ta kamu da irin wannan virus, ka na iya kare na’urarka ta hanyar updating antivirus dinka da kuma samun antivirus me lasisi.
Saboda haka muka sanar da duk mutumin da yasan cewar daya daga cikin dakin da yake mu’amala da shi a internet yana da mahimmanci ta ya canza password dinsa zuwa password mai karfi.
Rashin yin haka zai iya sanyawa a goge account dinka ko kuma ayi amfani da account dinka wurin cutar wa wadansu.