Assalamu alaikum malam Salisu Webmaster. A gaskiya na ji daɗin karanta wannan posting din (MENE NE SYSTEM UNIT?). Don wallahi na karu da abubuwa da dama, sai dai kuma ina da waɗansu tambayoyi kamar haka.
(1) Na ga a jikin system dina wajen zaman RAM har guda biyu ne kuma daya ne a jiki 4GB, shi ne ya sa na ce ko zan iya sayan wata 4GB din na kara mata?
(2) System ɗina kirar Hp Pavillion Dv6 ne Mai configuration kamar haka. 500GB HDD, 4GB RAM, 4.4system Riting 2.3GHz, Core i5 Processor amma kuma sai ta rinka slow, wallahi malam ba karamin slow take yi ba kome ya sa?
- Me ye bambanci da fa’idar kowane processor daga cikin wadannan? Single core, dual core, core i3, core i5, core i7. Ko me ye fa’idar ko wanne da kuzarinsa? Allah yataimaka ya bada ikon amsawa amin.
IBRAHIM MUH’D. Port Harcourt. Junairu 16, 2014 da 4:06 dare
Amsa:
Wa’alaikumus salam, Malam Ibrahim muna matuƙar godiya da irin kokari da ka ke yi na yawan bibiyar rubuce-rubucen mu, da fatan ba za ka gajiya ba.
(1) Amsar tambayarka ta farko ita ce “Na ga a jikin system dina wajen zaman RAM har guda biyu ne kuma daya ne a jiki 4GB, shi ne ya sa na ce ko zan iya sayan wata 4GB din na kara mata?” To babu shakka duk ramukan da ka gani a jikin kwamfutarka wanda ake saka RAM a jikinta to dama ce ake baka cewar zaka iya kara wani. Domin su kamfanonin da suke yin Motherboard (Uwar Allo) da kamfanonin da suke haka kwamfuta irin su HP da Dell da makamantansu suna yin su ne daidai da yadda mutane za su iya siya ba tare da lura da girman RAM ko Processor ba.
Su irin wadannan kamfanonin da suke yin motherboard suna rubuta irin karin girman da za a iya karawa ita kwamfutar, misali idan kwamfutarka ta zo da 4Gb Ram kuma ka sami wani wurin kara wani, to da zaka dauko asalin takardar da kwamfutar ta zo da shi ka duba za ka ga sun fadi cewar za a iya karamata RAM da ya kai misali 16GB. Abin da suke nufi shine idan rami biyu ne to zaka iya saka mata RAM 8GB har guda biyu, wanda shi girman RAM a kwamfuta kamar yadda muka yi bayani a wannan darasi na MENE NE SYSTEM UNIT? Mun fada cewar amfanin RAM a cikin kwamfuta shi ne sararin da kwamfuta ta ke bukata domin iya bude shafuka na application daban-daban.
Saboda haka zaka iya kara mata RAM amma kuma dole sai ka duba Manual da ta zo da shi ka ga har zuwa girman RAM nawa za ta iya dauka.
(2) Tambayar ka ta biyu ita ce “System ɗina kirar Hp Pavillion Dv6 ne Mai configuration kamar haka. 500GB HDD, 4GB RAM, 4.4system Riting 2.3GHz, Core i5 Processor amma kuma sai ta dunga slow, wallahi malam ba karamin slow take yi ba kome ya sa?” Wannan irin kwamfuta da irin kirar da aka yi mata lallai bai kamata ta yi nauyi ba, ko da yake wani lokaci komai karfin da kwamfuta ta ke da shi wani lokaci taka yi nauyi a dalilin wadansu abubuwa kamar haka.
- Yawan aiki da ita: wannan dalilin ya na sa mutum ya yaga kwamfutar tana dadewa kafin ta tashi, domin a farkon lokacin da take sabuwa doki da jin dadi ba ya baka dama ka gane cewar tana tafiya da sauri ko kuma bata yi. Amma da zarar ka fara sabawa da aiki da ita, saurin da kake yi sai ya wuce wanda take yi, sai ya kasance ka kosa mutuka alhalin ita kwamfutar tana tafiya kamar yadda ta saba ba tare da ta canza ba.
- Wani lokaci kwamfuta ta na yin nauyi a sanadiyar wadansu manhajoji (application) da ake daura mata. Wadansu manhajoji ba wai suna zama kawai a cikin babbar ma’ajiya kwamfuta ba ne kawai, su na zama a cikin manhajar da take tashin kwamfuta, ko kuma manhajar da kwamfuta take yin amfani da shi duk lokacin da za ta shi. To irin wadannan application idan suka fara yawa sai su rika rike kwamfuta a wurin tashinta. Shi ya sa da za ka sake karanta mukalar mu da muka saka me taken RASHIN TASHIN COMPUTER DA SAURI duk irin matakan da za ka bi domin ka sa kwamfutar ka da rika yin sauri wurin ta shi za ka kara saninsa. Amma ina son ka sani cewar irin wannan kwamfutar tana yin nauyi ne kawai a wurin tashinta ba wurin sarrafa manhaja ba. A lokacin da ta gama tashi ka bude wata manhaja mai karfi da girma kamar CorelDraw ko Photoshop ko AutoCAD da dai makamantansu ka ce zaka yi aiki zaka ga ne cewar lallai tana da karfi.
(3) Ita kuwa tambayar ka ta karshe ta ce “Me ye bambanci da fa’idar kowane processor daga cikin wadannan? Single core, dual core, core i3, core i5, core i7”. Wannan tambaya ita ma amsar ta tana karkashin wannan darasi na MENE NE SYSTEM UNIT? A wannan darasi mun fadi amfanin processor, wadannan core da ka ji ana magana yana magana a kan processor na kwamfuta ne, shi kuwa processor da kwamfuta take da shi, yana da manyan gidaje guda uku, Control Unit da Arthmetic/Logic Unit da kuma Rigista duk wannan abubuwan mun riga mun yi bayanansu a wannan darasi.
Amma idan zamu yi maka bayani a cikin Hausa mai sauki, shi ne a salin processor misali kamar Pentium 4 yana da daki guda na na wadancan dakuna, amma mai dual core yana da daki guda bibbiyu saboda haka idan kwamfuta mai single core (processor daya) zata yi minti biyu kafin ta gama sarrafa bidiyo (rendaring) to waccan mai dual core minti daya zata yi. Haka mai core i3 ita tana da dakuna uku-uku ne na wadancan dakunan. Idan kwamfuta mai core i3 za ta minti daya tana abu mai dual core zata dauki minti daya da rabi, haka abin ya ke.
Dalilin da ya sanya wacce take da core i7 ta fi kowacce sauri, saboda dakunan da bayanai suke shiga guda bakwai ne, a lokaci guda sakwanni suna iya shiga ta hanya guda bakwai ta sarrafasu ta fitar da su ba tare da daukan lokaci ba.
Da fatan wannan amsoshin da muka baka zai gamsar da kai da ma duk mai irin wannan matsala.
Allah ya biyaku from Abu-Ammar