Na bi wannan mataki ne domin na bayyana abubuwan da ke makure a cikin zuciyata game da dan bar da aka dora na gudanar da mulki a Jihar Katsina. Na kuma soma kokawa ne tun kafin tafiyar ta yi nisa saboda a sa wa tayoyin motar tafiya iska a kuma tabbata an sa wa notocin motar giris, don jin dadin tafiya.
Mai girma Gwamna, wadannan batutuwa da zan zazzage a nan, su ne muka zazzagawa wa tsohon Gwamna Shema lokacin yana kan mulki, amma canjin da muke tsammani bai samu ba har ka hau karaga. Abin da kawai zan yi a nan shi ne cire duk inda sunan Gwamna Sheme ya fito in maye shi da naka, domin mu ga ko canjin da aka yi mana alkawari zai samu kamar yadda yawancin mu ke bukata.
Ya mai girma Gwamna, ranar litinin, wato 28 ga watan Mayu 2012, na yi bikin cika shekara daya na samun ganawa da Gwamna Ibrahim Shehu Shema na jihar Katsina ta fuskar yin irin wannan rubutu, ganawa irin wadda ka yi da dattawa da kuma wasu daga cikin masu fada a ji a jihar Katsina ranar Asabar 12 ga watan Satumba, 2015. Ita wancan ganawa da Gwamna Shema, tamkar irin taka ganawar ce, ita ma Gwamna Shema ya nemi ganawa ne da duk wasu masana da suka samu kai koluluwar karatunsu na zamani, wato masu digirin digirgir da kuma Farfesoshi, ‘yan jihar Katsina. An yi wannan ganawa ce a Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua da ke Katsina bayan laccar da aka gabatar domin bikin hawan Gwamna Shema bisa karagar mulkin jihar a karo na biyu. Ita kan ta laccar da Mai Shari’a Umaru Abdullahi ya gabatar, abin tunawa ce, abin tinkaho ce, domin kuwa ta nuna cewa Gwamna Shema zai iya tattara mutane domin su ba shi shawara, ya kuma saurari mai dadi ko masar dadi. Wannan shi ne kila ya sa mani kwarin gwiwar da ta sa na amince in halarci taron ganawar da Gwamnan a kebance ba tare da hayaniyar sauran jama’a ko ‘yan jarida ba.
Amma duk wadannan abubuwa ba su ne makasudin yin wannan sharhi ba a yau. Niyyata a yau ita ce na kwance jakar da nake dauke da ita tun samun waccan damar ganawar da muka yi da Gwamna Shema, a shekarar 2011. Jaka ce da ke dauke da batutuwa da nake ganin za su yi mana jagora wajen kara fahimtar yadda gwamnati ke gudana da yadda sauran mutane da ke kusa da gwamnatin ke mu’amula da ita da ma kuma yadda wadanda ke nesa da ita ke mata kallon kitsen rogo da kuma uwa-uba yadda shi talakan ke faman kasancewa talaka duk da cewa wai shi ake wa mulki ko kuma in ce shi ake mulka.
Abin da ya burge ni a lokacin waccan ganawa da Gwamna Shema shi ne yadda Gwamna ya gayyaci masanan jihar Katsinar, aka kuma zauna, zama irin na gurguzun al’umma, ba Sarki balle Talaka domin a fahimci juna, a kuma ba juna shawara kan yaya za a ciyar da jihar Katsina gaba. Gwamna Shema ya gaya wa Daktoci da Farfesoshin jihar Katsina cewa, ya tara su ne domin a gaya masa inda ya yi kuskure a baya domin ya gyara, a kuma bayyana masa inda ake neman a mayar da hankali a gaba, domin a nazarta, a kuma kokarta jan akalar aiki zuwa can.
Shawarwarin da aka bayar ba za su kasaftu a nan ba, amma duk da haka Gwamna Shema ya saurari duk wanda ya ba da gudunmuwar yadda yake ko take son a tunkari lamurra.
Wasu gudunmuwar tasu ta gina kasa ce, wasu kuma domin gina kai da kai ne. Amsoshin da Gwamna Shema ya bayar da alkawurran da ya yi su ma abin dubawa ne, ba kuma inda ya fi birge ni irin shan alwashin da ya yi na tabbatar da zai yi aiki da shawarwarin da aka ba shi.
Ba zan iya kawo dukkan shawarwarin da aka ba shi ba, da kuma yadda ya yi alkawarin shawo kan matsalolin ba, amma zan mayar da hankali kan shawarwarin da ni da irina muka bayar da kuma irin alkawarin da Gwamna Shema ya yi game da su, domin a gane yadda ake tufka da warwara a fagen mulki, kila ta haka a tsinci dame a kala a lokacin gudanar da naka mulki yanzu.
Abu na farko shi ne alakar da ke tsakanin Shugabanni da Talakawa da kuma fafutikar zaman lafiya. Ni a nawa ganin kamar yadda na bayyana, ba yadda za a yi a samar da ingantaccen zaman lafiya sai in shugabanni da mabiya sun canza hali game da sha’anin mulki. Ba wani abu ya jawo matsalar da ake cin karo da ita a halin yanzu ba, sai lalacewa da tabarbarewar sha’anin mulki. Hanyar da nake ganin za a samar da zaman lafiya shi ne masu mulki su kusanci talakawa, su bar warewa can gefe suna kyamar wadanda suka zabe su. Idan suka yi haka, suka kuma inganta mulki da yin aikin kwarai, aka kuma samu wasu daga cikin al’umma da ke nuna wa shugabanni inda suka kauce, ba da son rai ko neman abin duniya ba, to za a samu zaman lafiya a tsakanin al’umma. Dole ne idan ana neman zaman lafiya da raya kasa a samu masu kururuwa game da cin hanci da almundahana da lalacewar lamurran mulki a kowane fanni na rayuwa.