38.1 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

Mene ne banbanci dake a tsakanin Windows XP da Windows 7

A gaskiya Malam Abbas Babayo Gombi akwai banbanci mai yawa dake tsakanin Windows Xp da kuma Windows 7, kadan daga cikin banbanci dake tsakanin su shine

1)Bangaren tsaro:- Kamfanin Microsoft sun kara USER ACCOUNT CONTROL tun daga windows Vista har zuwa windows 7 wanda babu shi a cikin XP, shi kuma aikin da wannan UAC yake yi shine ya lura da hanyar da duk wani program da yake son yayi installing kanshi a cikin computer ya zamanto ba zai yi ba sai ka bashi izini, idan kana amfani da windows Vista ko 7 idan kana son kayi installing wani program sai kaga wani dan karamin windows ya bude yana tambayar ka Allow ko Cancil, mene ne dalilin da yasa aka kirkiri wannan tsari, domin ko wane irin Virus da zai shiga computerka sai yayi installing kanshi kafin ya shiga, shi yasa suka kara wannan bangaren tsaro tunda dai sai yayi installation zai yi ta’adi dole sai ka bashi dama tukunnan ya zauna a computer ka, to kaga babu wanna a Windows XP, shi yasa yawancin Virus da suke shiga XP ba sa iya shiga Win7.

2) sannan kaga akwai banbanci mai yawa a wajen karbar Hardware! dukkanin hardware da zaka yi installing idan akan Win7 ne to zata zo da shi amma a wani WinXP sai ka nemo, haka wajan yadda program suke zaka a cikin computer da kuma rage matsalar lalacewar su a sanadin Virus shima an cireshi a cikin Win7.

3) Idan muka dawo ta wajen yadda Win7 yake iya handling files da folder shima an sami ci gaba

4) Windows Defender da Windows Update suma an kara musu karfi matuka wanda matukar kana da win7 sannan koda wani lokaci ka na Updating Windows din ka kuma kana Updating Windows Defender naka to ko da baka saka Anti-Virus ba kusan irin Virus da suke damun mu a Najeriya computer ka tafi karfin su.

5) Anytime Upgrade kusan idan kana amfani da Win XP home kana son ka mayar da shi Win XP Pro, dole sai dai kayi upgrading ta hanyar amfani da CD na Win XP Pro kafin ka iya upgrading din shi, amma koda Compterka ta zo da Win 7 Home kana son ka mayar da ita Win 7 Ultimate baka bukatar CD ko DVD abin da kake bukata shine kawai Serial Key na Win 7 Ultimate idan ka samu sai ka yi typing Anytime Upgrade a jikin search box na windows take zai fito ka saka wadannan serial numba ba tare da ya hada ka da internet ba yayi maka upgrading.

6) Ta wajen system yayi crashing ko kuma nuna maka blue screen of death Microsoft sun cire wadannan matsalolin da ake yawan samunsu tare da windows Xp wanda zai yi matukar wahala OS din ka yayi crashing ko kuma idan wani matsala ta faru ka kasa recorvery document din ka.

A takaice wannan shine kada daga cikin banbanci da ake iya samu tsakanin Win7 da XP. Amma maganar ka ta karshe na cewar ya zaka yi ka komar da Windows 7 zuwa Windows XP, a ka idan computer tazo da OS da yake babba ba bu wata hanya babba wacce aka bayar domin mutum ya iya downgrading OS dinshi, amma za ka iya upgrading daga XP zuwa Vista daga Vista zuwa Win 7, amma za ka iya share shi OS 7 da kake da shi ka mayar da shi XP amma wannan ba ana kiranshi da Upgrading bane ana kiranshi da FRESH INSTALLATIONS na gode da fatan zaka yi hakuri na rashin baka amsa da bamu yi akan lokaci, wannan domin mu tabbatar da mun baku abun da yake ingantacce kuma sahihi. Na gode Allah yabar zumunci

5 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img
Previous article
Next article