Ya ka ke rubuta password dinka a akwatin imel din ka? Ko kuma na facebook ko kuma twitter da duk dai wani shafin internet da kake shiga. Idan har kai ma’abocin kokarin rubuta lambobi masu sauki ne kamar 123456, ko kuma 98654, ko kuma kana amfani da sanan suna ne wajen password din ka kamar salisu, Ibrahim, ko kuma kai mai son saka sunan masoyiyarka ne kamar Fatima, ko Aisha, ko kuma kai ma’abocin rubutun kalmomin soyayya ne kamar iloveyou, ko kuma fatimamylove ko kuma thankyou, to ina tabbatar da cewar wannan password din naka zai zama mai sauki wajen ganowa ko bai zai yiwa hackers wahalar shiga ba domin sacewa ko kuma aika maka da virus cikin shafukanka ba.
Ga yadda ya kamata ka rubuta password dinka
- Karanci harrufa goma (10)
- Ya kunshi kananan harrufa da manya a cikin sa
- Ya kunshi alamomin rubutun na musamman
- Ya kasance akwai lambobi a cikin su
- Kada ya kunshi sunan masoyi, ko mahaifa da makamantansu
- Kada ka yi amfani da sanannun kalmomi, kamar iloveyou, ihateyou, ihateu, da makamantansu
- Kada kuma ka yi amfani da ranar haihuwarka kamar, oct1977.
Ga misali
Dun!yarComput@r98 – Wannan password yayi karfi sosai.
To ka yi la’akari idan ka kirkiri password dinka da wannan hada hade ya kake gani?
Mungode da wannan taimakon da muke. To don Allah yaya mutum zaiyi ya canza passward dinsa na email da facebook dinsa cikin sauki
Madalla da wannan bayani da kukai mana, na gode Allah ya saka da alkhairi. Tambaya ta ita ce: me yasa bana iya downloading din film a waya LG GX 300? haka kuma bana iya display din video a utube.
ba ko wace wayar hannu ba ce take da kayan da zasu taimaka wajen nuna video na internet ko kuma youtube ba, sannann kuma ba a iya downloading video da waya matukar ba anbaka hanyar saukar da shi bane
Gaskiya wannan shawara zata amfani mutane sosai، Allah saka da alkhairi.
shin meye dalilin da wani lokaci idan zan bude akwatin email daina sai yadinga cemun pasword badai dai bane bayan kuma na tabbatar da pasword din hakane
Abubuwa guda biyu ke iya jawo haka, na farko kodai su kamfanin naka na email din suna fuskantar matsala tare da server din su ko kuma network din ka yana da matsala
godiya muke webmaster
haka nefa mungode
kai lale, marhaban da wannan namijin kokari na WEBMASTER. Allah ya saka da hairan.
Nagode da wannan shawara taka webmaster. Allah ya taimaka mana. Ameen.
Mungode Allah Ya bada lada..
Agaskiya bayanan ku ba karamin taimaka mana suke yi ba Allah ya biya ku Ameen
Godiya mai tarin yawa dangane da wanan kokari mungode
Salam
Wa alaikumus Salam
Kamar haka…sa32%@rrn.com nasan wannan password din maikarfine
Mal Salisu, Allah Ya Saka maka da alheri irin fadakarwa, shawarwari da gane-mini-hanya da kake Dora mutane akai. Akwai wani VIRUS watau ‘Monkey Virus’ Wanda yanzu ya addabi wayoyin android, kuma gashi akasarin antivirus da yawa basu iya kawar dashi. Ko minene shawara?
Gaskiya wannan bayani ya gamsar dani kuma a kalla yasa na chanza tsarin password dina, muna godiya da wannan kamfani naku Allah ya biya muku bukatunku.