32.4 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

Yaya Za Ayi In Yi Amfani Da youtube a wayar hannu

A wannan dan takaitaccen rubutun zan yi magana akan abinda mutane da yawa suke yin tambaya a dandalin mu na facebook da kuma wuraren karatun akan matsalar da suke fuskanta idan suna son su kalli wani video a youtube ko kuma dai su kalli video a internet da wayar tafi da gidanka.

Wanann kuwa tana daga cikin matsalolin da mu kanmu a Duniyar Computer muka fuskanta da mutane da yawa suna son kallon videon da muke yi wanda suke warware matsaloli daban-daban game da abinda ya shafi computer da waya baki daya.

To, shi dai kallan video da waya musamman a dandalin youtube abu ne mai wahala idan aka yi la’akari da yanayin tsarin da su youtube suke da shi na yadda ake kallon video a gindan. Suna da tsari guda biyu wanda kuma yake goye akan tsari guda.

Youtube sun ta’allaka videon su akan za a iya kallonshi a computer ga wanda yake amfani da browser ta zamani wacce kuma take da player ta adobe flash wanda duk wanda bashi da wannan abubuwa guda biyu to, ba zai yiwuba ya iya kallon video a youtube.

Sai hanya ta biyu shine sabon tsarin da su youtube suke fito da shi a sakamakon sabuwar fasaha ta HTM5 wanda yake iya baka damar ka kalli video da aka saka a internet ba tare da adobe flash player ba. Duk wanda ya saka video dinshi a youtube kuma ya zabi tsarin cewar HTML5, to dole sai browser ta zamani wacce kuma take da alaka da HTML5 zata iya bude wannan videon har kuma a iya kallon sa.

Hanya ta karshe kuwa ita cewa tsarin da kamfanin youtube suka da shi ga wadanda suke son su kalli video amma da wayar hannu, wanda shi ba kowane video ba ne, sai video da aka saka shi da tsarin .3gp wanda daman shi shine tsarin da waya take iya budewa.

Masu amfani da iPohne da android:

Idan ba wai kana da waya ta zamani bace kamar wayar da ke da fasaha ta IPhone ko android to suna da zabi daya kacal da zasu bi domin kallon video a youtube amma shima wannan video sai wadanda muka ce an saka sune da tsarin .3gp.

Amma masu tsari wayoyin da suke da fasahar zamanin na IPhone ko android su suna iya kallon ko wane irin video a youtube ta hanyar amfani da application da kamfanin YouTube suka yi domin masu irin wadannan wayoyin. Da farko dai idan kana son ka ji dadin kallon video a internet dole sai idan kamfanin layinka suka bada goyon bayan tsarin 3G, wanda shine kawai hanyar da kamfanonin layikan waya zasu iya badawa domin kallon video domin kallo da sauri. Shi karan kanshi application din da youtube suka kirkiro suna bukatar a kalla kana da damar shiga internet ta dayan hanyoyi guda biyu, ko dai 3G ko kuma Wi-Fi.

Masu amfani da Nokia da Sony Ericsson da  windows da makamantansu kuwa:

Idan kuwa kana bukatar ka kalli video a youtube da daya daga cikin wadannan wayoyin da muka ambata a sama, to ka biyo wannan matakai.

  • Ka shiga website din youtube da wannan adireshi http://m.youtube.com/app da wayarka.
  • Bayan ka shiga zai fito maka da application din da wayarka take dubaka domin ka iya kallon video a youtube, bayan ya bayyana sai ka sauke shi (downloading)
  • Sai kayi Installing shi wannan application a cikin wayarka.
  • Idan ka samu damar yin haka to, video daga youtube zai rika kalluwa a wayarka.

A wasu lokuta sai ka dan daidaita tsarin shigarka internet idan ka sami matsala da budewar video din.

Java Midlet

Ga wadansu wayoyin Nokia da Sony Ericsson zaka iya amfani da Java Midlet wajen iya kallon video daga youtube.

Wadansu fa’idoji

Idan har zaka iya kallon video a youtube ta wayarka, to, zaka iya:

  • Daura video kai tsaye kaima zuwa ga youtube. Ma’ana kaima zaka iya daura video ta wayarka zuwa youtube website domin mutane su kalla.
  • Videon da kake kallo zaka iya watsashi ga sauran mutane suma su kalla.
  • Zaka iya recording na dvd ka watsashi.

15 COMMENTS

  1. Assalamu alaikum nima tambayana shine game da yadda xa a yi amfani da youtube a wayan hannu kuma in xai samu ina son reply ta email dina ne nagode.

  2. *Slm nidai maganata anan shine dan allah inaso insan inda kuke sannan kuma inaso inshiga schl, dinku dan allah idan allah yasa kungani kuturo min da amsar tambayoyina ta hanyar email address. Nagode allah yabaku nasara akan al amuranku na yau da kullum (DUNIYAR COMPUTER)

  3. Salam ni malam ina da wata matsala take da muna awaya na duk adin da zanyi dawlaod bayan dan wani lokaci in zan shiga seyarin ga ce min erro application.kamar irin su mozat shine nake so malam yayi min karin bayani akai

  4. Assalamu alaikum inatanbaya gamida wayata nayinayi inyikallon yutubi amma abin yakiya sunanta samsung c3100 koyaya zanyi ayimin bayani allah shikara ilime

  5. Ina da wayata nokia c1- 01 amma bana iya kallon youtube a cikin ta kuma naga wani yan yi da tasa wayar shima kuma c1-01 na tambayashi amma yace dani shima a haka ya siyata agurin wani dan allah ku taimaka iringa kallon youtube a wayata na gode allah ya saka muku da alheri amin.

  6. Kai duk mai bada irin wannan ilimin domin amfanin jama’a muna fata Allah yayi masu mafificin sakayyar Aljannah amin. Agaskiya nakaru daku matuka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img