Duniyar Musulunci ta yi Allah Ya tsine da harin da aka kai garin Makka wanda Allah Ya ba jami’an tsaro na Saudiyya ikon kakkabo wannan makami mai lizami da wadannan ‘yan ta’addan suka harbo zuwa birnin Makka mai daraja.
Wannan makami da ya fito daga wani gari da ake kira da Saada gari ne da ke gabar (border) kasar Saudiya wanda garin yana cikin kasar Yamen inda wata kungiyar shi’a da ake kiranta Alhusiyyun suka kawo wannan harin.
Irin wannan harin ba shi ne na farko da ake kokarin kawowa wadannan garuruwa masu alfarma ba, kusan a cikin sati guda an sami nasarar kakkabo irin wadannan makamai masu linzami har sau biyu.
Da farko dai ya kamata duk wani musulmi ya sani cewar wannan addinin musulunci da muke takama da shi yana da inda aka kyankyashe shi, kuma kodama baka da ra’ayin wani kungiya ko bangare a cikin addini in dai kai musulmi na gaskiya ne ka yi imani da rukunan musulunci guda biyar, ga wadanda suke ikirarin su Ahlussunna ne Wal Jama’a wanda ya tattara dukkanin wasu kungiyoyi da akidu na Musulmai banda masu da’awar Shi’a, kasan cewar rukuni na biyar shine ziyartar dakin Allah mai alfarma.
Komai kiyayya da mutum yake da ita ga kasar Saudiya, yasan cewar Allah ya albarkace ta da abubuwa guda biyu da duk duniya babu wata kasa ta samu wadannan abubuwan, saukar wahayi na farko a garin makka na karshe a garin Madina, haihuwar Manzon Allah a garin Makka, mutuwarsa a garin Madina, wadannan garuruwa har duniya ta nade wadannan ni’imomi ba za su canza ba. Komai bakin cikin mai bakin ciki da kiyayyar mai kiyayya.
Duk Musulmi ya sani cewar idan lokacin aikin hajji ya zo, burinsa shine yaje ya sauke farali a wannan gari na Makka. Babu wani musulmi na arziki da gaskiya da yake inkarin wannan gari na Makka da cewar ba tsarkakken gari ba ne, babu wani musulmi da ya ke shakkar cewar yana daya daga cikin garin da hatta tsiro da dabbobi a kwai lokacin ba a farautar su ko kuma cutar da su.
Shi yasa wannan gari shi kadai ne garin da koda kana boye ne ka yi niyyar ko da a zuci ne, ka ce idan na je sai na yi sabon Allah ko ta’addanci, Allah zai rubuta maka zunubin kar ka aikata ne, shi yasa duk mutum da aka kamashi yana da niyar yin ta’addanci da wadannan birane guda biyu yake yanke mishi hukuncin kisa.
Akwai kungiyoyin musulmai guda biyu da suke da burin garin sun rasa dakin Ka’aba ko kuma sun keta alfarmar garin Makka da Madina, wadannan kungiyoyi su ne, Shi’a da kuma Khawarij. Shi’a tana da ikirarin ganin an keta alfarmar garin Makka da Madina saboda su a ganin su Manzon Allah bai kamata a ce yana kwance a wannan kasar kafira ba, kasa ce wacce bata da tsarki, kasa ce wacce makiyan jikokin Manzon Allah suke kwance a cikinta, sune wadanda suke ganin kuskure aka yi wurin aikowa da manzon Allah annabci, sune suke ganin manyan aminan Manzon Allah sun ci amanarsa, sune suke ganin aminan Manzon Allah sun hana yar sa gadon ta, da dai maganganu akan ganin cewar wannan garuruwa ba su zama masu tsarki ba. Da wadannan dalilai ne malamansu suke bada fatawa a cikin littattafansu cewar kaiwa garin Makka hari ba laifi ba ne, sannan kuma kashe duk wani mutum da ba su ba lada ake samu.
Khawarij kuwa mutane ne masu akidar Ahalussunnah wadanda suke fassara Ayoyin Alkur’ani da Hadisan Manzon Allah da ra’ayinsu, basu yarda da duk wata magana da ta fito daga bakin wani malami ba sai dai malaman su, ba su yarda da tawilin da ya saba musu ba, sun yarda da kashe duk wanda bai yarda da hanyar da suke kan ta ba, sun kuma halasta jinin duk wani musulmi da bai yi shari’ar musulunci irin wacce suka ce ita ce shari’a ba, suna iya kashe duk wanda Annabi SAW ya ce ya haramta kashe shi.
A watan Ramadana aka kai hari Masallacin Manzon Allah SAW inda yake kwance da bom wanda a lokacin dan kunar bakin waken da ya kai wannan harin Allah bai bashi sa’ar karasawa jikin Masallacin ba bom din ya tashi da shi, wadanda suka dauki alhakin kai wannan harin sune Khawarij wanda suke ganin gwamnatin Saudiya kafira ce, kuma duk da ittifakin duniyar akan cewar ita kadai ce kasa a Duniya da take yin shari’ar musulunci na gaskiya amma wannan bai kubutar da wannan kasa da barazar irin wadannan miyakun Kuraye masu sanye da fatun Akuya ba.
Shi kuwa wannan harin da aka kai, wanda duniyar Musulunci tayi Allah Ya Tsinewa duk wanda ke da hannu a kan wannan harin shi da yake da makami mai linzami ne aka aiko daga wannan garin na Saada wanda ‘Yan Shi’a da suke da suna Alhusiyyun suka kai ya sanya an fahimci cewar zai wahala mutumin da yake ikirarin musulunci na gaskiya ya kaiwa garin Makka hari.
Akwai abubuwa da jama’a da dama ba su sani ba game da wannan harin da aka kawo da kuma shin wane irin makami aka yi amfani da shi wurin kai wannan harin ba? A hakikanin gaskiya, irin wannan makami ba kasafai ake samun shi a wurin kungiyoyin ‘yan ta’adda ba, kasancewar shi wannan makami da suka yi amfani da shi yana tafiyar kilomita dubu ashirin ne a sa’a guda (20,000 km/h). Wanda duk ya san wannan gari na Saada ya san cewar tsakanin sa da garin Makka bai wuce kilo mita dari biyar ba (500 km) wanda yake nuna cewar idan aka jefa wannan makami mai linzami cikin minti daya da rabi zai kai garin Makka.
Sojojin Saudiya Allah Ya basu nasarar kakkabo wannan mugun makami a cikin minti daya da dakika ashirin wanda ya nuna saura dakika goma wanda su ‘Yan Shi’a suka harbo a ranar 27 ga watar Oktoba 2016 da misalin karfe tare na dare (9:00pm) daga wannan garin na Saada dake kasar Yamen kusa da gabar garin Makka.
Kamar yadda hukumar tsaro ta Saudiya ta sanar cewar dakikoki tamanin da suka bata kafin su kakkabo wannan makami mai linzami sun yi kokarin ganin makamin bai fado a garin da yake da yawan jama’a ko kuma inda mutane suke yin hada-hada ba. Daukan wannan lokacin kafin su kakkabo wannan makami ya taimaka matuka wurin kiyaye rayukan mutanen da suke kauyen Barzah inda nan ne makamin ya fado.
Duk da cewar al’ummar wannan garin Barzah sun ga wannan al’amari amma kuma wannan bai hana su ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum ba.
Kamar yadda muka fada cewar wadannan kungiyoyi guda biyu Alhusiyyun da ISIS ba wannan karon ba ne kadai suka taba kai hari garin Makka ko Madina ba, duk da cewar Allah kowane lokaci yana tona asirin su, kuma yana sa ana gane makircin su a kodawane lokaci.
Wannan kungiya ta Alhussiyyun wacce kungiyar ‘yan shi’ar kasar Yeman wacce ke da tsattsaurar ra’ayi da kuma nufin ganin ta kasa gwamnatin shi’a da taimakon kasar Iran, an kafa ta ne a shekarar 1992. Suna kiran kansu da ‘Ansarullah’ wato masu taimakon Allah.
Duniya gaba daya a yanzu ta fahimci cewar gwamnatin Iran ita ce ta yi makircin kai wannan hari. Duk da cewar kasar ta fito ta barrantar da kanta daga wannan harin amma bata yi haka ba sai da kasashen duniyar suka nuna mata cewar ita ce ta sa a kai wannan harin kasa mai tsarki.
Kasar Saudiya tace daga shekarar 1980 zuwa yanzu kasar Iran ta kai hari kusan guda goma garin Makka wanda cikin ikon Allah duk lokacin da suka zo da irin wannan makircin sai Allah ya kubutar da su.
To bayan da su ‘yan Shi’an Alhusiyyun suka ga duniyar gaba daya tayi tofin Allah Ya tsine sai suka fito suka ce su ba manufarsu su kai hari garin Makka ba, wai su sun so ne su kai hari filin tashi da saukar jirage na Sarki Abdul Aziz da ke Jidda. Kuma sun yi haka ne domin suna neman wanke kan su daga zargin so rusa dakin Allah mai alfarma.
Kaiwa garin makka hari kamar kaiwa musulmai biliyan daya da milayan dari biyar ne hari (1.5billion) da suke cikin duniya, kuma Musulman duniya baki daya suna bayan kasar Saudiya game da taba Masallacin Harami ko kuma Masallacin Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa Sallam.
A karshe muna kira ga jama’ar mu wadanda suke wannan kasa ta Najeriya da suke da’awar Shi’a su sani cewar wannan da’awar babu inda zata kaika sai ga kiyayya ga garin Makka da Madina, da kuma karyata Annabicin Manzon Allah, da cin mutuncin wadanda ya barwa wannan addini har muka same shi, da karyata ayoyin kur’ani, da fito na fito da shari’ar Allah, da kuma kai mutum ga wutar Allah.
Allah ka tsare mana imanin mu da addinin mu, ka tsare Addinin Musulunci da Musulmai daga sharrin kowane me sharri da haddasa da kiyayya da ke ta da mugunta a duk inda muke, ya nuna mana gaskiya gaskiya ce, ya bamu ikon bin ta.
Allah ya bada lada malam, Ya Allah ubangijin ka’aba ka tsinema yan shi’a da duk wanda keda hannu aciki.
Ameen summa ameen, wannan abu dame yayi kama.