Utility Software suna wani ɓangare ne na System Software amma shi aikin shi shi ne lura da lafiyar Operating System da yadda abubuwa suke kaiwa da komowa a cikin taka kwamfutar. waɗannan ‘ya’ya na Utility sune suka da alhakin lura da devices da aka haɗa da kwamfuta da abubuwan da suke shiga da fita ta hanyar internet, da irin waɗanda suke lura da printer da dai makamantansu.
Karkasuwar Utility Software
Utility software suna da yawa wanda a wannan karatu ba za mu sami damar kawo muku dukkansu ba sai dai za mu yi ƙoƙarin kawo masu muhimmanci sosai duk da dukkansu suna da muhimmanci.
1. Add and Remove Hardware

Wannan yana ɗaya daga cikin Utility wanda yake lura da shiga da fitar kowane irin Hardware da aka haɗashi da kwamfuta. Abinda ake nufi shi ne duk lokacin da mutum ya saka wani hardware a jikin kwamfuta to Add and Remove Hardware shi ke da alhakin lura da shi, zai duba ya gani shin wannan hardware an taɓa saka shi a jikin wannan kwamfutar ko kuma ba a taɓa saka shi ba, idan ba a taɓa saka shi ba sai ya bincika a ɗakin ajiyar manhajojin devices akwai ilimin sanin yadda wannan Hardware ya ke yin aiki? Idan akwai sai ya ɗauko ya saka wa kwamfutar domin ta san yadda za tayi amfani da shi.
Idan kuwa ta duba ta ga babu ilimin wannan hardware sai ta nemi agaji a wurin kai mai harware ɗin wanda idan kana da driver ɗin sai ka saka mata, haka idan kai ma baka da shi sai ta nemi agaji ta Intanet, idan kana da intanet sai ta shiga idan kuma ba ka da intanet shi ke nan kwamfutar ba za ta iya sarrafa wannan hardware ɗin ba.
2. Add and Remove Software

Wannan shi kuma shi ke da alhakin duk wata ƙaramar manhaja da za a saka a cikin kwamfuta ya ɗauketa ya saka ta inda ya dace, tun daga ɗakin ajiyar manhajoji, ƙulla alaƙarta da Babbar Manhajar Kwamfuta da kuma yadda za a iya samunta a cikin kwamfutar duk lokacin da aka buɗe ita kwamfutar. Haka wannan Utility ɗin shi ke da alhakin iya cire duk wata manhaja da take cikin kwamfutar domin a lokacin da take ajiyar su waɗancan manhajoji ta kuma haddace duk ɗakuna da ta je ta zuba su, to duk lokacin da aka nemi a cire program to za ta sake bin waɗancan gidaje ta cire su.
Anti-Virus:

Kamar yadda da yawa daga cikin masu karatun wannan mujallar suka sani cewar Virus wani irin ɗan ƙaramin program ne da ake rubuta shi domin ya shiga kwamfutar mutane ya yi wata ɓarna ko kuma satar muhimman bayanai ba tare da mai ita ya sani ba. To Utility yana da ɗa wanda ake kira da Anti-Virus wanda aikin shi, shi ne tabbatar da cewar babu wani gurɓatacce Program da ya shigo cikin kwamfutarka ballantana ya yi maka ta’adi. Shi ya sa kowace kwamfuta tana da nata ant-virus da take zuwa da shi, wanda yake buƙatar kodawane lokaci ka rika shiga intanet kana ƙara saukar mishi da bayanan virus da suka shiga sababbi. Idan kuma na kwamfutarka ba shi da ƙarfi sai ka sayi na kasuwa waɗanda aka ƙarfafa da inganta ayyukansu.
Backup Software

Su ma Utility Software ne waɗanda aikin su shi ne su taimaka maka wurin tattaro abubuwa masu muhimmanci da ka yi ko ka ajiye a cikin kwamfutarka domin su ba ka damar taskace su a wani wuri domin ko ta kwana. Kowace kwamfuta tana da irin wannan manhaja wacce za ta iya ba ka damar ajiyar waɗannan ayyuka da ka yi, kamar aikin da ka yi na Document ko hotuna da ka zuba a Pictures Folder ko don ka ajiyesu a wani wuri cikin kwamfutar ko kuma ka taskace su a cikin wani wurin ajiya kamar External Hard Disk, ko flash da makamantansu. Idan kuma wanda yake cikin kwamfutar bai yi maka ba sai ka sami na kuɗi.
Disk Checker

Shi ma utility software ne wanda aikin shi shi ne tabbatar da lafiyar Hard Disk da suke jikin kwamfutarka, duk lokacin da aka kunna kwamfuta ko kuma aka kashe ta, Hard Disk ɗin kwamfutar files ne suke aiki to shi wannan Disk Checker shi ke da alhakin lura da mazaunin kwane file a jikin hard disk kuma ya tabbar da cewar Hard Disk yana cikin ƙoshin lafiya.
Disk Cleaner

Shi kuma aikin da yake yi shi ne ya tabbatar da duk wasu bola da kwamfuta take tarawa ko wanda mutum yake gogewa amma kuma ba sa barin cikin kwamfutar. To shi Disk Cleaner aikin shi shi ne ya tabbatar da irin waɗannan sharar ba a barsu ba.
Disk Defragementer

Shi ma Utility ne aikin da yake yi shine ya tabbatar babu wani aiki ko manhaja ko file da bai zauna inda ya dace ba, shi wannan Utility yana ɗaya daga cikin Utility masu amfani sosai, kasancewar babu wanda ya san mazaunin files ko folder na kwamfuta da kuma inda ya dace da su sai shi. Shi ya sa duk lokacin da mutum yake aiki sai kwamfutar ta mutu a daidai wannan lokacin file da kake aiki da su suna buƙatar su koma matsuguninsu na asali. To shi Disk Defragementer shi ke mayar da kowane file wurin zamanshi, sannan kuma yana mayar da kwamfuta ta riƙa tafiya da sauri.
Disk partitions

Shi ma utility ne da yake taimaka wa Babbar Manhaja wurin iya raba Hard Disk na kwamfuta ba tare da an rasa wani abu da ke cikin ta ba. Shi Disk Partition shi ake amfani da shi domin raba Hard Disk guda zuwa gidaje fiye da ɗaya. Shi ma kowace kwamfuta tana da nata amma idan kana son mai inganci sosai sai ka biya kuɗi domin siyanshi.
Device Driver
Wannan shi ne abu na ƙarshe da ake yin magana idan aka zo maganar System Software. Device Driver shi ne asalin ilimin da kwamfuta take buƙata domin ta yi magana da Hardware. Duk lokacin da aka yi sabon hardwara misali kamar printer ko keyboad ko irin su hard disk su kamfanin da suka yi, injiniyoyin da suka yi ta su suke da alhakin ganin sun rubuta program wanda idan aka saka shi a kowace irin kwamfuta domin ta fahimci aikinsa da yadda za ta sarrafa shi.
To wannan software da su injiniyoyin da suka yi wa wannan hardware shi ake kira da Device Driver, shi ya sa duk wanda ya sami wani hardware ya haɗa shi da kwamfuta amma kuma ba shi da driver ɗin shi sai ka ga wannan hardware baya aiki. A cikin kowane irin System Software akwai ɗaki na musamman da ake ajiyar irin waɗannan Driver ɗin. Misali lokacin da mutum yake ƙoƙarin ɗora Windows a cikin kwamfutarshi tana ƙirƙirar wata folda da take zuba mafi yawan hardware da ake amfani da su a cikin kwamfuta. To duk lokacin da aka saka sabon hardware a jikin kwamfuta to Add and Remover Hardware zai shiga cikin wannan foldar ya duba ya gani ko akwai Driver ɗin sa ko kuma babu.