Ba kowa bane yake da damar samun internet mai karfi, ko kuma wayar da take da RAM 3GB ko kuma 4GB. Har ila yau mutane da yawa suna iya samun damar shiga internet da 2G network tare da anfani da karamar waya mai amfani da 1GB ko kuma 2GB RAM kawai.
Kasanya a ranka cewa mafi yawan kafanonin kimiya a duniya sun fara yin kananan manhajojin da zasu wakilci mafi yawan shahararrun mahajojin su, domin anfanin masu kananan wayoyi.
Duka manyan manhajoji kamar na Twitter da Facebook da LinedIn da Google suna samar da kanan manhajoji domin wayoyi masu karancin girman RAM ko karfin internet wadanda ake kira da Lite apps ko Go apps a manhajojin Google.
A bangaran Facebook yana da karamar manhaja wato (Lite app) wacce take wakiltar babbar manhajar da kuma karamar manhajar tura sakonni wato (messenger).
Ita wannan manhajar ta shigo hannun mutane ne a shekarar 2015 wanda aka takaitata ga kasashe kamar Bangaladash da Ingiya da Sirilanka da makamantansu. Amma yanzu harda kasashen masu girman tattalin arziki suna amfani da wannan manhajar kamar kasar Amurka da Faransa da Ingila. Haka ana samun wannan manhajar ta Facebook Lite a wayoyi kirar Android da wayoyin Apple wato iOS.
Saboda haka bari mu duba wadannan manhajojin guda biyu muga da me daya tafi daya sannan kuma wacce ya kamata kai me karatu yayi amfani da ita a wayarsa.
SHAN BATIRI DA CIN WURI

Babban banbanci dake tsakanin wannan manhajoji shine cin wuri da suke yi a cikin wayar mutum. Misali ita babbar Manhajar ta Facebook tana da nauyin 58-50MB amma ita kuma Facebook Lite iya girman wurin da take ci shine 2MB.
Tunda girman 2MB wannan Lite take ci a waya wannan ya nuna cewar zata yi saukin girkewa a cikin wayarka kuma ba zata dibi wani yanki mai yawa ba na RAM din wayar haka zai taimaka wurin sarrafa wayar da sauri.

Shidan wannan Lite din baya cin batirin wayar idan aka hada da shi babban Manhajar ta Facebook.
GINI MAI SAUKIN SARRAFAWA

Tun daga kwankwalatin (icon) da ginin fuskar manhajar (User Interface) na su wadannan manhajoji na Facebook guda biyu kana ganin kana sun gamu sun banbanta.
Babban Facebook kwankwalatinsa yana zuwa da laurin shudi, shi kuwa Lite kwankwalatinsa yana zuwa da farin launi, sannan a wurin sunan ana rubuta Lite ne kawai ba wai Facebook Lite ba.

Shi Facebook Lite yana da kananan rubutu da maballai, ita wannan manhajar bata da tsarin motsi na Animation, babu hotuna masu nauyi, ba kuma abubuwan ado da ake samun a manhajar Facebook din ta asali.
SHAN DATAR INTANET

Bayan cewar shi Lite din na taimakawa wurin saukin cin RAM, an kuma gina shi wannan manhajar ta Facebook Lite domin ta iya yin aiki a wurin da babu sinadarin shiga intanet mai karfi kamar 2G.
Dalilin yin saurin shi saboda kamfanin Facebook sun cire dukkan wadansu hotuna da basu da muhimmancin a cikin manhaja, amma sun lura da wadansu kananan wadanda zasu karawa manhajar karfin shiga Intanet.
SAURIN BUDE ABU
Idan ana maganar saurin bude abu Lite baka hada shi da Manhajar Facebook ta asali, domin kamfanin yayi kokarin rage mata duk wani abu da zai sa ta yi nauyin budewa.
Duk da akwai wadansu tsare-tsare da idan kana son ka bude a cikin wannan karamar manhajar Facebook Lite yaka dan dauki lokaci kasancewar babu asalin sinadarin da ke sa wannan abun ya bude da sauri kamar yadda ake samun shi a cikin Manhajar Facebook ta asali.
Haka a wannan karamar Manhaja ta Lite ta rasa tarin sinadarin motsi mai kyau tsakanin bude shafi zuwa wani shafi a cikin manhajar (instant transition) wanda ake samun shi a cikin ita Manhajar ta asali.
WARWARE MANHAJA

Facebook Lite bashi da tarin nan na warware da bayyana sabon abubuwan da suka shigo a cikin wayarka. A babbar manhaja ta Facebook da zarar sabon abu ya shigo ita manhajar da kanta zata warware kanta ta zuko sababbin bayanai.
Amma ita Facebook Lite ba tada wannan tsari dole sai ka taba bata wani maballi da shi zai warware da kuma zuko bayanai sababbi.
MANHAJAR AIKAWA DA SAKO

Ba kamar yadda aka sani ba a shekarun baya da manhajar aikawa da sako (Facebook Messenger) take zuwa tare da Facebook App. Amma yanzu kowane yana zaman kansa ne.
Amma abin jin dadi shi Lite yana zuwa da likakkiyar manhajar aikawa da sako wacce baka bukatar ta musamman domin aikawa da sakonni.
Kodayake shi wannan manhajar ta messenger dake jikin Lite bashi da kayan aiki masu yawa kamar ba zaka iya kira da shi ba, babu stickers, da game. Amma dai yana aikawa da sako kuma zaka iya karbar sako kamar kowa.
AMFANI DA EMOJI

Duk da Facebook Lite yana bada damar amfani da reaction da stickers, abin mamaki shine wannan manhajar bata baka damar amfani da emojis.
TO WANNE ZAN YI AMFANI DA SHI?
Idan kana amfani da waya mai 1GB ko 2GB RAM ko kana garin da ba network mai karfi, to kayi amfani da Facebook Lite.
Amma idan kana amfani da waya mai baban RAM ko kana inda network yake da karfi sosai kayi amfani da babbar Manhaja Facebook.
A in burgewa na karu matuka
SLM.
ina yimaku fatan al’hairi.ALLAH SWA yakara muku kaifin kwarewa aka(Compoter) amin. Abin al’faharinmune ace duk Duniya ana alfari daku.
sannan kuma inayi maku fatan gamawa da duniya lafiya amin. Daga Muh’d Bashir kabir Gusau