24.4 C
Nigeria
Friday, April 25, 2025

SHAFIN SADA ZUMUNTA NA FACEBOOK

Sunan Facebook ba boyayye bane ga matasan wannan zamani maza da mata, musamman masu mu’amala da fasahar ziyarar yanar gizo. Domin kuwa koda mutum baya amfani da shafin ba zai kasa jin masu mu’amala da shi suna zancensa ba.

Duk da dai ba duk aka taru aka zama daya ba wato dai ba za’a rasa ‘yan tsirarun mutanen da basu san wannan shafi na Facebook ba, ko kuma idan sun san shi basu san wace irin mu’amala ake dashi ba, kai wasu ma suna amfani da shafin amma basu fahimce shi ba, domin kuwa idan zaka tambaye su menene amfanin Facebook, ka basu aiki ba karami ba. To idan kana daya daga cikin wanda basu san menene Facebook ba ko kuma kana daya daga cikin wadanda sun sanshi amma basu san amfaninsa ba, kai har ma da wadanda suka san shafin kuma suka san amfaninsa ku dan bani hankalinku na dan lokaci dan sanin menene Facebook, wa ya kirkire shi, don me aka kirkire shi, menene amfaninsa da sauran batutuwa makamantan hakan.

Facebook dai dandali ne na sada zumunta kuma yana daya daga cikin miliyoyin shafukan dake kunshe a rumbun yanar gizo wato Internet. Wato kamar irinsu shafukan Twitter, MySpace, Google+ da sauransu, sai dai shafin na Facebook ya banbanta da shafukan dana bayyana a sama ta hanyoyi da dama. Facebook shafi ne da wani dalibi mai suna Mark Zuckerberg ya kirkire shi tare da wasu abokan karatunsa su uku Eduardo Saverin, Dustin Moskovitz da kuma Chris Hughes. A ranar 4 February 2004. A makarantar Harvard a jihar Califonia dake kasar Amurka. Wadannan dalibai sun kirkiri shafin ne don amfani dashi a makarantarsu kawai, don haka cikin dan lokaci kankani shafin ya baibaye ilahirin wannan makaranta, saboda irin farin jinin da shafin ya samu a wurin daliban makarantar Harvard ba’a dau lokaci mai tsawo ba shafi ya tarwatsu zuwa sassan manyan makarantun kasar Amurka baki daya.

Kafin kace me tuni shafin ya tsallaka zuwa kasashen Canada da England, wajen shekarar 2005 shafin ya karade gaba dayan yankin kasashen turawa da yankin Amurka ta kudu. A ranar 26 ga watan 9 na shekarar 2006 kamfanin Facebook ya bayyana cewar kowa zai iya mallakar shafin a duk inda yake a duniya indai ya haura shekaru 13 da haihuwa.

Shafin Facebook shafi ne da kowa zai iya amfani dashi cikin sassakar hanya, shafi ne da masu amfani dashi ke samun damar haduwa da mutane kala kala daga kasashen duniya daban – daban, shafin yana da kayatarwa, nishadantarwa, ilimintarwa, shagaltarwa har ma da wa’azantarwa. Shafi ne daya hada al’ummatai kala – kala mabanbanta ra’ayi, kabila, addini, yare da kuma tarbiya. Haka yasa duk irin manufar da tasa mutum amfani da shafin yake samun ‘yan uwansa.

Facebook wani dandali ne daya bawa masu amfani dashi dama wurin baja kolen ra’ayinsu, ba tare da tsangwama ko hana ‘yancin magana ba, wannan dalilinsa Facebook ya tserewa dukkan wani shafi na sada zumunta wato social network a turance yawan masu amfani dashi. Kamar yadda kamfanin ya shaida cewar yana da sama da mutum miliyan 750 masu amfani da shafin a kiyashin da akayi a watan bakwai na wannan shekara ta 2011.

YADDA AKE BUDE SHAFIN FACEBOOK

Da farko mutum zai tanadi adireshin email mai amfani ko kuma lambar waya. Sannan sai mutum ya zarce kai tsaye wurin da yake shigar da adireshin gidajen yanar gizo idan zai nemo bayanai (browsing) a na’ura mai kwakwalwarsa (computer) ko kuma wayarsa ta hannu (handset). Sai ya shigar da adireshin shafin na Facebook kamar haka http://www.facebook.com idan kuma a wayar hannu ne sai ya shigar kamar haka http://m.facebook.com da zarar ka shiga zaka ci karo da inda aka rubutu SIGNUP sai a latsa nan daga nan kuma za’a aiko ma da form da zaka cike don zama daya daga cikin miliyoyin dake amfani da shafi.

Bayan an kammala ciki form din gami da shigarwa, anan za’a bukaci ka batar da email ko lambar wayar da kayi amfani dasu naka ne, wato kamfanin na Facebook zai turo sako ta cikin abinda ka zaba wurin budewar email ko lambar waya, hade da adireshin da zaka latsa ko lambobin sirri da zaka shigar don kammala rijistar Facebook din naka, da zarar ka shigar ko ka latsa adireshin da aka turo ma shi kenan ka zama daya daga cikin masu amfani da dandalin sada zumunta na Facebook.

Bayan nan kuma sai ka shiga shafin naka don sa hotonka gami da karasa cike ‘yan bayanai da suka dangance ka misali kamar: sunan garinku, addininka, abinda kafi sha’awa, yaren da kake ji, makarantar da kayi ko kake yi ko kuma wurin da kake aiki da sauran bayanai da suka shafe ka, domin saukakawa masu son mu’amula da kai ba dole sai suna tambayarka ba.

Ana zamu tsaya, sai kuma Allah ya kaimu wata na gaba, inda zamu dauko wani shafi kamar wannan dan warwarewa al’umma abubuwan daya kunsa.

Bashir Ahmad
Bashirgy@yahoo.com
08032493020

18 COMMENTS

  1. Lallai wannan fasaha da aka fede ta har bindi abin ya yi kyau, zai kara sani ga wanda bai da sanin, da fatan za’a yi amfani da abin da aka samu ta hanyar da ta dace, ba hanyar da bai dace ba.

  2. Salamu alaikum a gaskiya wannan bayanin ya gamsar yadda ba a tsammani kwarai da gaske.A Gakiya kuna kokari…facebook ta yi fice.Wannan hanya da kuka bi wajen zakulo bayanin nana yana da kyau ainun.An karu matuka gaya.

  3. Inna godiya da wannan shafin na ku>ko kuma in ce namu inna tayaku fatan Alkairi Allah yakara baku kaifin basira da kuke taimako bahaushe bissalam Naku Isa mg kano

    • Ina mika gai suwa ta musamman ga ma,abota wannan babban shafi na dandalin sada zumnta . Agakiya abun yai mani dadi kwarai da gaske. Ina maku fatan alkairi .Allah yai mana jagoranci amin summa amin

  4. Ya ALLAH kataimakawa mai gaskiya a duk inda ya samu kansa. Kwato dunbin kudade daga hannayen manyan azzaluman shugabanninda Buhari yayi niyan yi hakika abin ayabane. Don haka bai kamata anuna sani ko saboba ga dukkan marasa tausayin kasa da al’ummarta ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img