Bayan sakin mukalar mu wacce take bayani game da YADDA ATM YAKE YIN AIKI mutane da dama ta hanyar WhatsApp sun tambaye mu game da irin katin cire kudi da suke ganin bankuna suna bayarwa wani ana rubuta Verve ko Visa ko MasterCard a jikinsu, shin mene ne banbanci ko kuma dai dukkansu abu daya ne?
Wannan matsalar ma sai kaje banki kana son karbar shi wannan katin cire kudi sai ka rasa wannen ne zaka karba, sannan kuma me yasa wani lokaci banki basa ba mutum zabi sai kawai kaga sun sabunta maka da katin da ba shi ka saba mu’amala da a baya ba?
Da farko dai ya kamata mu fahimci cewar dukkan wadannan katunan guda uku da muke ganinsu a hannun mutanen Najeriya kati ne da zai baka damar ka yi siyayya ba tare da kana da kudi a aljihunka ba. Matukar kana da kudi a cikin asusun ajiyar kudin ka dake bankinka, kuma baka fitar da adadin kudin da aka baka damar kashewa kowace rana ba to zaka iya siyayyarka.
A wannan dan darasi da zamu baku, zai taimaka muku wurin sanin wanne kati na ke bukata sannan kuma mene ne amfaninsa da rashin amfaninsa da kuma banbance-banbance dake a tsakaninsu.
KATIN BANKI IRI BIYU NE
Abu na farko da yaka mata mu sani shine bankuna suna iya baka dayan kati biyu, ko kuma suma baka dukkan biyu domin aikinsu ya bambanta.
- Katin Kudi – Debit Card
- Katin Bashi – Credit Card
Katin Kudi – Debit Card

Idan mutum yana da kudi a jiye a asusun bankinsa kuma yaga wani kaya da yake son ya siya a shago ko kanti ko a wani shafi dake intanet to ko bashi da kudi a cikin aljihunsa matukar yana rike da wannan katin zai iya yin siyayyarsa amma kuma da sharadin yana da irin wannan kudi a ajiye a bankinsa, idan ya saka bayanan da banki suka bashi a cikin na’urar POS ko kuma a shafukan Intanet nan take za a cire kudinsa.
Katin Bashi – Credit Card

Sabani da Debit Card, shi Credit Card bankin ka ne zasu baka domin ka iya yin siyayya a shaguna ko shafukan intanet koda baka da ko sisi a cikin asusun bankin ka wanda daga baya idan ka samu sai ka biya. Wato sunan bashin da aka alakanta masa yayi daidai da aikinsa.
Saboda haka, kowane banki suna iya baka Credit Card ko Debit Card ya danganci da irin huldar da zaka yi da su banki, amma kuma kaso 90 cikin 100 na masu amfani da katin suna amfani da Debit Card ne.
BANBANCI TSAKANIN VERVE DA VISA DA MASTERCARD
Kamar yadda muka fada a farkon wannan rubutu cewar mutane suna rudewa idan suka je bankuna suna son su yi katin cire kudi saboda bankunan mu suna bamu zabi cikin kati uku da ake da shi. To, ga banbance – banbancen da ke a tsakanin su.
1. Verve Card

Shi wannan katin dan gida ne, wato an yishi ne domin ‘yan Najeriya kawai sannan ana amfani da shi a Najeriyar ce kawai. Idan banki suka kaba to zaka iya yin amfani da shi ne kawai a kasuwanni Najeriya da dukkan ATM din Najeriya. Za kuma ka iya amfani da shi a POS da kuma dukkan bankunan da kana nan cibiyoyinsu da suke amfani da mahadar Interdwitch.
Haka da wannan kati na Verve zaka iya biyan kudin wuta na PHCN, zaka iya siyan katin waya, zaka iya aikawa da mutum kudi zuwa asusunsa, za kuma ka iya siyayya a dukkan shafukan da ake siye da siyarwa a Najeriya, kamar su FATAUCI, da Jumia da makamantansu.
2. Visa Card

Wannan kati ne da ake karbar sa ko’ina a duniya. Wanda yake da wannan kati zai iya siyayya da shi a dukkan kasuwanni da suke duniya ba tare da wata matsala ba. Akwai shafukan dillanci da suka yi fice a duniya kamar su Amazon da Ebay da Aliexpress dukkansu zaka iya cinikayya da amfani da wannan katin.
Sannan kuma duk abin da katin Verve yake iya yi a cikin gida shima wannan katin na Visa yana yi shima. Shi wannan kati na Visa an samo shine daga BankAmericard daga Fresno dake California ta kasar Amurka a shekarar 1958 wanda daga bisani aka canza masa suna zuwa VISA a shekarar 1976.
3. MasterCard

Shima wannan katin kamar Visa ne ana amfani da shi a kowace kasa a duniya kuma duk abinda Visa yake yi a waje shima yana yi, sannan kuma yana aiki irin aikin da Verve yake yi a cikin gida.
Shi wannan MasterCard an kirkiroshi ne a shekarar 1966 ya fito da sunan Master Charge, daga baya ya koma Interbank Card, a shekarar 1979 aka canza masa suna ya koma MasterCard. Shima kati ne na bankin kasar Amurka dake New York a hedikwatarsa dake O’Fallon, Missour. Hukumomin lura da kudade sama da budu 25 ne suka mallake shi.
Daga cikin banbancin amfanin su, shine idan mutum yana rike da MasterCard ko Visa Card sai yayi tafiya wata kasa, to bashi da matsala matukar akwai kudi a asusun bankin sa da zarar yaga ATM zai iya fitar da kudin wannan kasar ba tare da yaje yayi canji ba.
KAMANCECENIYA A TSAKANIN SU
- Dukkkansu suna zuwa da wani maganadisu a jikinsu wanda yake bukatar a kiyaye sosai wurin ajiyarsa. A kiyaye saka katin wurin ruwa da maiko da kuma saka shi a aljihun baya ga samari domin zama a kansa kan rage masa dadewa wurin amfani.
- Dukkansu suna zuwa da wadansu lambobi guda goma sha shida, da lokacin da zai dena amfani da wasu lambobi guda uku a bayansa na CVV.
- Wani lokaci katin yakan zo da sunan mutum a rubuce wani lokaci kuma baya zuwa da suna.
BANBANCI TSAKANIN NAIRA CARD DA DOLLAR CARD
Akwai wani kuma banbanci da ake samu na irin kudin da mutum zai iya fitarwa, kowane banki zasu iya baka katin cinikakka iri biyu, ko na Naira ko na Dalar Amurka.
Naira Card
Kati ne da ake amfani da tsabar kudi na najeriya, wanda shi yana amfani da Savings ko Current Account din mutum ne da yake zuba kudi ko ajiya. Wato duk kudin da zaka saka a cikin wannan asusun kudin Najeriya zaka zuba, saboda haka idan aka baka kati da yake da alaka da wannan asusun naka to ana kiran wannan katin Naira Card domin asalin kudin da ake ajiye mishi Naira ce.
Duk da zaka iya yin siyayyar dukkan wani abu da ka gani a Intanet kuma a fitar da kudin da canjin irin wannan kudin da kayi siyayya, sannan zaka iya amfani da shi a ATM na wata kasa ka cire kudin wannan kasar.
Dollar Card
Shi wannan asusu ne na musamman ake budewa a banki da yake da alaka da bankinka da kuma wani banki dake kasar Amurka domin ajiyar kudin kasar Amurka na Dala, wanda a Turance suke kiranshi da Domiciliary Account.
Shi wannan account din ba a zuba mishi Naira sai Dalar Amurka kawai, kuma ba zaka je ATM ka zura shi ba ya baka kudin kasarku sai dai idan ATM din yana bayar da Dalar Amurka ne.
Zaka yi dukkan wani cinikayya a Internet a manyan shafukan dillaci na duniya, amma kuma ba zaka yi amfani da shi a kananan shafukan da basu da Dociliary Account ba.
Mutane da dama suna bude wannan asusun Dollar ne saboda ana cinikayya da dalar Amurka kusan a kowace kasa a duniya, amma idan kana son bude asusun ajiyar kudi na Pound Sterling ko Euro duk zaka iya mutukar bankin da kake suna da babban bankin a irin kasashen.
Ina fatan kun tsinci abu koda daya ne a cikin wannan mukalar kuma ya amsa wasu daga cikin tambayoyi ko abubuwan da suka shige musu duhu.
salam alaikum magana tagaskiya inason inyimuku fatan alheri ama bansamu damaba sai yau munagodiya
Jazakallahu bi kairan
Dan ALLAH yaya zanyi in cire kudina daga PayPal zuwa account nawa na banki, gamma dalar ce acikin PayPal din
ka turo min ta gmail Dan ALLA.
Allah ya Kara ilimi
Masha Allah Allah ya qara Basira da daukaka
Muna Godiya Wbmstr Nakasance Tunda Dadewa Ina Bibiyar Shafinku Yanzun Inasan Dan Allah Kaban Numbrn Ka Ngd