32.4 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

Yadda ake gane Facebook account da aka yi hacking da yadda ake magance shi

Ba abin mamaki bane ka bude shafinka na facebook ka wayi gari ka ga wani mara mutunci ya kwace ragamar tafiyar da shafin naka. Hakan fa na faruwa cutarwar da kuma zayi zai iya shafarka ko abokanan huldarka ko kuma ‘yan uwanka da suke amfani da intanet bama facebook ba.

Inda tsoron yake, wani lokaci zaka samu wani yana amfani da shi wannan account din naka amma kuma kai ba ka ma sani ba. Wani lokaci kuma sai mutum ya tashi budewa sai kawai yaji ance an canza masa passoword ko kuma yaga sunansa ya canza daga nashi zuwa na wani.

Madalla da wadansu hanyoyi da mutum zai iya bi ya gane cewa wani yana amfani da shafinsa kuma da hanyar da zai iya bi domin ya dakatar da wannan mutumi amfani da shafinsa.

Yadda zaka gane idan anyi hacking account dinka.

Wani lokaci ana iya fahimtar anyi hacking accout din mutum ne ta hanyar ganin tallace-tallace na shiga shafukan abokan ka a facebook da sunan kaine kake yi musu wannan tallan, wanda a ciki kana basu shawara ko ma tursasawa da su sayi wannan abin da kake yin tallansu.

Account din facebook da aka yi hacking wani lokaci yakan yi amfani da email address din da suke cikin facebook dinka ya rika aikawa da wadansu sakwanni da baka sani ba.

Wani lokaci idan kaga an canza maka suna ko wani bayani a profile dinka ko imel dinka ko password to lallai wannan account na facebook ba naka bane wani ke da iko da shi.

Hanyar da zaka gane cewar wani yana amfani da facebook account dinka shine ta hanyar shiga security setting na facebook dinka

Ka shiga settings>security>where you’re Logged in sannan ka taba Edit zai fito maka da hoton bayanin na’urorin da suke amfani da facebook dinka. Idan kaga bakuwar waya to sai kayi blocking dinta.

12 COMMENTS

  1. Masha Allah

    Tambaya:

    Idan ya kasance mutum yana da shafi a Fb kuma yana da mabiya akala kamar ace 10k amma kuma kullum sai raguwa suke yi har sun dawo 9.5k

    Kuma page ne ba Group ba.

    Sannan mutum yana yin Posted bai daina yi ba, Dan Allah, Malam ko akwai hanyar da zai bi ha gyara

  2. dan uwane yarasu kuma yabar kudi abanki kuma.munje banki basu yarda damuba akan sufada mana yadda zamu san pin dinsa bamusan komai akan bayanan account dinsa ba, dan allah kutaimaka min yadda ake samun pin din ATM

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img