38.1 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

Abubuwan la’akari wajen sayan sabuwar laptop

Salam. Wai shin, menene abubuwan la’akari in inason in sayi sabuwar laptop kuma wani brand yafi inganci? Not advert..lol.02 August 2011 at 16:36 Mustapha Adamu

Duniyar Computer Malam Mustapha Adam, akwai abu na farko da ake la’akari da shi a lokacin da mutum zai sayi kayan wuta ba ma dole sai computer ba, shine suna da inganci? idan aka zo ga maganar computer laptop kusan gaskiya campanoni da dama a wannan lokaci  suna matukar kokari wajen ganin sun wuce tsara, amma idan maganar wace irin laptop zaka ka siya saboda ingancinta to ya danganta da aljihunka domin kare da kudin shi ai zai sha lahaula. Idan kuwa ka zo siya ka duba mene ne girman processor dinsu, kuma mene ne girman RAM din su, mene ne kuma karfin batirin ta awa nawa take yi, domin a wannan lokacin karanci ka samu sabuwar laptop tana yin awa hudu da rabi cikakke kafin ta dauke, daga baya sai ka duba girman HARD DISK dinta, sannan kuma ka duba girman ta domin wata ta fiye kankanta wata kuma tafi girman da yawa ka duba matsakaiciya wacce ba zata baka wahala wajen dauka ba. sannan bayan ka biya ka lura da yi mata charging kafin fara amfani da ita domin rashin yi mata charging da farko yakan lalata batir, sannan kuma kada ka rinka saka mata program da ba zaka yi amfani da suba kuma ka guji saka games da video da baka san daka inda ta suke ba. Kuma tunda ka yi kokari ka saya laptop da kudi mai yawa to ka daure ka siya sabon antivirus daga company kaspersky ko kuma norton domin duniya anyi ittifaki babu wanda ya fisu defination na virus. A sha ruwa lafiya Allah ya karbi Azumin mu. 03 August at 14:36

6 COMMENTS

  1. Asl. Agaskiya wannan abubuwa da kukeyi domin bayin Allah yana matukar kayatarwa ga wanda yake da alakada fannoni da dama, Allah ya muku sakayya da gidan Aljannah, ya karawa karatun ku albarka duniya da lahira. Mukuma masu karantawa muna karuwa Allah yasa muma muyi aikidashi tahanya maikyau. Allah ya saka da alkairi. Wassalam.

    Sadiq Gombe.

  2. Ubangiji ya yi sakayya da alkhairi.ya rubanya mana irinku a cikin al’ummar hausawa.
    Tambaya,shin menene ke sa a yiwa waya flashing?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img