30.9 C
Nigeria
Wednesday, April 30, 2025

System Software da Operating System da kuma Utility Program – MENE NE BANBANCI TSAKANINSU?

System Software

Idan aka ce System Software ya kunshi dukkanin program da suke sarrafa ita computer da kuma Hardware nata, sannan shine ke zama mai fashin baki tsakanin mai amfani da computer da kuma Hardware, wanda shi mutum ba zai iya sanin abinda ita na’ura ke nufi ba idan babu System Software, haka ita ma na’ura ba zata iya fahimtar abinda mutum yake umartarta ba na aiki da hardware din ta sai idan ya kasance akwai System Software.
System Software shima ya kasu kashi biyu, akwai Operating System akwai kuma UtilityProgram, wadannan guda biyu sune suka hadu suka yi System software wanda kasancewar daya babu daya ba zai yuwu ka kira su da System Software.

Mene Operating System?

Shi Operating System shine ke jagorantar dukkanin Hardware da aka hada da na’ura. Haka Operating System shi ke baka damar yin amfani da Application da ka saka acikin ita computer. Yadda abin yake, shi Operation System shi dunkullen software ne, wanda yake za ma kamar rai ga ita computer wanda shike da alhakin sarrafa hardware da kuma Application software da aka ajiye a cikin na’ura, idan aka ce Operating System na na’ura ya lalace, to ana daukar kusan dukkan program da suke cikin suma sun lalace domin abinda ke sarrafasu ya daina aiki, kuma babu yadda za ayi ka iya ajiye kowanne irin program a cikin computer kuma kace yayi aiki mutukar babu Operating System a ciki.
Microsoft Windows na daya daga cikin irin wadannan Operating System wadanda sunan su ya shahara a duniya sabo da yawan amfani da shi da ake yi.
Yadda kuwa shi operating system yake aiki, idan ka kunna wutar na’urraka sai shi operating system ya fito daga hard disk zuwa memory na computer, zai zauna cikin shi wannan memory mutukar na’urar tana kunne domin ta baka damar yin ayyuka ko kuma sarrafa sauran abubuwan da suke cikin ita computer da kuma dukkanin software da ke cikin ta.

Mene ne Utility Program?

Wato idan aka ce Utility Program su wasu program ne wanda suke yin aiki na musamma da ya shafi sarrafa hardware ko kuma program dake cikin ita computer. Wato su ba kamar Operating system bane domin su kanan program ne da aka yin su domin su lura da wani bangare na operating system da yadda yake umartar hardware suyi aiki da kuma yadda yake tafiyar da aiki sa. Shi yasa a kowanne lokaci ake danganta Utility Program da ‘ya’yan Operating System saboda su suke wakiltarshi a wajen tafiyar da ayyukan shi. Irin wadannan Utility Program kamar misalin program da yake da alhakin lura da lafiyar ita kanta computer da bubuwan da suke cikin ta. Ba aikin shi ba ne ya san wane hardware ko software aka sa ba. Amma alhakin shine ya san idan wani bakon program zai shigo cikin wannan computer ya tabbatar da cewar lallai program ne, ba virus bane.
Haka daga cikin irin wadannan utility software akwai wanda aikin shi shine taimakawa operating system lura da umarni da ake ba computer wajen gabatar da wani aiki tare da wani Hardware. Kamar wanda yake lura da aikin da printer take yi, a lokacin da ka gama rubutu a cikin computer kana son ka fitar da shi a takarda, to daya daga cikin aikin da shi wannan utility yake yi shine ya tambaye ka, kowanne shafi nawa kake son a gurza maka, sannan kuma dukkanin shafukan da kayi rubutu kake son a gurza, ko kuma wasu bangere kawai kake son a gurza. Saboda haka, idan ka rubuta amsoshin wannan tambayoyin shi wannan utility shike da alhakin sanar da shi operating system cewar ana son ayi amfani da printer kaza, shafi na daya zuwa na biyar a kuma buga su sau biyar-biyar. Idan ya gama gaya mata shi ya gama aikin shi ke ann. Sai shi operating system yayi magana da ita printer idan ita kuma printer ta fara gurzawa ba za ta tsaya ba sai ta gama abinda aka umarceta. Da ace a daidai wannan lokaci takarda zata kare kuma ba ta gama ba za ta sake aiko da wani yaron ta ya gaya maka babu takarda a cikin printer.
Irin wadannan utility program suna zuwa tare da Operating system sannan kuma zaka iya siyan wasu irin su na daban da aka inganta ayyukansu da yan kudi kalilan.
Ko da yake su utility program suma kamar yadda muka fadi cewar program ne, suma suna amfani da fuskoki da aka tsaramusu domin suyi aiki. Duk da cewar ko wani program da irin fuskar da yake gabatar da kanshi ga mai amfani da shi wannan fuska ita ce ake ce mata

USER INTERFACE

Saboda haka shi Operating System dauka za ka yi cewar shine wani babban tsari da yake sarrafa ita computer, ba domin operating system ba to idan ka kunna computer ka babu abinda za ka gani a jikin monitor illa baki kamar ba a kunna ta ba. Sannan kuma shi Operating System na da ‘ya’ya masu lura da shi, kamar yadda muka yi bayni a baya, wadanda su suke taimakawa shi Operating System wajen tafiyar da ayyukan shi. Amma daga karshe akwai wadansu Operating System wadanda ba kamfanin Microsoft suka yi ba, akwai wanda ake kira da Mac OS wanda kamfanin Macintosh suke yi, duk da yake a wannan kasa ta mu ta Najeriya ba kowa ne ya san da labarin wannan Operating System na Mac ba, duk da cewar shi wannan operating system na Mac OS virus baya shiga cikin shi, idan ka daura shi a jikin computer ka to ba ruwanka da Anti-Virus. Haka kuma akwai OS wanda kamfanin Linux suke yi wanda shima kamar Mac OS yake babu ruwanshi da matsalar Virus, sannan kuma gashi shi kyauta yake ba a sayar da shi.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img