Hausawa kan ce ana za ton wuta a makera sai a same ta a masaka, wannan magana ta yi daidai da yadda akan yi zaton cewa wasu shafukan internet na kumshe ne da tarin illoli da cututtukan da ka iya lalata ta wasu kuma basu da shi amma abin ba haka yake ba
Hakika akwai wasu kebantattun shafukan Internet da suka fi ko’ina hatsarin shiga sabo da irin abubuwan da ake boyewa a cikin su, wadanda idan mutum ya ziyarci irin wadannan cututtuka zai iya sanyawa na’urarshi cututtukan da zasu iya lalata na’urar da kuma hanyayoyin da za su kiyaye ko su tsare a lokacin da suka fada cikin irin wadannan shafuka.
Mun kasa wadannan shafuka kusan gida biyar (5) wanda za mu sanya alama wacce idan muka sa kafin muyi bayanin wannan wuri yake nuna cewar illa ko rashin illar shiga wannan shafi. Zai iya yuwuwa bayanai da zamu fadi a wannan Mujallar Duniyar Computer ya zamanto an sami canji sakamakon irin ci gaba da ake yi da kuma gyare gyaren da wasu shafuka ko kuma gidajen internet suke yi a lokacin da suka fahimci cewar akwai matsaloli tare da shafukan su. Da fatar za a karanta da idon ba sira kuma a kiyaye, domin manufarmu shine a zama babu wata matsala a computer mu.
irin hotuna da zaka iya gani na ‘yan matan turawa ko na motoci ko na mawaka na iya zama ba hotu bane da aka sasu domin kallo kawai, za su iya yuwuwa akwai cutarwa da ke nade a jikinsu. Haka nan mafi yawan amsoshin da mutum kan bincika a shafi na google na iya zama amsa ga mai bincike, zai kuma iya yuwa su zama ciwon kai ga computer ka. Jin dadin kallon wasu video da kake yi a internet ko kuma sauko da su (Downloading) jin dadin da annashuwar na iya komawa bacin rai da damuwa a na’urarka.
Na san sau tari mutum yana jin ana gaya mishi hatsarin da ke cikin shafukan internet, wannan haka yake, wasu shafukan suna da hatsari, wadansu kuma za ka shiga ciki kayi wadakarka, babu abinda zai same ka. Zaka iya daukan ko wane irin mataki domin ka tsare na’urarka, zai yi wahala ya zama kai mai son shiga kowane irin shafi a internet a ce baka kwaso ko da malware ba, ko kuma a kwace ragamar tafiyar da akwatin e mail din ka, a rinka turo maka da sakonni na banza da wofi, ko kuma a kwace maka sirrin da kake ajiye wa a na’urarka, ya zama bayanan ka, bayanan katin kudin ka, da dai wadansu bayanai wanda baka son kowa ya sani. Irin wadannan dalilai sune suke sa mutum ya dauki matakin neman tsare kanshi daga fadawa hannun ‘yan baranda wadanda burinsu shine su ga sun lalata ko sun kwace ragamar na’urarka ta hanyar virus da malware da dai sauransu. Kuma yana da kyau mutum yasan irin cutar da zai iya samu a lokacin da ya shiga wani shafi, da kuma abinda zai yi domin ya samu tsari kada wani abu a cutar da shi.
Cutar shafukan da ake samu a internet ba iri daya ba ne, godiya ga Allah, Mujallar Duniyar Computer ta yi kokarin bincike kuma ta karkasa su irin wadannan shafuka har gida biyar kamar yadda na fara bayani a farko.
Saboda haka matakin farko shine kada ka shiga shafin da baka amince da shi ba, domin yin haka zai iya kawo maka matsala. Ka yi amfani da bayanan da zamu yi maka a matsayin hanyar shiriya.
Cuta ta 1:
Flash files da ake zargin suna hade da abinda zai lalata na’urarka.
Inda ake samunsu: Mafi yawancin shafukan da suke amfani da Flash
: Abobe sune kamfanin da suke yin wannan program na yin Flash wanda wadansu suke yin amfani da shi su daura wadansu umarni (Codes) na malware da idan mutum ya ziyarci shafin da suke na’urarshi ta kamu da cuta. Wani karin cutarwa dangane da su flash website shine wadanda suke kirkiran shafukan kuma su goya musu wadannan malware suna amfani da shi flash din ne sabo da shi flash ana rubuta wani tsari da zai tafiyar da shi, sai su yi amfani da wannan damar su daura musu umarnin da idan ya shigo na’urar ka zai basu wata kafa da zasu yi maka barna. Wani abin haushi sukan yi amfani da tsarin irin na Cookies, shi kuwa Cookies ya tunatar da browser (program da ake yin amfani da shi wajen bude shafukan internet) shafukan da mutum ya ziyarta da ita, sannan kuma koda ka share Cookies din browser ka, to na flash baya fita, yakan bar baya da kura
Ina son mutane kada hankalinsu ya tashi suce ke nan duk wani shafi da muka gani da flash ya na da malware ko virus ke nan. Amsar ita ce a a, domin mafi yawan shafukan da zaka shiga na kasannan kusa kadanne wanda basu da flash a kansu, kuma bana tsammanin akwai wani wanda yake iya yin wannan program da zai cutar a wannan lokaci.
Matakin da zaka dauka idan ka ziyarci wannan shafi
Domin ka tsare kanka daga farmaki irin na flash program, ya kamata ko da wani lokaci ka rinka amfani da gyararran plug-in na flash kuma ya kasance shi plug-in din yana tafiya tare zamani. (Plug-in shine wasu canje-canje da kamfanonin da suke yin software su ke yi a kai a kai domin cire wasu matsaloli da mutane suke fuskanta tare da program din su). Sannan zaka iya shirya tsarin yadda kake son idan flash ya sauko daga internet ya zai yi yayi aiki a cikin na’urarka.
Cuta ta 2:
Kutsattsarin Links wadanda zasu iya kai ka ga shafukan da zasu iya cutarwa
Inda ake samunsu: Twitter

: Macuta a harkar yadda kwayoyin cutar da na’ura (Scammers) lallai suna son Twitter sabo da shi shafin dandali da raja’ane ga kananan Link, sannan kuma a Twitter mutum zai iya rage tsawon Link zuwa dan gajere. Da wannan dalili ne, Scammers suke amfani da dandalin Twitter domin boye Link da yake kai mutum zuwa mugun shafi wanda ziyarar shafin na da hatsari.
Abu ne mai sauki mutum ya boye malware ko kuma cuta a irin wadannan gajerun links. Kuma kusan dukkan irin wadannan gajerun link a karshe suna kai mutum zuwa ga shafin da zaka sami (Trojan horse). Yadda abin yake ka kalli saman browser ka zaka ga inda aka rubuta misali kamar haka (http://www.duniyarcomputer.com), a in da ka ga wannan shi ake kira address to zai iya yuwuwa a cikin shafin internet ka ga an rubuta cewar idan kayi clicking nan misali salisu za ka shiga shafin cin gasa, wato duk inda ka ga rubutu a shafin internet a cikin shafin kuma da layi a kasan shi, shi a ke kira link, to yadda su macutan suke yi maimakon idan kaga wannan link idan ka kai dan yatsan mouse zai iya nuna maka wurin da zaka shiga, to tsarin da Twitter suka yi shine maimakon ka ga misali http://www.duniyarcomputer.com sai kawai kaga http://~QseHH kawai.
Matakin da zaka dauka idan ka ziyarci wannan shafi
Abu mafi sauki shine idan kaga wannan link din kada ga latsa shi. Na san kuwa abin zai baka dariya domin an hanaka yawo a twitter kenan? Wata hanyar da zaka bi kuma itace kayi amfani da kananan application da ake attaching din su da Twitter wanda su suna taimakawa wajen biyyana asali sannan cikakkiyar hanyar da wannan link zai kai ka. Amma shawara mafi inganci idan har ba ka san waye ya aiko maka da link ba, kuma baka san inda wannan link zai kai ka ba, abu mafi dacewa shine ka rabu da shi.
Cuta ta 3:
Sakon email da ga macuta ko kuma attachment da zai kai ga inda za’a kwashe maka mahimman bayanai ko kuma ka dibo Virus
Inda ake samunsu: Akwatin Email din ka

: dangane da abinda ya shafi emil da yadda ake amfani da shi wajen aiko da sakonnin na banza, wadanda su wadannan sakonni manufar turosu shine idan ka bude su, sai su aiko maka da kwayoyin cutar da computer. Ko da yake kamfanonin da suke harkar bayar da Email ko kuma ake amfani da su suna kokari matuka wajen warware sakonnin da suka yi kama da na cutarwa. Mafi yawan sako da ake turowa daga wasu kamfanoni wanda suka kumshi talla da sayar da haja, su scammers suna amfani da adireshi ko kuma sunan wani kaya sannan sai su goya wannan Virus ko kuma Malware a jikin shi sakon, yadda idan kaga, a misali “Saura kwana uku mu rufe bayar da Visa ta Amurka kyauta” da kaga irin wadannan talla sannan daman kai mai bukatar Visa ne sai kawai ka bude wannan sako, ka danna wannan sako ke da wuya sai kawai abinda suke so ya faru a na’urarka sai kawai ya faru.
Matakin da zaka dauka idan ka ziyarci wannan shafi
Kada ka yarda da ko wani irin sakon da baka san waye ya aiko maka ba, ko kuma ba kayi magana da su zasu aiko maka ba. Idan har kaga irin wannan sako kuma kana bukatar ka fahimci ina aka sa gaba, to, sai ka ki latsa wannan Link, ka shiga website da ka ji cewar suke da alhakin wannan sako idan sakon sabo da kai ne, to, kaga babu matsala.
Cuta ta 4:
Malware da ake boye su a jikin Video ko Music ko kuma Software wajen Downloading
Inda ake samunsu: Shafukan Torrent
: Shafukan Torrent da gidajensu na Internet basu da doka wajen tafiyar da sana’arsu, tun da daman kusan dukkan kayan da ke cikin irin wadannan gidaje na sata ne, kuma babu wata doka ko order a lokacin da wanda ya dibo kayan wasu yana son ya ba wasu kyauta akan cewar dole wannan kayan su zama masu tsabta. Wannan dalili yasa scammers suka fi amfani da gidaje irin na Torrent wajen yada Virus da Malware.
Ben Edelman wanda yake sashin bincike sannan kuma Farfesa ne a Harvard Business School yace “Ina ganin babu wani shafi a Internet wanda ya fi ko ina hatsarin shiga irin gidajen Torrent, domin su basu da doka akan abinda ake zuba musu, domin ba a sayar da kaya a ciki. Shi yasa nake ganin shafukan da suke nuna tsiraici zasu fi shafukan Torrent tsabta, idan ka dangantasu da cewar ana biyan su kudi domin amfani da kayansu”. In ji Ben Edelman.
Matakin da zaka dauka idan ka ziyarci wannan shafi
Hanya mafi dacewa ita ce, kada ka shiga wannan shafi, sannan kuma ka guji irin wadannan kayayyakin da basu da garanti wajen amincin wadanda suka bayar da su. Amma idan har ka dage akan cewar dole sai ka shiga, to, kayi amfani da wata na’urar da ka san babu mahimman bayanan ka a cikin ta. Kuma ya kasance idan zaka saukar da kaya daga irin wadannan shafuka ka rinka kokarin karanta jawaban da mutane suke yi a kasan shafin, idan kayan da kake son kayi downloading akwai matsala zaka ji idan akwai wani matsala, idan kuma babu matsala zaka ji shima. Idan kuma dai ka nace sai ka dauko shi, kuma babu wanda yayi bayanin lafiyarshi? To, idan ka saukar sai ka jira sai bayan kamar kwana biyu, sai ka bude shi. Amma shima da sharadi ya zamanto kana amfani da Anti-Virus mai lasisi kuma ya zama koda wanne lokaci kana Updating na anti-virus din.
Cuta ta 5:
Malware a cikin Hotuna ko Video wanda akwai tsiraici a cikin shi.
Inda ake samunsu: Amintattun Gidajen nuna tsiraici
: Shafukan da ake nuna majigi na tsiraici suna da matsalar tsaro ba kamar sauran shafuka da ake kallon majigi ba kai tsaye, amma hakan ba yana nuna maka an kai karshen bayanin ba ke nan. “Babu tantama shiga cikin irin wadannan shafukan zubar da mutunci ba yana nuna maka cewar yana da cikakken hatsariba, amma idan sana’arka kenan wata rana zaka tsinci kanka a wajen da zaka sami cuta” in ji Roger Thomson babban mai bincike a ma’aikatar AVG (wanda su suke yin AVG Anti-Virus) ya kara da cewa “Wannan abun bantakaici ne, tunda ko ka tsare kan ka daga shiga irin wadannan shafuka, ba yana tabbatar maka da ka tsaru ba ne. Domin mafi yawan gidajen Internet Scammers sukan yi fasa kaurinsu su saka irin wadannan abubuwa na cutarwa”.
Kamar yadda na fadi a baya, amintattun shafukan nuna tsiraici, yana da matukar wahala su bari a saka Malware a ciki, domin suna son koda wani lokaci abokanen huldansu su ci gaba da hulda da su. Amma yana da wahala ka iya raba tsakanin amintattun shafukan batsa da malware.
Matakin da zaka dauka idan ka ziyarci wannan shafi
Kayi hankali da irin Video da zaka sauko da shi, kuma ka kiyaye dukkan wani Video da zai ce sai ya dauko Codecs sannan ka iya amfani da shi, ko kuma kayi amfani da toolbar irin na Norton ko McAfee da SiteAdvisor da ke Firefox domin idan akwai gidan da zaka shiga akwai matsala su fada maka.
Wani mataki na biyu shine idan har kace zaka shiga wannan shafi, to ka yi amfani da wani computer domin tsaron mutuncin ka da na iyalanka.
Cuta ta 6
Trojan Horses wanda ake wufintar da mutum a matsayin video codecs, daga karshe malware su shiga computer ka.
Inda ake samunsu: Websites da ake saukar da Video, ko kuma a peer-to-peer networks.

: nasan babu tantama idan ka taba kallon video kai tsaye daga internet nasan an taba ce maka ka saukar da wani codecs da zai baka damar ka kalli wannan video. Codes wani dan karamin application ne da yake taimakawa wajen a iya kallon video a internet. Maganar gaskiya sau tari irin wadannan codecs din basu da matsala misali kamar DivX codec. Amma fa ka sani wadansu website din suna saka video a da za a kalla a internet kai tsaye sannan su makala mishi wannan codecs wanda akwai malware a jikin shi da kuma zarar ka saukar da shi ko kuma ka kalleshi sai computer dinka ta samu matsala.
Matakin da za ka dauka idan ka ziyarci wannan shafi
Mataki mai kyau shine ka tabbatar dukkan wani abu da zaka kalla kai tsaye a internet idan yace kana bukatar codecs wajen kallon shi kasan su wane ne masu video din, kamar misalin video’n da ake samu a dandalin YouTube.com da kuma Vimeo idan kaga sun ce kana bukatar codecs zaka iya saukar da su domin su amintattun gidajen ne, haka nan kamar gidajen ka amince da su cewar ba zasu saka tsiya a cikin website dinsu ba, ko kuma site da ka san ka biya kudi ne ka ke kallon abinda suka saka. Amma kuma idan kai ma’abocin kallo ne, ko da wane lokaci kana son kallon wasanni ko kuma labarin ko kuma irin shirye-shiryen wasan kwaikwayo irin daga gidajen Hulu.com ko TV.com ko kuma ABC.com da kuma iTunes.com to suma suna da aminci domin sunfi peer-to-peer network .
Cuta ta 7
Taswira a jikin wayarka wacce take baka damar ganin wurare daga jikin ta.
Inda ake samunsu: a wannan wayarka mai tsada (Smartphones)

: kasuwar wayoyin hannu da ake kira Smartphones har yanzu jaririyace, haka yake ita ma hanyar cutarwar irin wadannan wayoyi shima bai shaharaba, idan ma akwai abin da ya kamata mu saka idano akai shine taswira da take iya nuna mana wurare da muke son gani da kuma bayanai, domin nasan akwai mugayen mutane da suke kan hanyar cutarwa sannan kuma suna nan suna kara wanzuwa. Abu na farko da aka samu shine akwai wani game da ake sakawa a waya mai tsarin Android wanda a karshe aka gane cewar shi wannan game yana matsayin dan leken asiri a wayarka. Haka akwai wani website mai suna pleaserobme.com wanda yake nuna cewar ai wane kaza baya gida wanda haka hatsari ne ga tsaron shi.
Dangane da irin wannan misalan, tabbas akwai application da suke da amfani a cikin smartphone kamar wanda zai iya gaya maka wajen da ka nufa, ko kuma ka sauka a wani gari da baka sanshi ba zai iya fada maka wajen da kake da kamar misalign hotel ko kuma dakin abinci dake kusa da kai. Ko da yake kamfanin Apple masu yin irin su IPhones kwanakin baya suka kara kaimi wajen ganin sun kiyaye mutuncin masu amfani da kayansu, tun daga abinda ya shafi bayanan sirrin su, sunayensu da wurin da yake da dai makamantansu.
Matakin da zaka dauka idan ka ziyarci wannan shafi
Mataki mai kyau shine ka kiyaye da dukkan wani sabon abu da baka sanshi ba, ko kuma ka lura da kyau da irin hotunan da suke bayyana a fuskar smartphone dinka, sannan kuma ya kasance ba ko wane irin application zaka gani ba kamar daga facebook.com ko kumaFourSquare wanda suke nuna maka wurare a yarda da shi ba, sannan kuma ya kasance kana da cikakkiyar masaniyar inda zaka shiga.
Cuta ta 8
Gidajen yin bincike (search engine) wanda suke da guba, wanda a karshe su kai ka zuwa ga website dake da malware.
Inda ake samunsu: Search Engine (Gidajen da ikin su shine kawai bincike)

: Guba da Search Engine suke kai mutum ya samu asali ne daga irin shafun da mugaye suke kirkira su saka saka wani abu da suka san ya shahara ko kuma mutane suna yawan bincike a kanshi, sai su goya shafin malware sannan kuma su saka dukkanin wani tsari da suka san cewa Search Engine website suna nema wajen cika sharadi wanda daga baya idan ka binciki kamar wane kayane yafi kyau ta bangaren kaza, ko kuma wannen babban labara ko kuma a baka kaya goda goma wadanda suka fi daraja sai kawai ka fada tarkon su.
Kamar yadda kamfanin da suke yin Anti-Virus mai suna McAfee suka fada bayan sun gudanar da wani bincike, suka ce kashi 19% na sakamako da mutane suke yin bincike a Search Engine kamar irin su shahararrun ‘yan wasan fim na turai kamar Cameron Diaz ko kuma irin screensaver da mutane suke bincike suna kai mutane ne zuwa ga gidajen website masu malware. Haka kuma suka ce irin su Facebook da labarai da dumi-duminsu suma wurin kai hari ne ga irin wadannan mutane.
Matakin da zaka dauka idan ka ziyarci wannan shafi
Idan har baka san gidan da zaka shiga ban a internet, sannan kuma ka shiga search Engine website kayi bincike, to, ka natsu da kyau ka karanta URL (tsanin da zaka hau yakai ka gidan da kake son shiga) ka tabbatar shine inda kake so ka shiga. Kada kawai ka rufe idanun ka duk abinda ka ga sakamakon shi ya fito maka ka kawai ka latsa URL ka shiga.
Cuta ta 9
Takardu masu PDF da ake iya wawuntar da kai har ya saka maka malware.
Inda ake samunsu: wurare guda biyu (2) akwatin email naka, da kuma website da aka yi hacking dinshi.
: a lokacin da Hackers suka ga kamfanin Microsoft ma kara kaimi wajen ganin sun rage yawan malware da virus da ake jifan Windows dashi sai, sai Hackers suka canza sababbin hanyoyi da kuma salo da zasu yi amfani da shi wajen watsa irin wadannan cututtuka a computer. Daya daga cikin matakan da suke dauka suma Hackers din shine ta amfani da takardun PDF, wanda suke iya lullube malware a jikin shi su saka shi. Ana kiran irin wadannan PDF da (poisoned PDF) wato PDF mai guba. Kuma inda suke kutsa irin wadannan file masu guba shine cikin akwatin email dinka kaga sako da baka san waye ya aiko da shi ba da attachment. Ko kuma suyi kokari su kwace ragamar wani gidan internet su watsa irin wadannan takardu.
Matakin da zaka dauka idan ka ziyarci wannan shafi
Babban mataki shine ka tabbatar koda wane lokaci kana amfani da sabon Adobe Reader (kyauta ne ba a sayar da shi), haka kuma zaka iya amfani da wasu Program da suke iya bude PDF wanda ba kamfani Adobe suka yi ba, kamar yin amfani da sabon Foxit Reader. Yin amfani da sabon PDF reader zai kasance ya zaman maka garkuwa akan dukkan wata kafa da Hackers suke iya amfani da ita wajen su cutar maka da computer ka.
Za kuma ka iya hana Adobe Reader taka ta bude dukkanin wani attachment da ban a PDF, ta shiga Preferences sannan ka click Trust Manager sannan ka cire Allow opening of non-PDF file attachments with external application. Illa iyaka. Ko da yake sabon Adobe Reader 10.0 da ake da shi idan shine a jikin computer ka ka sami tsaro.
Cuta ta 10
Mugayen video da ake hadasu da lalatattun abin kallo (player) domin a kwace ragamar computer ka.
Inda ake samunsu: Website da ake saukar da Video

: Gwanayen fasakwaurin gidajen internet suna yin amfani da codecs da video kamar yadda suke yin amfani da shi a cikin PDF idan suka saka surkulensu kai kuma ka shiga kaga video’n ka dauko ka kalla sai na’urarka ta fara maka dangerda. Suna yin amfani da abun amfani da dama wadanda mutane suka fi shahara wajen yin kallon video da su a cikin computer, amma a wanda yafi ko wannen shahara shine a Quick Time Player, wacce ake amfani da ita wajen kallon video da ya kare da .mp4.
Matakin da zaka dauka idan ka ziyarci wannan shafi
Babu wani mataki da zaka dauka wajen kare kanka da irin wadannan video matukar kai mai son kallon video ne a internet ko kuma sauko da su ill aka rika ko da wane lokaci updating players dinka, domin wadannan kamfanoni masu yi player suna kara matakai na tsarewa da kuma gyaran wani matsala da zasu iya fuskanta a kowane lokaci. Idan kuwa kana da sha’awar kallo to ka kasance kana kallo a gidajen da yake suna da aminci kamar YouTube da kuma kayi amfani da gidan kallo irin na iTunes.
Cuta ta 11
Shafukan Intanet waɗanda suke tilasta wa mai shigan su saukar da Malware lokacin da ya ziyarce su.
Inda ake samunsu: Shafukan da Hackers su kwace ragamar sa.

A Turance ana kiran irin waɗannan shafuka da ’Drive-by Download’ shafuka ne waɗanda suke tilasta wa wanda ya ziyarce su domin ya saukar da waɗandu program zuwa ga Kwamfutarshi ba tare da ya sani ba. Za kuma a iya samun irin waɗannan matsalar a shafuka da dama. Kodayake mafi yawancin shafuka da ake ?ir?iransu domin saukar da irin waɗannan ?ananan program sau tari da gangan suke yin haka, waɗansu kuma rashin sa’a ake yi har hackers su ?wace ragamar tafiyar da ha?ar shafin, sai su saka abin da suke bu?ata ba tare da su kan su masu asalin shafin sun sani ba.
Matakin da za ka ɗauka idan ka ziyarci wannan shafi
Abu na farko shi ne idan ka san kai mai yawan shiga kowane irin shafi ne to, yana da kyau ya kasance koda wane lokaci Kwamfutarka ta na da cikakken tsaro, kuma kana updating din shi, kuma kana scanning Kwamfutar domin bincikar ko irin waɗannan program su shigo cikin ita Kwamfutar. Domin mafi yawan Anti-Virus suna iya gano irin waɗannan ?ananan program kuma su na iya cire su kai tsaye.
Cuta ta 12
Anti-Virus Software na ?arya ko bogi waɗanda aka yi su domin a ?arar maka da kuɗinka ko kuma a kwashi bayanan sirrinka.
Inda ake samunsu: Cikin akwatin Imel ɗinka da shafuka da aka yi Hacking ɗinsu.
Sau tari mutane bas u cika mai da hankalinsu a kan abin da ya shafi anti-virus software ɗinsu ba. Domin kuwa shi anti-virus ya fi zama komai hatsari a cikin harkokin da mutum yake yi tare da Computer. Irin waɗannan Anti-Virus na bogi mutum na iya saka su a cikin Kwamfutarsa bayan ya samo su a internet ya yi downloading ɗinsu da nufin cewar zai duba lafiyar Kwamfutarsa. To, a daidai lokacin da ya gama saukowa ka saka shi a cikin Kwamfutar sai bayan ka umarce shi da ya duba lafiyar Kwamfutar zai faɗa ma ka cewar ya samo matsaloli ma su yawa, waɗanda dole ka ce ya cire su. Saboda haka, da zarar ya cire kamar ashirin cikin ɗari biyu sai ya ce shi na gwaji ne, idan ka na bu?atar a cire dukkanin virus da ya kamo to sai ka sayi cikakken shi. Saboda haka da zarar ka ɗauko credit card ɗinka ka saka domin ka siya sai kawai su saci bayanan wannan kati ko dai su kwashe dukkannin abin da shi katin ya ?unsa na kuɗ ko kuma su ri?a sayan kaya ma su tsada da katin.
Matakin da za ka ɗauka idan ka ziyarci shafin
Duk lokacin da ka tsinkayi wani sabon sa?o da ya fita yana sanar da kai cewar wani sabon Virus ya shigo cikin Kwamfutarka kuma ka tabbatar cewar ba Anti-Virus din da ka saka ba ne ya fito da wannan sa?on to nan take ka kashe Kwamfutar, ka tashe ta ta SAFE MODE sannan ka kunna anti-virus ɗinka ka umarce shi da ya binciki ita Kwamfutar domin ya gani idan da gaske ne akwai ba?on virus.
Kodayake ba kowane Anti-virus ba ne ya ke da ilimin kowane virus ba, shi ya sa yana da kyau mutum ya sayi antivirus na ?warai sannan ya ri?a yin updating ɗin shi a kowane lokaci. Idan kuma haka ta faskara bayan ka kashe ita Kwamfutar ka tashe ta a SAFE MODE amma daga baya ka fahimci cewar yanayin yadda Kwamfutar ta ke yin aiki ya chanze, to sai ka nemo ?wararru domin su gano maka matsalar.
Cuta ta 13
Talla a shafuka da suke kai mutum zuwa ga masu cuta ko saukar da malware a Kwamfuta
Inda ake samunsu: Kusan kowane irin shafi da ya ke ɗauke da talla a cikin shi.
Ba kowane irin shafi ba ne da za ka ga talla a cikinsa ne ya ke ɗauke da talla da zai kai ka zuwa ga irin waɗdancan mugayen shafuka ba. Kusan ita talla da ake ganinta a shafukan internet su ake amfani da su wajen biyan wahalhalun shi website ɗin. Su irin waɗannan tallukan da ake ganinsu a shafuka ma su aikin cuta ko kuma fasa ?wauri a internet sukan ?ir?iri irin tasu talla wanda ya yi kama da talla ta zahiri, wanda idan mutum ya latsa domin ya ga abin da wannan tallar ta ?unsa sai kawai ya faɗa tarkon su.
A shekarun baya, kamfanin jaridar nan na ?asar Amurka ’New York Times’ a cikin shafinsu na internet cikin rashin sani su ka saka talla na shafin scammer wanda ya kawo ma su hallartar shafinsu su ka faɗa hannun ’yan baranda. Haka su ma kamfanin Google sun taɓa saka talla daga irin waɗannan gidaje cikin rashin sani wanda ya kai ga al’umma faɗawa ciki.
Kamar yadda wani babban ma’aikaci a kamfanin GFI Software Eric Howes ya faɗa ne cewa “masu fasa ?wauri a internet kullum sake samo hanyoyin cuta suke yi, yanzu burin su shi ne su ga sun lalata dukkanin wa ta kafa wacce ake talla da ita, ta hanyar kai mutane zuwa ga shafuka da suke ɗauke da ?wayoyin cutar da Computer ta yadda wanda ya ziyarci shafukan zai sami illa ga na’urarsa.
Matakin da za ka ɗauka idan ka ziyarci shafi
Idan mutum ya faɗa irin waɗannan shafuka waɗanda akwai talla a cikin su, mutum ya lura da kyau ya tabbatar da cewar ya san shafin da zai shiga, sannan kuma ya sani cewar ba dukkanin talla ba ne ke ɗauke da irin waɗannan cutuka ba. Kuma yana da kyau mutum ya kasance ana’urarsa akwai anti-virus mai lasisi.
Cuta ta 14
Application da suke facebook masu yin tambayoyi.
Inda ake samunsu: Facebook

Application da ake samu a Facebook mafi yawancinsu ba suna zuwa ba ne da matsala, sai dai mutane da dama suna ganin cewar Hackers a wannan lokacin suna yin amfani da irin wannan application waɗanda ake yin amfani da su wajen yin tambayoyi domin amsawa. Irin waɗannan application suna iya bijiro maka a shafinka na facebook tare da hoton da kuma sunan abokinka da cewar yana tambaya game da matsayin abu kaza, ko kuma ’Shin ka yarda cewar wane zai iya yaudarar ka?’ Irin waɗanna tambayoyi da makamantansu, wasu hackers su suke shirya shi ’application’ din domin su ɗauki bayanan sirri na mutum su yi amfani da shi daga baya domin cimma burinsu. Kodayake irin waɗannan application din kafin su fara aiki a cikin shafinka na sada zumunci na facebook sai ka ba su izini, shi ya sa yana da kyau matu?a ko da wane lokaci ka ri?a bibiyar wajen saita shi shafin facebook ka na duba waɗanne application suke amfani a cikin shafinka, sannan kuma su na da amfani a wurinka ko ba su da amfani.
Matakin da za ka ɗauka idan ka ziyarci shafin
Ya zamanto koda wane lokaci ka na mai tantance wane irin application ne z aka yi amfani da shi a shafinka na facebook, sannan kuma ya zamanto ka na yawaita bibiyar bayanai na shi wannan application. Ka kasance kana bibiyar wajen saita facebook naka, ka na kuma domin wane abubuwa ne ya kamata mutane su gani tare da kai ko kuma kada su gani tare da kai.
Cuta ta 15
Shafukan intanet waɗanda za su matsa maka da cewar ka yi ’Sign Up’ daga baya su sayar da adireshin ka na imel zuwa ga spammers.
Inda ake samunsu: Shafuka waɗanda ake kira da ’Free Electronics’
Babu shakka akwai irin waɗannan shafukan waɗanda ake iya gane ta hanyar yadda suke tunkarar masu mu’amala da su ta hanyar tallata masu wata haja, kamar misali ka ga ’Get a free iPad’ ko kuma ’Get a free notebook! Gaskiyar magana irin waɗannan shafukan a zahiri ba su da wata matsala, domin abu ne mai matu?ar wahala idan ka shiga irin waɗannan shafuka ka sami malware ya shigo cikin Kwamfutarka. Amma matsalar shi ne bayanan ka da ka shigar lokacin da ka yi ’sign up’ za a iya sayar da su ga waɗansu ’yan kasuwa.
Matakin da za ka ɗauka idan ka ziyarci shafi
Idan ka tsinci kanka a irin waɗannan shafuka yana da kyau kafin ka shigar da bayanan ka ka karanta sharuɗansu da ?a’idojin yin amfani da shafinsu ’privacy policy’ wanda a cikinshi idan ka karanta za su iya ga ya maka cewar ga abin da za su yi da bayanan da su ka karɓa a wurinka. Shi ya sa yana da kyau duk wanda zai shiga wani shafi da ake bukatar ya cike ’form’ to ya tabbatar ya karanta dokoki da ?a’idojin shiga shafukansu domin ya san me zai faru da bayanan da ya shigar a nan gaba. Kodayake wani lokaci a kan samu bayanai na ?arya a wurin ma su shafuka amma dai irin waɗannan bai ciki shahara ba. Amma dai ko ma me su ka faɗa ko su ka rubuta babu wani abu da ke iya tabbatar da cewar za su sayar da bayanan ka ko ba za su sayar ba.
Cuta ta 16
Shafukan sada zumunta ’Social Network’ waɗanda za su zambace ka har ka saukar da malware a cikin kwamfutarka daga baya ya aikawa da macuta bayan ka.
Inda ake samunsu: Shafukan sada zumunci ’social networks’

Ban da application mai yin tambayoyi da kuma ?ananan links da suke kai mutum ga shafukan da za su cutar da Kwamfutarsa. Shafukan sada zumunci kamar Facebook ya yi ?aurin suna da kuma samun magauta wajen ?o?arin yaɗa dukkanin wani abu da zai iya zama barazana ga shafukan sada zumuncin. misalin Scammers za su iya ?wace ragamar tafiyar da shafin sada zumuncin ka na facebook sannan su saka wani ɗan ?aramin link da zai ba abokananka damar shiga wannan shafi wanda in da za a kai su shi ne wajen cutar da Kwamfutarsu. Wannan kuwa ya haɗa da ?wace ragamar tafiyar da shi shafin daga hannun mai shi da yin amfani da dukkanin ma su hulɗa da shi da ɗiban bayanan sa da kuma kai shi hannun masu fasa ?wauri a intanet.
Babbar matsalar da ma su amfani da shafukan sada zumunci irin su facebook da twitter za su fuskanta shi ne barazanar malware, da adware da kuma spyware ta suke yawo sa?o-sa?o na internet. Mutane za su iya ganin abubuwa ma su ban sha’awa wanda suka haɗa da hotuna da kuma video wanda a zahiri manufar saka irin waɗannan hotuna domin ka faɗa hannun ’yan baranda ne. Wani lokaci ma za ka ga application da zai gyara maka shafinka na facebook ko twitter ’widget’ wanda kai ma da kan ka z aka yi sha’awa amma bayan ka saka su a cikin shafinka sai ka samu babu abin da zai kai ka illa ya kawo maka su adware da malware ko kuma spyware a cikin Kwamfutarka ko kuma shafinka na sada zumunci.
Matakin da za ka ɗauka idan ka ziyarci shafin
Kada ka yarda da kowane irin link da ka gan shi a shafin sada zumunta na facebook ko twitter, ko da kuma ɗaya daga cikin abokanan ka ne ya saka shi. Kafi ka latsa wannan shafi ya fara shiga asalin shafin da aka ce wannan maganar take ka duba ka gani da gaske ne ko kuma yaudare. Ko kuma ka kira shi wannan abokin na ka ka tambaye shi ko shi ne da kanshi ya saka wannan link ɗin ko kuwa ba shi ba ne.
Idan kuwa kai ne aka yi amfani da shafinka ake aikawa da mutane irin waɗannan bayanai, sannan kuma ka ke zargin cewar an ?wace ragamar tafiyar da shafinka ne, to mataki na farko shi ne ka canza ’password’ ɗinka. Ya na kuma da kyau ka ri?a ziyartar ɓangarorin shafukan zumunta da suke warware bayanai na cututtuka da ke cikin su, domin akwai shafuka da ke cikinsu waɗanda su ne suke bayani a kan irin waɗannan miyagun mutane. Waɗanda suke facebook za su iya shiga ’security page’ waɗanda kuma suke twitter za su buɗe @spam da @safety domin sanin mene ne matsalar tsaro da ake fuskanta a irin waɗannan shafuka na sada zumunci.
Cuta ta 17
Saka bayanan barkatai da suka shafeka a cikin shafukan sada zumunci
Inda ake samun su: Shafukan sada zumunta ’social networks’
Mutane ba su cika damuwa da wane irin bayanai za su saka ba a cikin shafukan su na zumunta, za ka samu samari da ’yan mata suna zuba bayanai da bai dace kowa ma ya sani ba sai dai su a cikin shafukan sada zumunci. Irin waɗannan bayanai ba wani matsala ba ne ga lafiyar computer ko kuma su shafukan. Sai dai matsalar a nan ita ce bayyana bayanai da za su iya cutar da kai kan ka da kuma bayanai waɗanda wani ka iya amfani da shi domin ya yi abin da bai dace ba.
Kamar misali za ka samu samari da ’yan mata suka saka bayanai wanda ya shafe su, ko kuma ya shafi iyalansu, ko kuma ya ke faruwa cikin gidan su, ko kuma labarin cewar gobe ko yau zan je wuri kaza, duk irin wannan yana faruwa a cikin facebook da twitter da 2go wanda mutum bai san wane ne ke bibiye da shi ba a cikin wannan shafi, sannan kuma mene ne zai biyo baya,
Matakin da za ka ɗauka idan ka ziyarci shafin
Wannan ba wani abu ba ne, domin mutum zai rage saka bayanai ne barkatar, da kuma lura da abubuwan da mutum yake yi a cikin shafukan sada zumunci.
Hakikanin gaskiya kamar yadda aka lissafo wadannan shafu ka masu hatsarin gaske naji dadi matuka saboda wannan ma cigavane domin ragewa masu sha’awar zaluntar jama’a a internet.ALLAH ya saka da Alkairi.
Salam!
Duk wadannan bayanai hakane, kuma zaka ga duk wurare ne da mutane suke ziyarta a kullum. Wanda kuma yafi matsala shine gidan nuna tsiraici, abin mamaki sai kaga zai yi wuya mutum ya ketare wannan waje. Allah Dai Ya Kyauta.
Idan mutum ya kiyaye to computar sa ta tsira.
Godia Mai tarin yawa gareku. Allah ya kara basira.
Allah ya saka da alkhairi.
SLM Mlm Salisu Allah yaqara daukaka yakuma budamaka mafitu arayuwarka
agaskiya Na Gamsu
Allah ya saka da alkairi
Allah yasaka da alkairi
Jazakallahu khairan don Allah muna don ƙarin bayani akan yahoo boy hanyoyin kare kanka daga fadawa tarkon su