38.5 C
Nigeria
Saturday, May 10, 2025

Sabuwar Laptop Me ake dubawa

Salam. Wai shin,menene abubuwan la’akari in inason in sayi sabuwar laptop kuma wani brand yafi inganci? Not advert lol

Malam Mustapha Adam, akwai abu na farko da ake la’akari da shi a lokacin da mutum zai sayi kayan wuta ba ma dole sai computer ba, shine suna da inganci? idan aka zo ga maganar computer laptop kusan gaskiya campanoni da dama a wannan lokaci… suna matukar kokari wajen ganin sun wuce tsara, amma idan maganar wace irin laptop zaka ka siya saboda ingancinta to ya danganta da aljihunka domin kare da kudin shi ai zai sha lahaula. Idan kuwa ka zo siya ka duba mene ne girman processor dinsu, kuma mene ne girman RAM din su, mene ne kuma karfin batirin ta awa nawa take yi, domin a wannan lokacin karanci ka samu sabuwar laptop tana yin awa hudu da rabi cikakke kafin ta dauke, daga baya sai ka duba girman HARD DISK dinta, sannan kuma ka duba girman ta domin wata ta fiye kankanta wata kuma tafi girman da yawa ka duba matsakaiciya wacce ba zata baka wahala wajen dauka ba. sannan bayan ka biya ka lura da yi mata charging kafin fara amfani da ita domin rashin yi mata charging da farko yakan lalata batir, sannan kuma kada ka rinka saka mata program da ba zaka yi amfani da suba kuma ka guji saka games da video da baka san daka inda ta suke ba. Kuma tunda ka yi kokari ka saya laptop da kudi mai yawa to ka daure ka siya sabon antivirus daga company kaspersky ko kuma norton domin duniya anyi ittifaki babu wanda ya fisu defination na virus. A sha ruwa lafiya Allah ya karbi Azumin mu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Jagora Zuwa Ga Koyon HTML: Yadda Ake Gina Website a Hausa

Gabatarwa: Fahimtar Tubalin intanet A wannan duniyar tamu, kusan kowane...

Yadda ake amfani da Google Drive

Google Drive wata ma’ajiya ce da kamfanin Google dake...

Blockchain a Gwari-Gwari

Wannan wani kirkirarriyar fasaha ce mai wuyar sha’ani da...

Fasahar AI: Kafin Musulmi yayi amfani da ita dole yasan wadannan abubuwa guda 7

Rubutawa: Salisu Hassan Webmaster GabatarwaA zamanin da na’urori ke iyan...

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img