38.2 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

Mene ne aikin Tauraron Dan Adam

Assalamu alaikum duniyar computer don Allah ina tambaya ne, wai yaya ne tauraron dan adam take ne wai? A sama ake har bashi? koko sama yake yana dauko bayani, labarai da hotuna?

Wato da kaji a na cewa tauraron dan adam bawai tauraro bane, wani injine da ake kerashi ake saka mishi kayan zamani na sadarwa ake kuma jefashi a sararin samaniya, da yake mahalicci makadaichi wato Allah ya halicci sama da nau’o’i launi – kala akwai bangaren da babu iska babu kuma wani abu da zai iya yin wani motsi wato idan ka jefa dutse har yakai wannan wuri zai tsaya cik ba tare da ya motsa ba, to, turawa da kasahen da suka ci gaba suna jefa wannan injin domin saukake musu hanyar sadarwa, wanda wannan rubutu da kayi sai da ya shiga cikin wannan tauraro sannan ya shigo cikin akwatina na facebook haka labarai da kake gani a nayi irin na BBC ko CNN da makamantansu duk suna amfani da wannan, uwa uba ana amfani da irin wannan tauraro wajen lura da tsaron kasa, kusan duk kasar da akace ta jefa irin wannan tauraro kuma tana iya sarrafashi to hakika na saka ta a cikin kasahen da suke da tsaro, misali kaga kasar amurka takan jefa irin wannan tauraron domin ta rinka dauko bayanan sirri na wasu kasahe, shi yasa wasu wadanda suka shahara suke kabo irin wannan tauraron saboda kare kasarsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img