Firewall Software yana baka damar ka yi iko da dukkan abin da zai shigo na’urarka idan tana hade da internet, ko kuma abin da na’urarka za ta aika cikin Internet.
Gwanayen sata (Hackers) ko da wane lokaci kokarin su shi ne su ga sun huda na’urar ka, ta hanyar internet wanda zai ba su damar satar makullenka (Password), bayanan (Credit Card) da dai wasu muhimman bayanai da sirri da ke cikin na’urarka. Idan ba a yi sa’a ba, za su iya kwace damar tafiyar da ita kanta na’urar ta yadda za su bankado dukkan wani sirri da ke cikin wannan na’ura, kuma su iya samun damar kai farmaki da tarin naurorin da ke hade da taka ta (Remote Server). Idan kana son ka rabu da wannan sharrin irin wadannan Barayi, abu daya kake bukata, Katangar Wuta (Firewall Software).
Wannan shi ne misalin yadda Katargar Wuta take duk abin da ba a yarda da shi ba za ta kona shi kafin ya fado cikin na’urarka.
Firewall yana tsayawa ne tsakanin Kwamfutarka da kuma connection na internet, saboda haka shi software din yana lura da dukkan abin da zai shigo ko kuma ya fita daga internet.
Kana bukatar Firewall a kan na’urarka ko da kana da Anti-Virus a kan na’urar, Firewall yana tsare na’urar ka daga dukkan wani data (duba darasin Mece ce Na’ura mai Kwakalwa) ko sako da zai shigo na’urarka daga internet ta mafita daba a yarda da ingancinta ba, kodayake inda amfanin anti-virus yake shi ne Firewall baya iya duba file da suke shiga ko fita daga na’ura.
Akwai Firewall cikin Windows XP da Vista da Windows 7
Window XP da Vista da kuma Windows 7 suna zuwa tare da Firewall wanda shi abin da yake iya dubawa shi ne kawai abin da ke shigowa, ma’ana dukkanin abin da yake shigowa computer ta hanyar internet kawai shi yake iya lura da shi. To ka sani fa, gaskiya bai kai kula ko lura kamar yadda wasu software da aka yi su musamman domin lura da abin da ke shigowa ta internet ba yin aiki, wanda yake iya lura da ba wai abin da yake shigowa ba, hattama abin da yake fita, domin wani lokaci virus ma kan nemi ya tura wani sako ta hanyar amfani da email account (Duba darasin Virus), kuma aikin da shi virus din yake yi, shi ne ya tattara muhimman sirrin wannan na’ura, tun daga sunayen abokan huldarka, makullanka, credit card ya aika ga barayi ko ‘yan sane a internet.
Amfani da Firewall
Zaka iya sayan Firewall mai zaman kan shi da ‘yan kudi, kamar irin su Zone Alarm>. Za kuma ka iya samun Anti-Virus wanda yake tare da Firewall a hade. Saboda haka, idan ka sanya Firewall a kan na’urar za ka gaya mashi wadansu programs da ka ke son a ba su damar amfani da internet, sannan setin kara ko ihu idan wani program da ba a bashi dama ba, ya nemi shiga internet, ko kuma ya hana yamutsi shigowa na’urar.
Idan kuwa kana son ka gyara shirin da ka yi na Firewall bayan ka sanya shi a jikin na’urarka, to sai ka je kan teburinka (Desktop) ka latsa Icon din firewall program sau biyu a lokaci guda (Double-click). Bayan ya bude maka program din, sai ka zaBi program da kake so, ko kuma wanda baka son su hadu da internet, ko kuma ya hana dukkan program daga amfani da internet sai dai kawai wadanda aka ba su dama su yi haka.
Abinda ya kamata ka yi idan ka ga manuniya (Firewall Alert)
Firewall din da ke kan na’urarka zai iya nuna maka cewar ga wani program da ba a ba shi dama ya shiga internet ba yana son shiga, zai tambayeka a ba shi dama ko yaushe? Ko kuma a ba shi dama yanzu kawai, ko kada a ba shi damar shiga. To, wani lokaci yana da kyau ka duba ka ga wani program ne, sannan ina yake son ya shiga, idan ka fahimci cewar wannan program ga inda zai shiga. Misali Microsoft Word yana son ya samu damar shiga domin ya dauko maka wasu Update kamar hotuna, da dai sauransu, ka ga wannan ai babu illa za ka iya ba shi dama, kuma zama ka iya bashi dama kowane lokaci idan akwai bukatar updating ya yi ba tare da ya tuntuBe ka ba, haka ma Anti-Virus shi ma ka ga yana da muhimmanci ya yi update, domin ya tabbatar na’urarka tana cikin koshin lafiya. Amma idan baka fahimci wane program ne ke kokarin shiga internet, kuma baka fahimci ina zashi ba, to ka ga babu illa ka hana shi. Idan kuwa kana bukatar karin bayin wannan program sai ka latsa “more info” shi kuma zai shigar da kai Internet ya binciki bayanin wannan program idan yana da amfani ko kuma ba shi da amfani, sai ka sani.