- Kwamfutar tana tafiya a hankali ba kamar yadda ta saba ba.
- Makalewa wani lokaci
- Kwamfutar ta rika kashe kanta tana kunna kanta wani lokaci.
- Wani application ya rika nuna maka baya aiki kamar yadda ya kamata.
- Hard Disk ko makamantansu idan ka saka su su nuna maka cewar baka saka suba, ko kuma ba za ka iya aiki da su ba.
- Ya zamanta ba zaka iya printing ba yadda ya kamata.
- Sakwannin matsaloli da b aka san da su ba.
- Lalacewar menu ko rikicewar su ko kuma dialog boxes.
- Wani lokaci sai ka ga hakkin mallakar document (extention) ya maimaitu sau biyu ko fiye ga duk wani sako da ka bude shi kamar ka ga .jpg ko .vbs, ko .gif ko .exe sun bayyana har sau biyu
- Kawai ka ga anti-virus software din ka ya daina aiki haka kawai ba tare da wani dalili b aba kuma kai katsayar da shi ba, ko kuma shi anti-virus software din ya ki tashi kwata-kwata.
- Ko kuma ka ga ka kasa saka anti-virus software a cikin computer, ko kuma ya ki fita daga cikin computer.
- Bakin icons (maballai) ba da babu su a cikin Kwamfutar.
- Bakon waka ko kuma sauti ya fara fitowa daga speaker ta computer wanda kai ba kai bane ka kunna wanan sauti, kuma inda ka kashe computer wani lokaci sai ta sake saka wannan sautin.
- Haka Kwamfutar ta ki tashi, gashi kuma kai baka yi wani ayyanannen canji ba, baka saka wani sabon program bah aka kuma baka cire wani program ba..
- Modem da kake browsing da shi ya rika yin wadansu aiki da ba kai ne ka saka shi yayi ba, ko kuma ya rika harba wutar aiki da sauri fiye da yadda ka san cewar haka yake yi. Wannan yana faruwa ne a lokacin da ka saka software da aka gurbatasu kai kuma baka san an gurbata su ba (pirate software).
- Windows din ka ba ya ki tashi sabo da wani hamimmin file ya bace, wani lokaci ma sai an lissafa maka files din da suka bace.
- Wani lokacin idan an tsahe ta zata tashi kamar yadda aka sa rai, amma kafin ta kai desktop sai ta makale ko kuma kafin ta nuna icon na desktop kima kafin taskbar ya bayyana.

shin idan daya daga cikin matsalar nan tafaru dani yazanyi na magance ta
Shin wayar salula tahannu nokia kirar asha 201 tana kamuwada cutar virus kuwa
IDAN COMPUTER TA KAMU DA VIRUS HARBA NA IYA HAWA INTERNET YA XANYI, KUMA CD ROOM DINA BAYA BUDEWA SHIMA YAXANYI
Wace software ake amfani da ita wajen hada virus kuma ya ya ake hada antivirus
Ko veirus yana iyasa wani hardware yadena aiki kuwa?
Virus ba ya iya lalata Hardware sai dai ya bata Software da yake sarrafa wannan Hardware. Yin haka kuwa zai sa shi Hardware ya dai na aiki.
Mungudi Allah yasaka da alkhaire
Ina da matsala daya, wato :: Wani lokaci sai ka ga hakkin mallakar document (extention) ya maimaitu sau biyu ko fiye ga duk wani sako da ka bude shi kamar ka ga .jpg ko .vbs, ko .gif ko .exe sun bayyana har sau biyu: dan Allah me ya kamata inyi.
Wannan yana nuna maka cewar kwamfutarka tana dauke da cutar virus kuma wannan matsalar ba zata kaudu ba sai ka yi amfani da antivirus mai kyau.