Wannan lamari na barin account da mutumin da ya rasu a social network yana bai wa mutane da dama haushi da takaici, musamman waɗanda suke kusa da wanda ya mutu. A wani lokaci za ka ga mutane suna jingina (tagging) hotunan banza ko na batsa ga shi wannan mamaci, haka za ka samu duk shekara mutane su yi ta masa murnar cika shekara (birthday) amma alhali shi yana lahira, wasu waɗanda suka saba wasa da shi, idan suka yi magana da shi bai amsa ba su yi fushi ko zagi da dai makamantan su.
Muna yawan samun ƙorafe-ƙorafe a wurin jama’a musamman waɗanda suka damu da makomar ‘yan uwansu waɗanda suke da account a Facebook ko Twitter ga shi kuma Allah Ya yi musu mutuwa dangane da ya za a yi su iya goge wannan account domin yadda hankalinsu yake tashi duk lokacin da suka ga hoton shi ko kuma wani abu makamanci haka.
Wannan dalilin ne ya sa muka yi bincike muka gano ashe tun tsawon wancan lokacin da muke ganin haka tuni kamfanin Facebook suka fito da wani fom wanda shi ne kawai abin da kake buƙata domin goge irin wannan account ɗin.
A GYARA HALI KAFIN A MUTU.
Yana da kyau duk wanda yake karanta wannan takarda ya sani wata rana shi ne wanda mutuwa zata riske shi, kuma bai san wani lokaci ba ne, kuma bai san a wani hali ba ne. Yana da kyau mu riƙa tsaftace abubuwan da muke saka wa social networks domin duk abin da ka saka yana nan kuma wani ya killace shi. Kuma da ni da ku duk mun san watan wata rana za a tambaye mu, kuma sai mun bayar da bahasi a kai.
Mutane da dama basa la’akari da cewar duk abin da na rubuta ko na saka a social network Allah Zai tambaye ni, idan na saka wata magana ta ƙarya wani ya yaɗa to zunubin yana kaina, haka idan na yaɗa abin da yake na alkairi ladan yana kaina. Mu guji yiwa mutane ƙazafi, saka hotunan da basu dace ba, da kuma yaɗa jita-jita da zarge-zarge domin waɗannan abubuwan suna da wahalar tuba kuma suna da wahalar kankarewa.
INA ZAN SAMI FOM DA ZAN CIKE
Shi wannan fom da za ka cike, yana da waɗansu ƙa’idoJi da ya kamata mutum ya sani, kuma aKwai abu mai muhimmanci da kowa ya kamata ya kiyaye.
Kamfanin Facebook basa la’akari da garinka ko kuma addinin ka, suna la’akari da addininsu da kuma al’adunsu, saboda haka abin da suke buƙata wurin cike fom ɗin shi ne takardar shaidar cewar wannan mutumin ya mutu wacce kotu ko Asibiti suka tabbatar da haka. Saboda haka kafin ka fara cike wannan fom sai ka je ka karɓi takardar shaidar cewar wane ya mutu, sannan ka yi scanning sai ka fara cike fom ɗin.
Za a iya buɗe wannan fom ɗin ta bin wannan link kamar haka https://www.Facebook.com/help/contact/228813257197480
Fom ɗin wanda da Turanci aka rubuta shi yana buƙatar ka amsa tambayoyi guda takwas (8) kafin ka aika shi wanda su kamfanin Facebook za su duba su gani sannan daga baya su goge shi wannan account ɗin.
TAMBAYOYIN DA AKA AMSA
- Cikakken Suna: A wannan ɓangare ana son kai da za ka cike wannan fom ɗin ka saka sunanka cikakke misalin Salisu Hassan
- Sunan wanda ya mutu: Shi kuma rami na biyu sai ka rubuta cikakken sunan wanda kake son a gogeaccount ɗinshi, namiji ne ko mace.
- Imel ɗin mamaci: a na son ka saka imel ɗin da kake tunanin cewar da shi wannan mamacin ya buɗeaccount, kodayake wannan imel ba dole ne ka san shi ba, kuma idan ma ba ka cike wannan ramin ba saboda rashin sani babu matsala, amma saka imel ɗin zai baiwa kamfanin sauƙi zaƙulo account ɗin kuma su goge shi.
- Link ɗin mamaci naFacebook: Duk mutumin da ya buɗe Facebook, suna bashi wanilink (hanya ko rariyar liƙau) da ita ce hanyar shiga shafin ka kai tsaye, kuma wannan hanya babu mai ita a Facebook sai kai. Misali nawa shine https://Facebook.com/salisuwebmaster duk mutumin da ya rubuta wannan link a jikin browser to zai kaishi shafi na Facebook kai tsaye. To idan ba ka san na wanda ya mutu ba, abin da za ka yi shi ne ka nemo shi a cikin abokanenka, sai ka taɓa sunan shi, zai kai ka kai tsaye cikin shafin sa, sai kayi amfani da browser ka kwafe link ɗin da ka gani sai ka saka a wannan ramin.
- Dangantar ka da mamaci: LallaiFacebook suna buƙatar su san dangantakar ka da wannan mamaci kafin su cire wannan shafi a gidansu. Saboda haka za ka zaɓi dangantakar ka, a cikin kashi uku da suke da shi.
- Iyalai mafi kusa: Kai ɗan uwansa ne, ko baban sa, ko matarsa ko kuma yayansa da dai makamanta su.
- Dangantakar jini: Kamar kaka, goggo, baffa, da kawu da dai makusanta na jini
- Abokantaka: Idan wanda ya rasu, abokinsa ne ko kuna aiki wuri guda ne ko kuma aji ɗaya kuka yi, ko kuma ma dai ka san cewar ya mutu ne, sai ka zaɓi nan.
- Me kake sonFacebook su yi da account ɗin: A nan Facebook suna son ka faɗa musu abin da kake son a yi maka da account ɗin domin ba goge shi kaɗai za su iya yi ba, a nan aƙwai abu guda huɗu (4) da za ka iya ba su dama su yi.
- A faɗa wa abokansa ya mutu: Wannan zaɓi ne da za ka baFacebook na su saka a cikin shafinsa cewar wane fa yanzu ba shi, ya mutu, kuma su saka alamar da kowa zai iya ganewa cewar yanzu da gaske babu shi.
- A gogeaccount ɗin sa: wannan shi ne ɓangaren da ya fi kyau a yi amfani da shi, domin zai ba Facebook dama su share dukkan abin da wannan mamacin ya saka a cikin Facebook, tun daga rubutunsa, likes da comments da sharing da hotuna da video da ya sa a Facebook, yadda ba shi suna ba su.
- Ina da buƙata ta musamman: idan kuwa aƙwai wani abu da kake buƙatarFacebooksu yi maka ba sharewa ba to sai ka zaɓi wannan ɓ
- Ina da tambaya: wannan kuma idan kana da tambaya da kake son kayi waFacebooksai ka zaɓi wannan ɓ
- Yaushe mamacin ya rasu?:A wannan ɓangare suna son ka zaɓi rana da wata da shekarar da ya mutu ka saka musu.
- Takardar shaidai mutuwarsa: A wannan wurin shi ne za ka sakawaFacebooktakardar shaida daga kotu ko asibitin da mutum ya mutu cewar wannan mutumin ya mutu, ko shaida da mutane gidansu cewar su suka ba ka izini cewar Facebook su cire shafinsa.
- Da zarar ka gama cikewa sai ka aika musu da wannan fom domin su duba su gani sannan su yi abin da ka ce kana so.
Ba kamar yadda mutane suke tsammani ba, zai ɗan ɗauki lokaci kafin kamfanin Facebook su waiwayi takardar, domin kamfanin da yake da mutane sama da biliyan ɗaya da rabi yana buƙatar lokaci kafin ya aiwatar da wani abu. Kai dai tun da ka aiki sai ka jira.
Kuma babu laifi idan mutane mabanbanta suka aika, misali a sami mutane da yawa su aika domin hakan zai sa Facebook su gane cewar wannan bawan Allah da gaske ne cewar ya mutu.
Muna rokon Allah Ya jiƙan waɗanda suka riga mu mutuwa da imani, Ya kyautata ƙarshenmu ya yafe mana kurakuranmu, ya amintar da mu baki ɗaya. Amin
Assalamu alaikum Malam SALISU barka da war haka da fatan kana cikin koshin lafiya,
Tambaya shin ya dace mutum ya ba wasu manhajoji permissions su samu information akan *calls recording da messages da phone books da sauran su?