38.1 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

Find My Android’: Sabuwar hanyar gano wayar da aka sace!

A wani sabon yunƙuri da kamfanin google na ƙasar Amurka ya yi na sake fito da wata sabuwar hanyar magance satar wayar-komai-da-ruwanka (smartphone) mai ɗauke da manhajar Android shi ne na ƙara wani sabon kalmar bincike a shafin su na google mai suna Find My Android.

Wannan kalmar ita ce mutum zai yi amfani da ita a lokacin da yake neman wayarsa, ko ta wurin tunanin wani ya ɗauke ta, ko kuma ta hanyar neman ta domin rashin sanin inda ya saka ta.

Kamfanin wanda suka haɗa wannan tsari da tsarin da suke da shi na Android DeviceManager yana baka damar gano wurin da wannan wayar take, kuma har ya baka damar kiran wayar domin jin ƙarar ta idan mutum yana tunanin cewar wayar tana kusa da shi.

Wani ƙarin abin jin daɗi shi ne, shi wannan tsari zai buɗe maka taswirar wurin da wayar take (Map) ta amfani da google Map, ya nuna maka daidai inda wayar take a yanzu, ko kuma lokaci na ƙarshe da google ya sami labarin inda wayar take.

Abubuwan da mutum yake buƙata a wannan tsari shi ne mallakar gmail account, kamar yadda muka yi bayani a cikin muƙalar mu mai taken Android – Tambayoyi 7 Da Mai Amfani Da Wayar Android Ya Kamata Ya San Amsarsu A wannan muƙalar mun yi cikakken bayani a kan muhimmancin mallakar gmail account ga duk wanda yake riƙe da waya ƙirar Android. Idan kana buƙatar sanin yadda ake buɗe gmail accout za ka iya kallon bidiyon gmail ta wannan hanya Yadda ake buɗe Imel na Gmail.

 

YAYAFind My Android YAKE?

Find My Android: Ba manhaja ba ce, kamar yadda aka saba a baya cewar manhajojin da suke iya gano waya idan ta ɓace za ka ga manhaja ce. Find My Android tsarin bincikene da kamfanin google ɗin suka ƙara a cikin surkullen binciken su. Misali idan mutum yana neman abu a intanet zai shiga browser kawai ya buɗe shafin google ya rubuta abin da yake nema, idan sakamako ya fito sai mutum ya zaɓi wanda ya fi dacewa da shi ya buɗe shi.

To shi ma wannan tsarin neman wayar kusan haka yake, idan kana neman wayarka abin da za ka yi sai ka nemi kwamfuta ko waya mai intanet ka buɗe browser sai ka rubuta www.google.com idan shafin ya buɗe sai ka yi sign in da imel ɗinka na gmail.

Shafin google a lokacin da ka rubuta www.google.com

 

[blockquote]Wannan imel da za ka yi amfani da shi ka tabbatar da cewar shi ne wanda kake amfani da shi lokacin da wayar take tare da kai. Da shi kake saukar da manhajoji da suke Google Play Store. Kasancewar duk abin da kake yi da wannan wayar gidan google suna lura da shi.[/blockquote]

Idan shafin ya karɓi abubuwan da ka saka na username da password sai ka dawo ramin da aka ajiye domin yin binciken abubuwa a google sai kawai ka rubuta Find My Android. Wannan shi ne kawai abin da za ka rubuta, da zarar ka gama rubutawa sai ka latsa maɓallin google search daga nan google zai fara bincikar inda ya ga wayar ɗazu ko kuma yanzu.

YA GOOGLE YAKE IYA GANO TA?

Kamfanin google suna amfani da abubuwa guda biyu wanda duk wayar-tafi-da-gidanka tana tare da su, Intanet da GPS. Duk wayar da aka ce Smartphone (wayar-tafi-da-gidanka ) ce to za ka samu tana yin browsing wanda shi ne ma dalilin da ya sa mutane suke son amfani da wayar. Global Positioning System (GPS) wata na’ura ce da ake amfani da ita wurin gano wurin da abu yake ta hanyar amfani da ilimin sanin wuri na Longitute da Latitude. Wannan na’ura ma’aikatu da dama suna amfani da ita, musamman masu fitar da filaye, ko taswirar garuruwa, ko masu neman faɗin wuri kamar masu aiki Ƙasa da Safiyo da dai makamanta su. To kusan dukkan wayoyin-tafi-da-gidanka suna da wannan na’ura ta GPS a cikinsu, wanda shi ne, mutane ke amfani da shi a Google Map wurin yin tafiya don gano wurin da mutum bai sani ba, ko kuma domin fahimtar adireshin da wani wuri yake.

Tun da wayoyin wannan lokaci suna amfani da Intanet da GPS sai kamfanin google suke yin amfani da wannan dama su gano wurin da wayar take.

ME ZAN IYA YI IDAN NA GA WAYAR TAWA?

Idan aka yi sa’a wanda ya tsinci wayar ya kunna intanet, to da zarar ka neme ta zai nuna maka wurin da take, idan kuwa a daidai lokacin da kake neman ta ba ta kan intanet to google zai nuna maka wuri na ƙarshe da lokacin da aka shiga intanet da ita.

Abubuwa guda uku zaka iya yi da wayar

  1. Kiranta: Da farko za ka iya sagoogle su kira wayar (ringing) wanda idan kana tunanin ba dauke maka ita aka yi ba, ka rasa inda ta shiga ne, kuma ba ka da wayar da za ka kira amma kuma ga kwamfuta mai intanet a wurin.
  2. Kulle Ta: Za ka iya rufe wayar yadda ba wanda zai iya amfani da ita. A lokacin da kake ƙoƙarin shirya yadda kake son wayar ta rufe, za ka cike wani ɗan ƙaramin fom da googleza su ba ka wanda za ka rubuta kalaman sirri da kake son ayi amfani da su wurin buɗe wayar (password), domin idan an kulle ta kuma aka ganta ba sai kayi amfani da intanet ba wurin buɗe ta ba. Sannan zaka rubuta saƙon da kake son wanda ya buɗe ita wayar ya gani misalin kamar ka rubuta “Wannan wayar an sace ta ne”. Daga ƙarshe sai ka sa lambar wayar wanda kake son a kira idan an tsinci wayar.

Wannan shi ne abu na biyu da mutum zai yi, yin haka zai kulle wayar duk lokacin da aka buɗe intanet ɗinta. Kuma ko da mutum ya yi factory reset, wato ya goge wayar ta dawo kamar ranar da aka sayeta, da zarar ta ji ƙanshin intanet za ta sake kulle kanta.

  1. Goge ta: Abu mafi muni da mutum zai yi shi ne ya goge wayar gaba ɗayan ta, ta hanyar lalata dukkan abin da ke cikinta. Ba ana maganarcontact da saƙonni ba ne, wannan tsarin zai baka damar goge wayar ce baki ɗayanta, ta hanyar goge manhajar wayar gaba ɗaya yadda wayar har abada ba zata yi amfani ba.

Wannan shine tsarin da kamfanin google suka ɓullo da shi domin magance masu satar wayar Android.

3 COMMENTS

    • Maraba da zuwa da fatan zaka ci gaba da bibiyar wannan shafi domin samun karuwa a kowane lokaci.
      Mun gode.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img