Bayan kusan shekaru biyu da kamfanin google suka yi suna ƙoƙarin nuna cewar sun kawo ƙarfi a lokacin da suka ƙirƙiro Tabarau me kwamfuta a jikinta, sance a yanzu suna ta ƙoƙarin tantance irin mutanen da za su yi amfani da su.
A hannu guda kuwa, kamfanin Microsoft a satin da ya gabata ya gabatar a karon farko yadda sabon manhajarsa mai suna Windows 10 zata kasance, wani abin jin daɗi a karon farko kamfanin ya yi alkawarin bayar da wannnan manhajar kyauta ga duk wanda kwamfutarshi take da manhajar Windows 7 ko 8.
HoloLens wani irin sabon tabarau ne da kamfanin Microsoft suka nuna shi a lokacin bukin nuna sababbin manhajojin da suke sanya ran cewar za su bayyana nan gaba.
HoloLens wani irin tabarau ne me dauke da kwamfuta a cikinsa, tabaran wanda baya buƙatar a haɗa shi da System Unit, kuma baya buƙatar jona shi da wuta ko keyboard ballantana mouse. Aikin da wannan HoloLens yake yi, shi ne tabbatar da abubuwan da mutum ke yi da kwamfuta zuwa zahiri.
Wani cikakken bayani a kan GoogleGlass da HoloLens sai mun haɗu a sabuwar Mujallar Duniyar Computer In Sha Allah!