38.2 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

Illan Kwamfuta Ga Ido, Hanyoyi Goma Na Samun Sauki

Ƙaruwar mutane da ke amfani da na’uran kwamfuta ya sa ana kokawa kan yawan samun zafi ko raɗaɗin da nauyin idanuwa. Bincike ya nuna cewa yawn samun ciwon idanu ko alamun hakan yakan faruwa a cikin kashi hamsin (50%) zuwa casa’in (90%) cikin ɗari na mutane masu amfani da kwamfuta musamman a wajen aiki.

Wannan matsalar kan auku ne saboda yawaita samun gajiyawar idanu a sanadiyyar ƙuri ga hasken kwanfuta.

Ga wasu hanyouyi guda goma (10) da ka iya rage ko sauƙaƙa wannan  matsalar

  1. Samu dubawar Idanu ka daga ƙwararru:- samun dubawar idanu a kai-a kai yana da matuƙar muhimmanci domin kaucewa ko magance matsalolin gani a sanidiyyar amfani da ita kwamfutar
  2. Taƙaita hasken kwamfutarka:- Zugin ido yana aukuwa idan hasken rana da ke shigowa ta taganka ko hasken lantarki mai tsanani ya yawaita. Rage hasken ko ka daidaita shi kamar yadda yawancin hasken ofishi yake,yin hakan yana taimakawa sosai. Ka rage hasken ta saukar da labulen tagogin ka sannan kada kasa ƙwaya-ƙwayan lantarki da yawa ta yadda haske zai yawaita. Kana iya amfani da marasa haske sosai. Sannan Idan zai yiwu ya zamo cewa na’uran kwamfutarka (monitor) ya zama tagarka na ta gefe ne maimakon ta gaba ko bayan monitor.

Saboda da yawa daga cikin masu amfani da kwamfuta sukan faɗi cewa sun samu sauƙin raɗaɗi ga idanuwansu idan suka bi wannan tsarin.

  1. Taƙaita ƙura idanunka:- ƙura idanu ga duk wani abu mai ƙyalli kai dama hasken kwanfuta kanta na iy haifar da zafi ko raɗaɗin idanu. Ka kwatanta amfani da irin gilashi nan da ake amfani da wajen rage matsanancin haske kwamfuta (anti galre screen) ko kuma ya zamo fentin ɓangon ɗakin ka ko ofishi ya zama mara haske sosai. Hakan zai taimaka maka sosai.
  2. Canza talbijin din kwanfutar ka (monitor):- idan ba ka taɓa canza akwatin kwamfutarka ba (monitor) daga tsohon yayi (CRT) wanda ke taimakawa wajen samun ciwon idanu to ka gaggauta yin hakan. Domin irin wanda ake amfani da shi yanzu bashi da kaifin haske da ka iya jawo maka ciwon ko zafin idanu.

Idan kuma babu hali ya zam dole kayi amfani da irin wannan na farkon (CRT) to ka rage kaifin haskensa. Ka duba hasken ta cikin control panel idan kaifin hasken na ƙasa da mizanin 70Hertz (Hz) to ka canza shi zuwa sama har ƙarshen sa.

  1. Daidaita saitin hasken kwamfutarka :- Daidaita hasken talbijin ɗin kwamfutan ka (monitor) zai taimaka maka sosai wajen rage nauyi  ko raɗaɗin zugin idanu. A takaice saita hasken yana da muhimmanci sosai kamar haka:
  2. Hasken kwalba (monitor);- rage shi zuwa hasken sa yadaidaita da hasken ɗakin ko ofishin da kake aiki.
  3. Girman harufa:- ka rage ko kara girman haruffan daidai da idanunka yadda za ka samu sauƙin ganinsu ( wato yadda ka ji ya yi ma)
  • Kaifin kala (colour):- amo na kala spectrum of visible light yana nashi illar ga idanunka. Idan baka daidaita shi ba musamman shudi 9blue) wanda yake da gajeren zango (short wavelrnth) zai cutar da ganin ka.

TSAURIN RUBUTU KO KALA NA’URANKA:-

Domin kauce war illar cutar da idanu haruffan rubutun ka ya kamata su zama girman su kamar linki uku mafi ƙarancin ganin ka na haruffan da kake iya gani.

Misali danna “Ctrl +” zai dinga kara grima fuskan monitor ne kawai. Sannan kuma ‘Ctrl o”zai daidaita shi sannan ‘Ctrl – “rage girman.

Idan kuma rubutu kawai kake so ka rage ko ka ƙara sai kai amfani da “Alt V’ sannan “Z” da “T”. sai kuma kayi amfani da “+” za ka ga rubuta ne ƙwai ke canza wa.

  1. yawaita ƙiftawa:- ƙiftawar idanu nada muhimmanci wajen kiyaye fama da matsalar idanu a sandiyyar amfani da kwamfuta. Ido na nasamun danshi a yayin da ka kifta saboda bushewada yake yi idan ka ƙura ma abu ɗaya idanu.

Da yawa dag cikin mutane za ka ga idan suna aiki da kwamfuta basa ƙftawa kamar yadda binciki yanuna.

Danshin ƙwalla da ke samun idan ka rufe kwayan idanu ta kiftawa yakan sa idanuwa su samu sauƙin raɗaɗi.

  1. Ka dinga yi ma idanun ka atisayi:-Babban abu dake haifar dazugin idanu shi ne gajiya. Domin rage gajiyar idanu saboda ƙuri na dogon lokaci da kake yi, ka dinga kautar da idanunka duk bayan mintuna ashirin. Sannan ka yi atisayi kamar haka, kalli abun d nesa kamar aƙalla ƙafa ashirin (20 feet) na tsawon kamar daƙiƙa ashirin (20s). Likitocin ido na kiran wannan tsarin da suna “20-20-20 rule” .

Wani atisayin kuma shi ne ka kalli nesa kamar na daƙiƙa goma – sha biyar (10 – 15 seconds) sai kuma ka ɗaga idanun ka sama sai ƙasa kamar adadin shi ma (10 -15 seeconds).

  1. Dinga samun hutu;- Domin samun sauƙi daga kamuwa da ciwon idanu, wuya da baya wanda yawan zama kan kwamfuta ke haifarwa, ka dinga samun hutu ( break) a kai-a kai.

Mafi yawancinmu masu aiki da kwamfuta ba sa samun isasshen hutu da ya dace da su ta inda hakan ke haifar da cutarwa gare su. Kamar yadda bincike yanuna. Wasu suna ganin cewa idan suka tsaya hutu kamar aiki zai wuce su. Idan ance hutu ba wai ana nufin ka zauna dirshan bane, ana so ka tashi kaɗan yi dan tattaki, miƙa, da miƙar da hannuwanka ,ƙafa, wuya da kafaɗunka domin karage gajiya.

  1. kyautata wajen aikin ka:- Yin irin zaman da bai dace ba kamar durƙushe da tanƙwarewa na cutar da jikinka da idanuwanka: Ka dai daita akwatin talbijin ɗinka (monitor) ta yadda ba sai ka durƙushe ba, wato ya ƙale fuskan ka na zaune. Ka kuma zaunar da shi kamar inchi ashirin zuwa ashirin da huɗu nesa da kai (20-24inches) akan teburinka.
  2. kana iya amfani da tabaron idanu:- Gaskiya ne idan ka yi amfani da tabaron ido zai taimaka maka sosai. Amma fa kayi amfani da masanan lafiyar ido suka tantance ko zaɓa maka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img