Abubuwa da dama zasu iya haifar da wadannan matsaloli a jikin Computer, tun daga rashin fara aiki akan lokaci, kin baka damar bude wani program da dai makamantansu.
Da farko dai ya kamata ka sani cewa ita computer tana da zubi irin na mutum, kamar yadda ka sani mutum na iya kamuwa da ciwo, tun daga zazzabi, mura, ciwon kai da dai makamantansu, to ita ma Computer tana iya kamuwa da kusan irin wadannan matsaloli, Na san mai karatu zai ce wani sabon salo, mai ke kawo a gane cewar mutum ya kamu da ciwo iri ka za,Duk lokacin da aka ji ya fiye korafi akan wani bangare na jikin shi, to, ai ita ma na’ura ana gane haka ne idan ka ga ta canza daga yadda ka saba ganin ta.
Kamar yadda na fadi cewar ita computer kamar mutumce, ta na iya kamuwa da wadansu matsaloli, wannan gaskiya ne, amma abu na farko da ya kamata shine ka gane wace matsala ita wannan na’ura ta kamu da shi kafin ka san hanyar magance shi.
Ba dole ka gane matsala nan take ba
Ba zaka iya gane cewar computer tana cikin wani matsala ba, matukar ba taka bace, abin da nake nufi idan ka ari computer wani, kana kuma son ka yi anfani da ita zai iya yiwuwa kaga bata aiki da sauri. Wannan kuwa ba hujja bace na cewa wannan na’ura tana da matsala, shi yasa take da wuyar budewa. Domin ya yiwu ita na’urar bata kai karfin wacce ka saba aiki da ita ba, ko kuma computer daka aro tsohuwa ce, ko kuma sabuwa ce amma RAM da ke jikin waccan wacce ka saba aiki da ita yafi na wannan girma, to, kaga ai dukkan wadannan ba matsala bace ga computer, ba wani abu ya faru da ita ba balle ace ta lalace.
To kaga idan da irin wadannan matsaloline zai yi matukar wahala a matsayinka na wanda ya ari computer ya gane cewar tana da matsala. Duk da cewar dukkanin na’urar da aka kunna ta, har ta kai tsawon mintoci kamar 4 zuwa 10 bata gama tashi ba to lallai akwai matsala.
Sai ka lura da kyau kafin ka gano matsalar
Kana iya gane computer ta sami matsala idan takace, kaine wanda ya sayeta da farko ko kuma kana amfani da ita a baya lafiya lau amma yanzu sai ta zamanto tana dan yin wandansu abubuwa da basu kamata ba. Misali a lokacin da take sabuwa da zarar ka kunnata cikin da kankanin lokaci sai ta tashi ta fara aiki, amma yanzu sai ka gaji da jira kafin ta baka damar fara aiki, ko kuma idan ka zo zaka kashe ta maimakon ta mutu da wuri sai ta dauki tsawon lokaci bata mutu ba.
Ko da yake idan mutum yana hade da Internet, kuma bai rufe Window Update ba, to, computer shi zata shiga Microsoft ta duba ta ga wani sabon tsari da aka kara ta dauko ta kara maka a cikin na’urar ka, to idan haka ta faru to na’urar da kanta zata gaya maka cewar ta dauko sababbin tsari daga Windows Update kuma tana bukatar ta ajiye ko wannan file a wurin da ya dace da shi, harma za ta fada maka yawan abubuwan da ta dauko misali 1 of 45 ma’ana ta dauko abubuwa guda 45 ta kuma sa daya. Haka idan ka daura wani sabon program wanda ya zama ya zo da sababbin tsare-tsare to shima wani lokaci zai dade kafin computer ta mutu.
Rashin kula ke kawo matsala a computer
Sau tari na’ura ba wani babban matsala take kamuwa da ita ba, ka ga mutum ya shiga cikin dimuwa da kuma damuwa, wani lokaci ma, rashin lura da wadansu kananan abubuwa shi ke iya kawo wannan matsalolin, wani lokaci rashin yi wa ita na’urar garanbawul, ko yawan amfani da manya-manyan programs a na’urar da ba zata iya daukarsu ba, ko kuma sauko da kananan program na kyauta daga internet, ko kuma sa games a na’ura ko wani iri, ko kuma amfani da program wanda bashi da lacici na asali sai dai abinda ake cewa crack, ko kuma Virus ya kamata. To, dukkan wadannan abubuwa da na ambata suna iya kawo matsalolin tashi da mutuwar na’ura.
Hanyoyin magance su
1. Virus Scanning
Duk lokacin da ka gano cewa yadda na’urar ka take tashi ko mutuwa ba haka ta saba yi ba, to daya daga cikin wadannan matsaloli ne, abu na farko da zaka yi shine ka tabbatar kana amfani da Anti-Virus wanda yake da cikakken tsaro, ko da kuwa na kyautane, domin akwa Anti-Virus na kyauta wadanda idan har kana updating din su, to, lallai Virus ba zai iya kama na’urarka ba. To, idan kana da Anti-Virus kuma kayi updating dinshi to sai kayi scanning na’urar gaba dayanta ka tabbatar babu wani virus a ciki, ko da yake wadansu Virus karfinsu ya kai Anti-Virus karami ya kasa gane su, akwai cikakken bayani akan Virus da yadda yake aiki.
2. Disk Cleanup
Bayan kayi scanning ka tabbatar da ba virus bane suke hana na’urar tashi ba, so sai kayi amfani da wadansu utility programs da suke cikin naurarka ka duba lafiyar hard disk dinka kamar haka:
Alama (=>) idan kaga wannan alama tana nufin ka latsa kalmar dake gabanshi.
=> Start Menu => All Programs => Accessories => System Tools =>Disk Cleanup
Wannan program na Disk Cleanup yana cikin kowace na’ura kuma binda yake yi shine ya taimaka ya share maka dukkan abinda ya saura ko kuma burbushin file da yaka mata basa cikin na’ura amma wani dalili ya sa basu fita ba. Haka shima Memory wani sa’ilin yakan bar irin wadannan burbushin file a cikin shi to wannan dan karamin program zai tai maka wajen share dukkan wadansu kazanta ko bola da suka rage.
3. Disk Defragmenting
Idan ka goge dukkan wadannan file sai ka koma ka duba lafiyar zaman kowane document dake cikin na’urar musamman idan kana amfani da manya-manyan files kamar audio da video da aiki irin na graphics, duk sanda ka cire su ko ka goge su a jikin na’urar to na’urar tana barin gurbin babu komai a wurin ita kuma na’urar sai ta rinka ganin kamar akwai wannan babban file a wajen to, idan kuwa aka yi rashin sa’a akan haka zata rinka dan dadewa wajen tashi. Ga yadda zaka yi ka magance wannan matsala => Start Menu => All Programs => Accessories => System Tools =>Disk Defragmenter
Shi wannan program na Disk Defragmenter yana taimakawa wajen daidaita sahun dukkanin file zuwa mazauninsu da ya kamace su, kamar yadda na fada a baya cewa idan ka share document na na’ura file din ke bacewa amma gurbinshi baya bacewa shi wannan program ke taimakawa wajen haka.
4. Check Disk
Hanya ta gaba ita kuma zata duba maka matsalar hard disk dinka ne, ta ga cewa dukkan kafa da file ko document ko program kai kuma meye dake jikin na’ura suna nan lafiya babu matsala a jikin su, domin rashin bin ka’ida wajen kulle na’ura ko kashe ta kamar yadda ya kamata ka iya jawo matsalar hard disk ya sami rauni, idan raunukan da hard disk yayi yawa zaka ji wani lokaci yana kara kamar kat-kat-kat, wannan kuma yana nuna maka alamar cewa nan gaba kadan za ka iya rasa dukkanin program da suke cikin na’urarka. Sau tari mutane sukan yi watsi da sakonni da na’ura ke fitowa da su a lokacin da aka dauke wutar lantarki kuma baka da UPS, zaka ga ta gaya maka cewar wannan na’ura ba a kashe ta ba kamar yadda ya kamata, saboda haka zata binciki babbar kwakwalwar ajiya domin gyara wata matsala da daukewar na’urar zai iya haifarwa, saboda rashin sanin mahimmancin wannan sako sai kaga mutane suna wucewa tunda dama biyu take bayarwa, kodai ka tsaya ta yi wannan bincike, ko kuma ta taba ESC a jikin na’urarka ta manta da wannan sako. Sai ka ga mutane suna daukar dama ta biyu.
Da zarar mutum ya hada wadannan matakai guda hudu, binciken virus (Virus Scanning), share datti ko bolar computer (Disk Cleanup), daidaita mazaunin file da document (Disk Defragmenting) sannan ka duba lafiyar babban hard disk (Check Disk) to babu shakka computer zata kara kuzari. Ko da yake ga wanda ya zamanto shi bakon amfani da na’ura ko kuma yana amfani da ita domin dan karamin aiki, ko kuma bai yi zurfi a kanta ba, amfani da irin wadannan kananan program zai iya bashi wahala duk da cewar basu da wani wahalar bi. Ko da yake akwai wasu program na musamman wadanda aka kirkiresu domin su magance irin wadannan matsaloli wanda latsa daya za ka yi duk yayi wadannan abubuwa guda hudu da na lissafa.
5. System Configuration
Bayan ka bi dukkan wadannan matakai sai ka lura da cewar har ila yau bata daina dadewa ba wajen tashi, ko dadewa wajen mutuwa, mataki na karshe shine yin amfani da System Configuration Manager.
Shi system configuration manager shike da alhakin tashi da mutuwar na’urarka, shi ke rike da dukkanin programs da suke bukatar su fara tashi a lokacin da ka kunna na’urarka, haka shike da alhakin fara kashe program da na’ura ke amfani da su wajen ta kashe kanta. A wannan wuri, za ka samu hatta sunan da na’ura take nunawa a lokacin da take tashi kamar Windows XP da take nunawa duk a wannan System Configuration Manager ake iya bashi dama. To ka tuna daman matsalar itace rashi tashi akan lokaci.
6. Ya Zan Yi Anfani Da System Configuration Manager?
Shi wannan manager ana iya kiranshi ya bayyana ta hanyoyi da dama, amma kusan amfani da Run wizard shine hanya wacce tafi saukin amfani. Ga wanda yake amfani da Windows Xp, zai sami Run wizard da zarar ya latsa start menu, zai ga Run sai ya latsa bayan ya latsa run dan karamin window zai bude sai ya rubuta msconfig sannan ka latsa Run zai budo maka System Configuration Manager.
Shi kuwa wanda yake amfani da Windows Vista, ko Windows 7 ba zai yi amfani da Run Wizard ba, bayan ya latsa Start Button sai ya rubuta msconfig yana gama rubutawa zai ga komai ya bace a jikin menu sai wannan kalma da ya rubuta sai ya latsa bayan ya latsa System Configuration Manager zai bayyana.
Idan har kaga ka kira System Manager bai zoba, abu biyu zasu iya hanashi, na farko wanda yake da alhakin lura da irin wadannan mahimman program ya hana kowa shiga domin yayi wani canji sai shi kadai kawai, saboda haka da zarar ka kira System Configuration Manager zai fada maka cewa System Administrator ne kadai ke da damar ya bude wannan program. Abu na biyu shine idan aka samu Virus mai karfi ya shiga na’ura wanda idan akayi amfani da System Configuration Manager zai kashe shi, to wadanda su ka kirkiro shi virus din sai su ba shi damar share wannan program tun daga lokacin da wannan virus ya kamu da computer
Wannan shine a takaice hanyoyin da mutum zai bi don dawo da kuzarin na’urar shi.
Don Allah akwai wani virus shoutcut yana damun cumputer ta idan zan cire abu romove sai yaki fita pls mai nene matsala ne
Wanan gaskiya haka yake Allah biyaku