29.8 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

YADDA AKE KIRKIRAR FOLDER DA KUMA AMFANIN TA A COMPUTER

Folder za a iya kiranshi da mazubi da ake tattara ko kuma ajiyar kayan computer waɗanda aka fi sani da ‘data’. Ita folder ta na daga cikin abubuwa masu mahimmanci a cikin computer, domin kusan da ita folder ake shirya dukkanin document na computer a shirya su kamar yadda ka san ake shirya kaya a file na ofis.

Ita folder kamar yadda muka faɗa kamar ma zubi ne, saboda haka, kusan ita kanta Kwamfutar an shisshirya komatsenta ne a cikin foldoji daban-daban. Haka kuma folder ta na iya shiga cikin wata folder, wa ta ma a cikin wata.

Kusan dukkanin application da suke cikin computer duk suna cikin folder ne a shirye. Shi ya sa kake iya ganin kayan computer suna ba ka sha’awa domin sun killace ne. Ɗauki misalin ofis ne babu drawer da za a iya ajiyar takardu, duk takardar da ta shigo wannan ofishin sai dai a ajiye ta a ƙasa, ko’ina takardu sun yi kaca-kaca a ciki. Na san ba sai an faɗama mai karatu ba cewar wannan ofishin komai kyanshi ba kintsattse ba ne. To, da waɗanda suka ƙirƙiri computer ba su yi tsarin folder ba to da wanda zai yi amfani da ita da bai san inda zai fara ba.

A misalin mutumin da yake amfani da computer kuma shi mai ɗaukar hoto ne, to waɗanda su ka ƙirƙiri Operating System sun tsara mashi a kan ya yi amfani da ‘My Picture Folder’ a cikin ita wannan folder zai kuma iya ƙirƙirar wata folder ya kira ta da misalin sunan shi, sannan kuma zai iya ƙirƙirar wata folder a cikin ita folder ya saka ma ta sunan hoton da ya ɗauka a misalin ya kira folder da BIKIN SALLAH, sannan ya zuba waɗannan hotuna a ciki. Yin haka ya tabbatar da cewar duk lokacin da ya zo neman hotunan da ya ɗauka da bikin salla to zai shiga my picture – folder mai sunansa – bikin sallah.

Haka wanda yake son ya zuwa karatu a cikin Kwamfutar shi, kamar yana son ya saka karatun tafsiri na Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi da na Sheikh Abubakar Gumi da na Sheikh Jafar Adam to zai shiga cikin folder ‘my music’ daga nan sai ya ƙirƙiri wata folder ya saka ma ta suna Tafsir daga nan sai ya shiga cikin wannan folder ya ƙara ƙirƙirar wata ya saka mata sunan malamin farko. Misali Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi 2012 bayan ka gama sa ka sunan sai ka buɗe ta ka zuba karatun. To, duk lokacin da kake son ka ɗauko ko ka saurari karatun ɗaya daga cikin waɗancan malaman sai ka shiga my music – tafsir – Sheikh Abubakar Gumi 1982.

Haka rubuce-rubucen da mutane suke yi a cikin computer ko kuma abubuwan da ka ɗauko na karatu a intanet suma haka ake son ka shirya su daki-daki a cikin kowace folder ta na wakiltar document da suke cikin ta.

YAYA AKE ƘIRƘIRAR FOLDER

Ana iya ƙirƙirar folder ta wurare da dama a kuma kowane wuri a cikin computer sai dai yana da kyau duk lokacin da kake son ka ƙirƙiri folder to ka tabbatar wurin ba shi da alaƙa da wurin da ba a son a ajiye wani abu ‘reserve place’. Waɗannan wurare ne da waɗanda su ka yi Operating System ba sa son kowa ya saka wani abu domin saka wani abu a cikin wurin zai iya cin karo da wani tsari da zai hargitsa computer.

Wanda yake son ya ƙirƙiri folder a Desktop zai bi wannan hanyar >> Right Click a jikin sararin Desktop >> New >> Sai ka latsa Folder. Za ka ga ya kawo maka folder amma wurin sunanta ya sa ka ma ka suna ‘New Folder’ nan take sai ka rubuta sunan da kake buƙata, kamar ‘Salisu’s Files’. Sai ka danna ‘Enter Key’ da ke jikin ‘keyboard’ ko kuma ka latsa wani wuri a jikin Desktop ɗinka da ‘left click’.

Wannan shi ne hanyar da ake bi a ƙirƙiri folder a cikin computer kuma da wannan hanyar ce a kowane wuri ka ke son ka yi folder haka za ka yi. Wanda kuma ya yi kuskuren sa ka suna kuma yana son ya gyara sunan, to, zai je kan ita foldar ne ya yi right click a kanta sai ya taɓa rename sai ya gyara sunan sannan ya taɓba wani wuri na daban gafen folder ɗin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img