38.1 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

Ya ya ake shafukan internet suke yin aiki?

Idan ka bude shafi a website a internet na san kana kallon shafuka ne kamar yadda kake ganin rubutu da hotuna a jikin takarda. A mataki na farko bayyanar da shafin internet abu ne mai sauki domin mutum yana kiran shafin da yake so ne ta hanyar amfani da abinda muke kira da browser. Zaka umarci Kwamfutarka ta bayyanar maka da shafi a internet ta hanyar amfani da adireshin da shafin ya ke (URL). Ita kuma browser ta fito maka da shafin a jikin majigin computer. Idan bayanan da kake son ka bude suna cikin Kwamfutarka ne to duk abin da ka kira zai fito da sauri, amma idan bayanan su na cikin wata Kwamfutar ne to za ka ga bayyanar shafin ya dan tsawai kadan.

Akwai abubuwa da dama da shafukan internet suke yi wanda ko kadan shafukan da muka saba gani na takardu da mujallu ba bu yadda za a yi a ce suna yi. A misali babu yadda za ayi kaga an yi rubutu a karkashin rubutun an rubuta cewar sauran maganar ko cikakkiyar maganar za a same ta a shafi na 57, kawai da ka taba hannunka a jikin wannan lamba ta 57 sai shafin ya bude. Babu wannan abu a takardun mu kuma ba kuma a yin tunanin haka zata yiwu a nan gaba. Haka idan ka bude wani form wanda ake son mutum ya cike ya aika da shi zuwa wata ma’aikata, a ce da ya cike shi nan take form din da kansa ya kai kansa wannan ma’aikata ba tare wani bata lokaci ba. Haka na san ba mu taba ganin hotuna suna motsi ba a cikin littafi ko kuma muji magana tana fitowa daga cikin littafi. Amma duk wannan abubuwan da na lissafa da ma wadanda suka fisu ana samunsu a jikin shafukan internet.

Amma akwai banbanci tsakanin mai nisa tsakanin shafukan internet da kuma shafukan takarda. Domin akwai abubuwa da dama da muke ganin su a shafukan intenet wanda a zahiri muke ganin su amma a badini ba haka suke ba. A misali ba kamar yadda duk abin da ka gani a cikin shafin takarda ba yana cikin wannan shafin ne, da hotuna da rubuce rubucen da suke cikin shafi duk a shafin ya ke. To, shafukan internet ba haka suke ba, domin akwai abubuwan da yake faruwa a bayan shafukan (backend) wanda kai wanda ka bude shafin ba ka sani, sannan kuma ba komai bane za ka ganshi a jikin shafin da ka bude ka yi tsammanin yana cikin shafin ne gaba daya. A misali zai iya yuwuwa ka kira shafi wanda asalin shafin yana cikin wata kwamfuta ne a kasar Amurka, hotunan da suke cikin shafin kuma ya kasance suna cikin wata kwamfuka ne da take kasar Jamus, sannan kuma sautin da muke ji yana kasar Brasil, sannan kuma majigin da muke gani ya kasance yana kasar Saudi ne.

Aikin da browser suke yi ya wuce su bayyanar mana da rubutu da hotuna da sauti da muke ji ko gani a jikin talabijin na Kwamfutocin mu ko kuma Wayoyinmu. Wadannan browser suna yin wadansu ayyuka da suka wuce hankali ga wanda bai san abin da ke faruwa a bayan shafi ba (backend). Domin su browser su suke da alhakin lura da sharudda da dokoki da wanda ya tsara shafin ya ce haka yake son su bayyana, da kuma abin da ya ke son masu shiga shafin su gani. Irin wadannan sharudda da dokoki su ne wanda su browser kowace iri ce ta ke lura da su. Su kuwa irin wadannan dokoki wani ilimi ne na musamman da ake koyanshi kuma ake rubuta shi domin ita browser ta iya karanta shi. Shi wannan ilimi da browser take iya karantawa ana kiran shi HTML wato HyperText Markup Language.

To a nan zamu iya cewar browser wani program ne na Computer wanda ya ke iya fassara rubutun da aka yi da dokokin na HTML.

Wadannan Browser da ake da su suna da yawa amma kuma wadanda suka fi shahara a wannan lokaci wanda kusan kowa yana amfani da su sune, Opera, Opera mini, Google Chrome, Internet Explorer, Mozilla Firefox da kuma UC Browser. Akwai daruruwan brower amma wadannan sune wadanda suka fi shahara. To, dukkanin wadannan program aikin su shine su fassarawa computer dokoki da ka’idojin da wanda ya tsara shafin ya ke son mutane su gani.

Kamar yadda mai karanta wannan mukalar yake gani (idan amujalla kake karantawa) yana ganin akwai wadansu rubutu wadanda suke an dan kaurarasu, wasu kuma na lankwasa su, wasu kuma sun fi wasu girma, duk wadannan abubuwan da muke gani a takarda idan an yi amfani da MS Word ne aka yi su, bai wuce a ce an saka bold ko italic ba. Amma a wajen yin tsara shafukan internet ba haka abin ya ke ba, domin su ba italic ko bold ba ne wasu surkulle na daban ake yi.

Shi wannan ilimin sanin yadda ake shirya shafin internet (web design) ilimi ne mai zaman kansa wanda ake koyar da shi a matakai daban-daban da kuma matsayi bayan matsayi. Wanda kowane daya daga cikin wadannan matakai ana son mai karatu ya san shi sosai kafin ya tsallaka zuwa wani bangare.

Ga duk wanda ya ke son ya ga ya wannan ilimi ya ke da kuma wane irin kokarin masu shirya shafukan da kake budewa a cikin internet suke yi, za ka iya bude kowane irin shafi a internet sannan ka yi right click sannan zaka ga view source sai ka zabe shi, zai bude maka wani shafi da zai baka bayan shafin abin da ke faruwa a shafukan internet.

Wasu shafukan an gina su da babban ilimi shirya shafuka saboda haka ba komai mutum zai gani ba a wancan shafin da ya dube, domin akwai ilmomi da dama da ake daurawa a lokacin da ake bude shafukan internet wadanda suke taimakawa shi HTML wajen inganta aikin gina shafukan.

Akwai ilimi da dama wadanda suke taimakawa wannan ilimi na HTML domin yaukaka shafin wadanda suke hada XHTML, XML, JAVA Script, PHP, ASP, ASP.Net da ColdFusion. Irin wadannan ilimin suna da yawa amma kuma wadannan su suka fi shahara.

Kodayake kowace browser tana da irin yadda take ganin abubuwan da suke kunshe na dokoki da kuma ka’idojin rubutun shafukan internet. Shi yasa idan mutum ya koyi ilimin yadda ake shirya shafukan internet to ya na da kyau duk lokacin da yazo zai gwada shafukan ya gwada su a kalla a browser kala hudu wadanda suka hada da Internet Explorer, da Mozilla Firefox, da Google Chrome, da kuma Safari.

Da rasi na gaba da yardar Allah za mu fadi hanyoyi da kuma matakai da ake bi domin a shirya shafukan internet.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img