Ya kamata da farko ka gane cewa shi booting na computer abu biyu ke kawo shi na farko idan computer ta kamu da virus da yake taba boot sector nata za ta iya fuskantar wannan matsala, ko kuma ita computer ta gane cewar akwai wani matsala da operating system ko kuma da wani hardware to shi ma zai rinka sa hakan ta faru. Misali idan processor na computer yana yin zafi ko kuma iskar da ke shigarshi bata ishe shi ba zai rinka re-starting, haka idan ya zamanto computer bata da isasshen RAM koma ka loda mata program masu nauyi kuma ka budesu kana aiki da su to su ma za su iya kawo wannan matsala