Rubutawa: Tukur Kwaironga
Dukkanin wani abu da ya kasance ƙarami ba shi da wahalar a ce an ɗauke shi ko kuma ya faɗi. Ƙananan wayoyi na hannu suna da daɗin sha’ani da kuma sauƙin amfani, wasu suna da sauƙi ko arha a wajen siya, wasu kam ɗan karan tsada ke gare su, wanda ya zamanto sai ka jajirce ka daure za ka iya sayensu.
Mafi yawancin masu riƙe da wayoyin hannu suna ƙoƙarin kaffa-kaffa da su saboda masu farautarsu. Da wannan dalili ne ya sanya muka zaƙulo muku waɗannan hanyoyi guda biyar (5) da za su taimaka wa wanda yake da waya mai tsarin Android idan ta ɓace ko an ɗauke ya iya gano inda take.
1. Contact Owner: (https://sites.google.com/site/paranoidandroidproject/ContactOwner) wannan wani ɗan karamin application da ake samun shi a Android Market wanda yake taimaka maka wajen rubuta bayanai game da kanka wanda idan mutum ya tsinci wayarka zai ga cikakken sunanka da adireshinka, wanda hakan zai taimaka wajen neman ka idan wayan ta faɗa hannun nagari ne. Hanyar da ake amfani da wannan ɗan application hanya ce mai sauƙi wacce da zarar ka saukar da shi wannan application a cike shi ne sau ɗaya, za ka iya yin amfani da bayanai naka da ke cikin wayarka, ko kuma ka rubuta su kai tsaye. To, duk sadda ita wayar taka ta je dan hutu zata kulle kanta sai waɗannan bayanai da ka saka su bayyana a jikin fuskarta.
2. Wheres My Droid. (https://market.android.com/details?id=com.alienmanfc6.wheresmyandroidwannan ) Wannan application yana da matuƙar amfani wanda shi ma zai taimaka maka wajen gano inda wayarka ta hanyar amfani da “GPS”. Shi wannan application yana iya baka dama ka kunna Ringtone ɗin wayarka ko kuma ka kashe Ringtone ta hanyar aikawa da Text Message daga wata wayar, kuma idan wayar ɗauke ta aka yi wannan application zai taimaka maka wajen hana barawon yin waɗansu muhimman canje-canjen.
3. Anti-Virus Software: za ka iya yin amfani da waɗansu shahararrun Anti-Virus software domin gano inda wajen inda wayarka take. Misali AVG Anti-Virus na waya idan ka saka shi a cikin wayar yana zuwa da dan wani karamin application mai suna Lost-Phone-Tracking. Idan ka saka Anti-Virus na AVG sannan ka yi “configuration” na shi wannan application nasu, su kamfanin za su taimaka maka wajen kulle wayar taka sannan ka iya gano wayar ta hanyar amfani da google map. Sannan akwai wani application mai suna Lookout Security & Antivirus shi ma kusan yana irin wannan aiki wanda suke iya baka damar idan waya ta ɓace ka iya gano ta ta hanyar Internet.
4. Kamfanonin SIM: wasu daga cikin kamfanonin da suke bada service na waya kamar T-Mobile, da irin su Verizon dukkansu suna da application na musamman da suka yi domin gano wurin da wayarka take idan ta ɗace.
Plan B: To idan duk waɗannan hanyoyi guda huɗu sun ki yin aiki, to, ga wata sabuwar hanya mai suna “Plan B” wanda ko da baka samu damar saka wani application da ke bada damar gano wayar ka ba, to wannan application ɗin zai iya gano maka wayarka ta hanyar turo maka da saƙon SMS da kuma taswirar wurin da wayar take zuwa ga akwatin gmail naka.