Rubutawa: Salaha Wada Wali
Ma’aikatar lura da tsaron lafiyar wayoyin hannu game da abin da ya shafi Virus na waya mai suna Lookout (https://www.mylookout.com/download)su ne suka ƙirƙiri wani application na Android suka kuma sake shi kyauta wanda ake kiran shi da suna Plan B.
Plan B application da aka yi shi musamman domin wayoyin zamani masu tsarin Android, wanda wannan application yake taimaka wa matuƙa wajen gano inda wayar take a lokacin da ta ɓace ko kuma aka sa ce ta.
Yadda ake amfani da wannan application shi ne lokacin da ka nemi wayarka ta Android ka rasa, kuma ka tabbatar da cewar ta ɓace, ko kuma kana da yaƙinin cewar sa ce ta aka yi, sai ka shiga Internet ka yi downloading ɗin wannan software sannan ka yi installing ɗin shi a kan internet ɗin. Amma kafin ka saka shi wannan application a wayar taka da ta ɓace kana buƙatar ka shiga shafuka na Android Market ta hanyar amfani da email na google (gmail). Da zarar shi application din ya gama downloading a cikin wannan shin na Android Market zai yi ƙoƙarin binciken inda wannan wayar take ta hanyar aiko da saƙon email zuwa wannan akwatin da ka shike wannan shafi da shi (gmail), bayan wasu ‘yan lokuta kuma zai ci gaba da aiko maka da hotunan taswirar wurin da wayar ake amfani da ita a halin yanzu. Haka zai ci gaba a duk tsawon mintina goma.
Idan kuwa bayan mintina goma baka saƙon email cikin akwatin k aba, to sai ka aikawa kanka saƙon SMS zuwa wayar taka da kalmar “locate”, yin ha kan zai baiwa shi wannan application damar ya fara aiki kai tsaye. Shi kanshi Plan B yak an aika da saƙon SMS zuwa ga wayar ka ta hanyar neman ta “GPS” ko da kuwa ba a kunna GPS din wayar ba.
Kodayake shi wannan application a lokacin da muke tattara wannan bayanai ‘yan aiki ne kawai a ƙasar Amurka ga masu amfani da AT&T da masu amfani da Sprint, da kuma masu amfani da Verizon da kuma masu amfani da T-Mobile. Sannan shi wannan application na Plan B baya aiki sai a kan Android 2.0, haka kuma ba zai yi aiki ba idan an kashe waya, ko kuma an cire SIM ko kuma wurin da babu network.
Yadda ake yin amfani da Plan B a takaice
1) Ka shiga shafi na Android Market da Gmail account.
2) Ka rubuta Plan B a wurin bincike, ko kuma ka shiga shafin Plan B Market
3) Ka yi installing Plan B a wayar da kake son ka gano ta ta internet (wato zai fito maka da jikin wayar ta internet sai ka saka wayarka a ciki).
4) Da zarar ka gama installation ɗin shi zai aiko da saƙon email cikin akwatinka na gmail yana faɗa maka wurin da za ka samu wayarka.
5) Da zarar Plan B ya gano wayar taka, sai ka sake duba cikin akwatinka za ka ga ya turo maka da taswirar wurin da wayar taka take ta amfani da Google Map yana kuma nuna maka daidai wurin da wayar take. Haka zai ta aikawa bayan minti goma goma.
6) Idan bayan minti goma da downloading baka iya samun bayanan inda wayar take ba, sai ka aika da saƙon SMS a wata waya zuwa ga wayar taka ka rubuta “locate”.
7) Bayan ka gano wayar taka yana da kyau ka yi downloading cikakken application ɗin Lookout Mobile Security, domin samun ingantaccen tsaro.
Dan Allah yazanyi nasamu wannan app na plan b