38.2 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

Mene ne Modem yaya kuma ake amfani da shi?

Modem dai kamar yadda muka sani wani ɗan ƙaramn device da ake amfani da shi wajen haɗa computer da internet, da farko dai modem kala biyu suka fi shahara a Najeriya akwai Huawei da ZTE duk waɗannan modem ɗin ana kiransu da ‘plug and play’, wato da zarar ka saka su a cikin computer za su yi installing kansu, kuma su fara aiki kamar yadda aka tsara.

Modem waɗanda ake da su basa buƙata a ce mutum ya kasance ƙwararre ne kafin ya san yadda zai sarrafa su. Da zarar ka soka shi a jikin USB port, idan baka taɓa saka shi a cikin computer ba, zai yi ƙoƙarin ya fahimtar da ita computer cewar ni ne wane, ga kuma irin aikin da nake yi, daga bisani zai fito maka da wani ɗan ƙaramin window da zai tambaye ka me kake son ka yi da shi modem, nan take sai ka zaɓi Installation (wato zan saka shi ne ne).

Wani abu da ake kira Installation Wizard zai fito shi wannan wizard shi ne ke sauƙaƙa wa mutum wurin sanya kowane irin application a cikin computer zai riƙa yi maka waɗansu ‘yan tambayoyi kai kuma kana ba shi amsa ta wurin yin amfani da latsa maɓallin da yake cewa NEXT.

Idan ya gama shigar da application ɗin, zai sake fito maka da wannan ɗan ƙaramin windows irin na farko sai ka sake latsa wannan installation, wannan karan ba zai yi installation ba ne zai buɗe maka program ɗin ne. To, daga wannan wuri ne kake buƙatar yadda za ka fara browsing da shi wannan modem ɗin.

Mataki na farko shi ne ka sani cewar kowane modem da ka saya yana zuwa da tsarin kamfanin la yin shi ne, misali MTN modem yana zuwa da configuration na MTN ne kawai, sannan shi modem ɗin la yin MTN kawai zai yi aiki da shi, haka ma sauran modem. Kodayake ana yin amfani da wani application na musamman da yake iya lalata asalin tsarin da kamfanonin modem suka ƙaga na cewar la yi ɗaya kawai zai yi amfani ya ko ma yana amfani da kowane irin la yi, ma’ana idan ka yi craking ɗin, shi modem ɗin to zai ko ma universal moden wanda duk la yin da aka sa mishi zai yi aiki.

Abu na biyu, shi ne dole ka saka wa wannan modem kuɗi daidai da ƙarfin ka, domin cimma wannan nasara za ka latsa inda ka ga an saka Data Plan sai ka zaɓi plan ɗin da ka ga ya yi maka kuma nawa za ka saka a cikin wannan plan ɗin idan N500 ko N8000, to sai ka buɗe wurin da ka ga an saka alamar kuɗi (Naira Sign) sai ka sayo kati ka rubuta pin ɗin kawai ban da code ɗin wato idan Airtel ne ba sai ka saka *126* ba, za ka saka pin ɗin ne kawai.

Bayan da ka tabbatar da kuɗin ya shiga sai ka ko ma wajen plan ɗin sai ka latsa maɓallin da ke jikin plan ɗin da kake son saya, daga ƙarshe ka jira saƙon da ke tabbatar maka da cewar sun cire wannan kuɗi, kafin ka haɗa (Connecting) domin idan ba su aiko da saƙon sun cire kuɗi ba kuma ka yi connecting to cikin minti 3 ko da N8000 ka saka internet zata lashe su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img