38.1 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

Bill Gates ya sha ruwan ba-haya

Mai Kamfanin Microsoft Bill Gates, ya sha wani ruwa da aka sarrafa da wata na’ura wanda kuma asalin sa daga ba-haya aka samo shi.

A cewar Gates, wanda ya nuna amincewar sa da na’urar da ta sarrafa ba-hayan zuwa tsabtacaccen ruwan sha, fasahar za ta iya taimakawa wajen samar da ruwan sha ga kasashe masu tasowa.

Haka itama kungiyar nan mai suna WaterAid dake fafutukar ganin an samar da tsabtacaccen ruwan sha a duniya, ta ce ta amince da wannan kimiyya.

A cewar kungiyar, akalla mutane miliyan 748 a duniya ba su da hanyar samun tsabtaceccen ruwan sha.

A wani hoton bidiyo da ya sa a shafinsa na intanet, Gates ya shaida lokacin da aka zuba ba-hayan a na’urar ta kuma sarrafa shi ya koma tsabtataccen ruwan sha.

“Ruwan ya na da dandanon da kowane irin ruwan sha yake da shi, kuma bayan da na yi nazarin irin fasahar da aka yi amfani da ita wajen sarrafa ruwan, zan dinga shan ruwan kullum.” Gates ya rubuta a shafin na sa.

Har ila yau a hoton bidiyon, wanda ya kera na’urar, Peter Janicki, ya ce da farko nau’rar tana kona ba-yahan ne, sannan sai ta tace ruwan dake jiki daga gudajin ba-hayan.

Ya kara da cewa daga nan ne kuma sai nau’rar ta kona ruwan ta yadda zai koma tsabtacacce ruwan sha.

Gates ya kara da cewa idan aka samar da hanyoyin kawar da ba-haya, za a iya kaucewa cututtuka da dama da ke hana yara kanana girma.

Daga BBCHAUSA.COM

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img