38.2 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

Wayar Galaxy Note 7 ta Kamfanin Samsung Bala’i ce ga masu ita

Hukumomi a kasar Amurka suna kira ga jama’ar da suka siya sabuwar wayar Galaxy Note 7 wacce bata jima da shigowa kasuwa ba da su sauri su kashe ta domin batirin wayar yana kamawa da wuta.

Hakan ya biyo bayan bincike da wata hukuma da ke kasar Amurkan tayi wacce take kula da hajjin kare masu mu’amala da kayan na’ura suka fitar da jiya Juma’a 8/09/2016. In da suka ce batirin wayar yana da hatsari matuka kuma zai iya fashewa a duk lokacin da ake amfani da wayar.

Wannan dalilin ne ya sanya hukumar kula da zirga-zirgar jiragen saman Amurka ta haramta wa fasinjoji amfani da wannan wayar acikin jirgin sama

Suma a nasu kamfanin Samsung tun a wancan satin da ya gabata kamfanin ya fara kira da a dawo da irin wadannan wayoyi wanda suka shiga kasuwa kusan miliyan biyu.

A yanzu haka kasar Indiya tana daya daga cikin jerin kasashen da yanzu aka hana amfani da wannan wayar saboda wannan matsala. Saura ga jama’a daidai ku da suke da irin wannan wayar da su bi wannan umarni domin kare lafiyar su da ta wadanda suke kusa da su.

Fashewar waya ko kama wuta ba bakon abu bane ga kayan wutan lantarki musamman irin wayoyin-komai-da-ruwanki (Smartphones) idan kunne ya ji ya yi aiki jiki ya tsira.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img