38.2 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

NAN GABA NOMA DA KIWO ZA SU GAGARI TALAKA

Rubutawa: Sadiq Ibrahim Dasin

Ina nufin haka zai kasance nan gaba. Sabida na lura cewa duk abinda dan Adam ya dauka for granted, sannu a hankali, or a kwana a tashi, abin zai zo yafi karfin sa.

Alan misali ba zani taba mantawa ba lokacin da nike makarantar sekandare a Aliyu Mustapha College, Yola zamanin Shugaba Shehu Shagari ana raba form na allocation na gidaje a Shagari low cost Housing Estate a Yola, keuta. Mutane da yawa suka ki karba akan cewa wai su baza su zauna a daji ba. Today Shagari low cost yafi karfin talaka.

Again I can still remember lokacin da aka kawo aikin traffic wardens. Mutane da yawa suka ce su baza su shiga aikin ‘Yellow Fever’ ba. Today, Yellow fever are also policemen. Shiga police kuma yafi karfin dan talaka.

Coming home to the two burning issues in our country today, maganar noma da kiwo, su ma nan gaba wallahi talaka bai isa yayi su ba. Mark my words as they will come to pass.

Yanzu batun noman nan, in many of our cities and towns noma yafi karfin talaka. Dole sei mai kudi ya keyin noma a birni da manyan garuruwa. Ba kuma wai talakan da ke birni ko babban gari baya so yayi noman ba ne fa, a a abin yafi karfin sa ne.

Na farko sabida yawan jama’a gonakin dake kusa da gari sun zama gidaje. In Yola, Jimeta, Mubi, Ganye, Song, Numan, Fufore for instance, the nearest gona inda filin noman ke da inganci, sei kayi tafiyar da zai kai a kalla kilomita goma kafin ka isa gonar. Koma fiye da haka. Now that can not be done on foot.

You have to have a motor cycle and a motor cycle now cost over N200,000/ . Even if you have the money, how do you get the fertilisers to apply.

Bugu da kari, a yanzu dei kam baka isa ka tirsasa ‘ya’yanka su dauki fartanya su duka suyi maka noma ba. A birni kam bazai yiwu ba. A kauye ma rike fartanya a duka a yi noma ya kusa zama yawa.

Batun kiwo ma nan gaba wallahi zai fi karfin talaka. Rike garken shanu a yanzu haka ba aikin talaka ba ne whether he is Fulani or not. For instance in the whole of garin Fufore, we only found one boy that is indigenous to Fufore that is a herder. I know now that all the cattle in Fufore are herded by Fulani herdsmen who have no cattle of their own.

Kada mu manta fa, fadin kasa ba karuwa ya ke
yi ba. Hakama filin kiwo ba karuwa zai yi ba. Mutane kuwa sei karuwa suke yi a kullum kwanan duniya. Don haka za a wayi gari kasar da za a raka saniya taje tayi kiwo ta dawo wallahi ba za a sameta ba. Don haka zaizo ya kasance sei mai kudi zai iya rike saniya.

A yanzu dei, in kai Bafulatanin gida ne, ko a kauye kake yaron da ka haifa ba zai je kiwon shanu ba sei dan Fulanin daji. Kada kowa ya dauka cewa Fulanin dajin nan zasu ci gaba da zama a dajin ko ace sun dinga bin shanu har abada ke nan. Kuma in kun lura, duk talakan da yaci gadon saniya sayar ta ya keyi sabida wahalar rike saniya tafi karfin sa. In ko dan boko ne, ko dan kasuwa, sei ‘yan uwansa su cinye shanun ko barayi su sace su.

Don haka ayi hattara. Noma da kiwo abubuwan da talaka ke dogaro a kayin su, suma zasu zo su gagari talakan.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img