38.1 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

RASHIN TASHIN COMPUTER DA SAURI DA HANYOYIN MAGANCEWA

Rubutawa: Bashir Bature

Abubuwa da dama za su iya haifar da wadannan matsaloli a jikin Computer, tun daga rashin fara aiki a kan lokaci, kin baka damar bude wani program da dai makamantansu.

Da farko dai ya kamata ka sani cewa ita computer tana da zubi irin na mutum, kamar yadda ka sani mutum na iya kamuwa da ciwo, tun daga zazzabi, mura, ciwon kai da dai makamantansu, to ita ma Computer tana iya kamuwa da kusan irin wadannan matsaloli, Na san mai karatu zai ce wani sabon salo, me ke kawo a gane cewar mutum ya kamu da ciwo iri kaza,Duk  lokacin da aka ji ya fiye korafi a kan wani bangare na jikin shi, to, ai ita ma na’ura ana gane haka ne idan ka ga  ta canza daga yadda ka saba ganin ta.

Kamar yadda na fadi cewar ita computer kamar mutum ce, tana iya kamuwa da wadansu matsaloli, wannan gaskiya ne, amma abu na farko da ya kamata shi ne ka gane wace matsala ita wannan na’ura ta kamu da shi kafin ka san hanyar magance shi.

Ba dole ka gane matsala nan take ba

Ba za ka iya gane cewar computer tana cikin wani matsala ba, matukar ba taka ba ce, abin da nake nufi idan ka ari computer wani, kana kuma son ka yi amfani da ita zai iya yiwuwa ka ga ba ta aiki da sauri. Wannan kuwa ba hujja ba ce na cewa wannan na’ura tana da matsala, shi ya sa take da wuyar budewa. Domin ya yiwu ita na’urar ba ta kai karfin wacce ka saba aiki da ita ba, ko kuma computer daka aro tsohuwa ce, ko kuma sabuwa ce amma RAM da ke jikin waccan wacce ka saba aiki da ita yafi na wannan girma, to, ka ga ai dukkan wadannan ba matsala ba ce ga computer, ba wani abu ya faru da ita ba balle a ce ta lalace.

To ka ga idan da irin wadannan matsaloline zai yi matukar wahala a matsayinka na wanda ya ari computer ya gane cewar tana da matsala. Duk da cewar dukkanin na’urar da aka kunna ta, har ta kai tsawon mintoci kamar 4 zuwa 10 ba ta gama tashi ba to lallai akwai matsala.

Sai ka lura da kyau kafin ka gano matsalar

Kana iya gane computer ta sami matsala idan takace, kaine wanda ya sayeta da farko ko kuma kana amfani da ita a baya lafiya lau amma yanzu sai ta zamanto tana dan yin wandansu abubuwa da ba su kamata ba. Misali a lokacin da take sabuwa da zarar ka kunnata cikin dan kankanin lokaci sai ta tashi ta fara aiki, amma yanzu sai ka gaji da jira kafin ta baka damar fara aiki, ko kuma idan ka zo za ka kashe ta maimakon ta mutu da wuri sai ta dauki tsawon lokaci ba ta mutu ba.

Kodayake idan mutum yana hade da Internet, kuma bai rufe Window Update ba, to, Kwamfutarsa za ta shiga  Microsoft ta duba ta ga wani sabon tsari da aka kara ta dauko ta kara maka a cikin na’urar ka, to idan haka ya faru to na’urar da kanta za ta gaya maka cewar ta dauko sababbin tsari daga Windows Update kuma tana bukatar ta ajiye ko wannan file a wurin da ya dace da shi, har ma za ta fada maka yawan abubuwan da ta dauko misali 1 of 45 ma’ana ta dauko abubuwa guda 45 ta kuma sa daya. Haka idan ka daura wani sabon program wanda ya zama ya zo da sababbin tsare-tsare to shi ma wani lokaci zai dade kafin computer  ta mutu.

Rashin kula ke kawo matsala a computer

Sau tari na’ura ba wani babban matsala take kamuwa da ita ba, ka ga mutum ya shiga cikin dimuwa da kuma damuwa, wani lokaci ma, rashin lura da wadansu kananan abubuwa shi ke iya kawo wannan matsalolin, wani lokaci rashin yi wa ita na’urar garanbawul, ko yawan amfani da manya-manyan programs ana’urar da ba za ta iya daukarsu ba, ko kuma sauko da kananan program na kyauta daga internet, ko kuma sa games ana’ura ko wani iri, ko kuma amfani da program wanda ba shi da lacici na asali sai dai abin da ake cewa crack, ko kuma Virus ya kamata. To, dukkan wadannan abubuwa da na ambata suna iya kawo matsalolin tashi da mutuwar na’ura.

Hanyoyin magance su

1. Virus Scanning

Duk lokacin da ka gano cewa yadda na’urarka take tashi ko mutuwa ba haka ta saba yi ba, to daya daga cikin wadannan matsaloli ne, abu na farko da za ka yi shi ne ka tabbatar kana amfani da Anti-Virus wanda yake da cikakken tsaro, ko da kuwa na kyautane, domin akwai Anti-Virus na kyauta wadanda idan har kana updating din su, to, lallai Virus ba zai iya kama na’urarka ba. To, idan kana da Anti-Virus kuma ka yi updating dinshi to sai ka yi scanning na’urar gaba dayanta ka tabbatar babu wani virus a ciki, kodayake wadansu Virus karfinsu ya kai Anti-Virus karami ya kasa gane su, akwai cikakken bayani  a kan Virus da yadda yake aiki.

2. Disk Cleanup

Bayan ka yi scanning ka tabbatar da ba virus ba ne suke hana na’urar tashi ba, so sai ka yi amfani da wadansu utility programs da suke cikin na’urarka ka duba lafiyar hard disk dinka kamar haka:

Alama (=>) idan ka ga wannan alama tana nufin ka latsa kalmar da ke gabanshi.

=> Start Menu => All Programs => Accessories => System Tools =>Disk Cleanup

Wannan program na Disk Cleanup yana cikin kowace na’ura kuma binda yake yi shi ne ya taimaka ya share maka dukkan abin da ya saura ko kuma burbushin file da ya kamata ba sa cikin na’ura amma wani dalili ya sa ba su fita ba. Haka shi ma Memory wani sa’ilin yakan bar irin wadannan burbushin file a cikin shi to wannan dan karamin program zai taimaka wajen share dukkan wadansu kazanta ko bola da suka rage.

3. Disk Defragmenting

Idan ka goge dukkan wadannan file sai ka koma ka duba lafiyar zaman kowane document da ke cikin na’urar musamman idan kana amfani da manya-manyan files kamar audio da video da aiki irin na graphics, duk sa’adda ka cire su ko ka goge su a jikin na’urar to na’urar tana barin gurbin babu komai a wurin ita kuma na’urar sai ta rinka ganin kamar akwai wannan babban file a wajen to, idan kuwa aka yi rashin sa’a a kan haka za ta rinka dan dadewa wajen tashi. Ga yadda za ka yi ka magance wannan matsala

=> Start Menu => All Programs => Accessories => System Tools =>Disk Defragmenter

Shi wannan program na Disk Defragmenter yana taimaka wa wajen daidaita sahun dukkanin file zuwa mazauninsu da ya kamace su, kamar yadda na fada a baya cewa idan ka share document na na’ura file din ke bacewa amma gurbinshi baya bacewa shi wannan program ke taimaka wa wajen haka.

4. Check Disk

Hanya ta gaba ita kuma za ta duba maka matsalar hard disk dinka ne, ta ga cewa dukkan kafa da file ko document ko program kai kuma meye da ke jikin na’ura suna nan lafiya babu matsala a jikin su, domin rashin bin ka’ida wajen kulle na’ura ko kashe ta kamar yadda ya kamata ka iya jawo matsalar hard disk ya sami rauni, idan raunukan da hard disk ya yi yawa za ka ji wani lokaci yana kara kamar kat-kat-kat, wannan kuma yana nuna maka alamar cewa nan gaba kadan za ka iya rasa dukkanin program da suke cikin na’urarka. Sau tari mutane sukan yi watsi da sakonni da na’ura ke fitowa da su a lokacin da aka dauke wutar lantarki kuma baka da UPS, za ka ga ta gaya maka cewar wannan na’ura ba a kashe ta ba kamar yadda ya kamata, saboda haka za ta binciki babbar kwakwalwar ajiya domin gyara wata matsala da daukewar na’urar zai iya haifarwa, saboda rashin sanin muhimmancin wannan sako sai ka ga mutane suna wucewa tun da  dama biyu take bayarwa, ko dai ka tsaya ta yi wannan bincike, ko kuma ta taba ESC a jikin na’urarka ta manta da wannan sako. Sai ka ga mutane suna daukar dama ta biyu.

Da zarar mutum ya hada wadannan matakai guda hudu, binciken virus (Virus Scanning), share datti ko bolar computer (Disk Cleanup), daidaita mazaunin file da document (Disk Defragmenting) sannan ka duba lafiyar babban hard disk (Check Disk) to babu shakka computer za ta kara kuzari. Kodayake ga wanda ya zamanto shi bakon amfani da na’ura ko kuma yana amfani da ita domin dan karamin aiki, ko kuma bai yi zurfi a kanta ba, amfani da irin wadannan kananan program zai iya ba shi wahala duk da cewar ba su da wani wahalar bi. Kodayake akwai wasu program na musamman wadanda aka kirkiresu domin su magance irin wadannan matsaloli wanda latsa daya za ka yi duk ya yi wadannan abubuwa guda hudu da na lissafa.

5. System Configuration

Bayan ka bi dukkan wadannan matakai sai ka lura da cewar har ila yau bata daina dadewa ba wajen tashi, ko dadewa wajen mutuwa, mataki na karshe shi ne yin amfani da System Configuration Manager.

Shi system configuration manager shi ke da alhakin tashi da mutuwar na’urarka, shi ke rike da dukkanin programs da suke bukatar su fara tashi a lokacin da ka kunna na’urarka, haka shike da alhakin fara kashe program da na’ura ke amfani da su wajen ta kashe kanta. A wannan wuri, za ka sami hatta sunan da na’ura take nunawa a lokacin da take tashi kamar Windows XP da take nunawa duk a wannan System Configuration Manager ake iya bashi dama. To ka tuna damar matsalar itace rashi tashi a kan lokaci.

6. Ya Zan Yi Amfani Da System Configuration Manager?

Shi wannan manager ana iya kiran shi ya bayyana ta hanyoyi da dama, amma kusan amfani da Run wizard shi ne hanya wacce tafi saukin amfani. Ga wanda yake amfani da Windows Xp, zai sami Run wizard da zarar ya latsa start menu, zai ga Run sai ya latsa bayan ya latsa run dan karamin window zai bude sai ya rubuta msconfig sannan ka latsa Run zai budo maka System Configuration Manager.

Shi kuwa wanda yake amfani da Windows Vista, ko Windows 7 ba zai yi amfani da Run Wizard ba, bayan ya latsa Start Button sai ya rubuta msconfig yana gama rubutawa zai ga komai ya ba ce a jikin menu sai wannan kalma da ya rubuta sai ya latsa, bayan ya latsa System Configuration Manager zai bayyana.

Idan har ka ga ka kira System Manager bai zoba, abu biyu za su iya hana shi, na farko wanda yake da alhakin lura da irin wadannan muhimman program ya hana kowa shiga domin ya yi wani canji sai shi kadai kawai, saboda haka da zarar ka kira System Configuration Manager zai fada maka cewa System Administrator ne kadai ke da damar ya bude wannan program. Abu na biyu shi ne idan aka samu Virus mai karfi ya shiga na’ura wanda idan aka yi amfani da System Configuration Manager zai kashe shi, to wadanda suka kirkiro shi virus din sai su ba shi damar share wannan program tun daga lokacin da wannan virus ya kamu da computer

Wannan shi ne a takaice hanyoyin da mutum zai bi don dawo da kuzarin na’urar shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img