32.4 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

Duniyar Computer barka da dawowa – Abubuwan da suka kubucewa masu karatu daga shekarar 2020 – 2025

Jama’ar masu albarka,

Da farko dai, zuciyar ta karkadu da raurawa kamar yadda idan mutum na karkashin gini mai dakin karkashin kasa kuma yake neman network yake shan wahala, haka muma muka bace a daidai lokacin da ake neman mu. Wancan lokacin an shiga cikin rudun Covid-19 wanda ya firgita duniya da batar da abubuwa masu yawa muma, hakan ya sanya muka bace kamar an aiki bawa garin su. In Sha Allah mun dawo kuma da karfin mu da izinin Allah, kuma zamu tattauna da ku mu fada muku abubuwa masu muhimmanci da suka faru a harkar ICT a cikin wadannan shekaru 6 da muka yi bacci.

Ku daura dammara da zake damtse, domin ba wai kaiwa kanun abubuwan da suka faru zamu bayyana muku ba, magana ake ta fahimtar da ku wadannan abubuwa da kuma shigar da ku kuma a dama da ku a cikin wadannan abubuwan da zamu tattauna.

Dole mu baku hakuri!

Bayan kasancewar mu daya daga cikin shafuka da mutane suke dogara da shi a abinda ya shafi harkokin ICT a wannan nahiyar tamu, ko ma mu ce Duniyar Hausawa gaba daya, shafukanmu, tun daga Website dinmu da Facebook da Twitter da Instagram har ma da Mujallar mu sun bace tun a farkon 2020. Kamar yadda duniya ta kadu da maganar COVID-19, wanda ya boye kowa, amma wannan baya daga cikin dalilin da zai sa Duniyar Computer ta bace, kasancewar mafi yawan aikace-aikacen da muke yi daman na Computer ne. Muna fatan za a yi mana afuwa na rashin jin mu, kuma muna fatan wannan rubutu da zamu yi ya warkar da ciwon da muka jiwa kowa na rashin jinmu baki daya.

Zamu dauki kowace shekara domin mu yi wa masu karatu bayanin abubuwa masu muhimmanci da suka faru da kuma cigaba da aka samu a harkar Kimiyya da Fasahar kere-kere da makamantan su.

Ka kalli yadda a farkon shekarar 2020, hanyoyi da tituna suka zama shiru, ajujuwan karatu ba dalibai, an rufe ofisoshi saboda kwayar cutar Corona da yadu a bayan kasa. Amma a cikin wannan shirun da ya faru, wadansu cigaba da ba a taba tunani zai zo ba yazo cikin kankanin lokaci, da kuma kara samun budewar idanuwa a harkar ICT wanda, a wani lokaci a shekarun baya sai an dauki a kalla shekara 10 ko 100 kafin a same su.

Yanzu bari mu dau hanya domin fara wannan tafiyar mai albarka. Tafiya ce kan hanyar abububuwan da bamu yi bayanin su ba a wadannan shekarun ta hanya da zaka dawo cikin hayyacinka a harkar ICT.

Zamu dauki kowace shekara mu bata taken abinda ya faru a dunkule, sannan mu biyo da labarin su, daga baya mu kawo abubuwan da suka faru masu muhimmanci guda goma tare da misalansu.

Zamu dauki kowace shekara mu ware mata nata rubutun, kowace shekara tana biye tare da shekarar ta.

Muna fatan Allah yayi mana jagora, ya bamu damar da zamu dama da kuma sanar da ku abinda Allah ya bamu ilimi a kansa, muna fatan zaku ci gaba da bibiyar mu da kuma kara bamu lokacinku wurin yi mana tambayoyi kamar yadda a shekarun baya kuke yi.

Na gode

Salisu Hassan Webmaster

Shugaban Duniyar Computer

Babban Editan Mujallar Duniyar Computer

25 COMMENTS

  1. Masha Allah

    Allah ya tabbatar da alheri, Allah ya qara daukaka Duniyar Computer.
    Munyi farin ciki da wannan bisharan Mal.

  2. Masha Allah
    Za mu kasance da duniyar computer a ko da yaushe Allah ya saka muku da mafificin alheri ya yi muku jagoranci a dukkanin lamurran ku.

  3. Alhamdu Lillah haƙiƙa nayi farin ciki sosai da samun wan nan labarin,kuma insha Allah ina fatan inkasan ce cikin masu samun cikakkun wan nan ilimi dazaku amayar Allah ta’ala ya anfanar da mu abin da zaku karantar damu,
    Ameen

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img