Artificial Intelligence ko ka kira shi da AI (fasahar wucin gadi), idan aka fada maka aikin sa kai kayi tsammanin wata alamrace irin wacce ake bada labarin tatsuniyar Duniyar Aljanun da Zulke dan Muhamman ya je. Amma ba haka abin yake ba domin wannan harka ta AI ta riga ta shiga cikin rayuwarmu da ayyukan da muke yi dumu-dumu, tun daga gida, asibiti, noma wanda idan ba an fada maka ba kai ba zaka yarda cewar kai ma kana amfani da wannan fasahar ba.
Kama daga ayyukan mu na gidaje da ofisoshi, da kuma yadda muke musayar bayanai tsakanin mu ta hanyar wayoyin tafi-da-gidanka lallai wannan fasahar AI ya zama karfen kafa wai takalmin kaza mutu ka raba. Amma matsalar ma wai mene ne shi wannan AI din sannan wasu ayyuka ne za a bada misali da rayuwarmu ta yau da kullum?
Mene ne AI?
Artificial Intelligence (AI) wata fasaha ce da ke ba kwamfuta ko na’ura damar yin abubuwan da da can sai mutum ne kawai ke iya yi—kamar yin tunani, yanke shawara, fahimtar harshe, da kuma koyan abu da kwarewa a cikinsa. A takaice, AI na nufin “basirar wucin gadi” wato basira da aka kirkira ta hanyar fasaha.
A wani lokacin akan danganta fasahar Aritficial Intelligence na’urar kwamfuta wacce take yin aikin da dan-adam mai kwakwalwa ke iya yinsa. Wannan aikin da take yi ya kunshi, karantar abu da fahimtar shi ta yadda ita wannan fasahar za a koyar da ita bayanai masu yawa ta fahimci wannan bayanan sannan ta bayar da sakamakon da ya dace.
Haka zalika, fasahar AI zata iya karantar bayanai ta fahimci matsala dake ciki sannan kuma ta iya magance su ko kuma ta bayar da hanyoyin da za a bi don a warware wannan matsalar. Haka ita wannan fasahar zata koyi yare ko harshe da ake mata da kuma ta iya yin mu’amala da mai irin wannan yaren. Haka wannan fasahar tana iya ganin hoto ko sauti ta iya fahimtar hoton waye ko sautin waye.
Shi yasa manhajoji ko na’urorin da aka hada su da wannan fasahar ta AI zasu iya ganin abu su kuma gane wannan abun. Suna iya fahimtar yaran dan adam, suna koyon sabon ilimi kuma su sarrafa shi, zasu iya bayar da gamsasshiyar shawara fiye da gwani. Suna iya sarrafa kansu da kansu, wanda hakan na nuna zasu iya aiwatar da kowane irin aiki ba tare da sa hannun mutum ba. Misalin motoci masu tuka kansu ya ishe ka misali.
Amma a shekarar 2024, masu bincike da kirkirar na’urori ko manhajojin AI, hatta da manyan gidajen jaridun duniya sun mayar da hankalinsu a bangare guda ne na generative AI (gen AI), fasahar da take iya kirkirar sabon rubutu, hotuna, bidiyo da dai sauran abubuwa.
Idan kana son samun cikakkiyar fahima game da fasahar AI ta bangaran gen AI, yana da matukar muhimmanci ka fara fahimtar kimiyyar da ke tattare da kayan ginin fasahar generative AI, kamar machine learning (ML) da kuma deep learning.
Mene ne Machine Learning?

Machine learning (ML) bangare ne na Artificial Intellegence (AI) wanda ya mayar da hankali wurin baiwa computer ko na’ura damar kwaikwayon yadda mutum yake koyon abu, yadda mutum yake yin aiki da kansa sannan ya inganta abinda ya koya domin a samu daidaito saboda gwanancewa koda an samu wadansu bayanai nan gaba.
Misalin da za a iya bayarwa a nan shine kamar yadda manhajar YouTube ko Tiktok ku kawo maka wasu bidiyoyi da kansu ta hanyar fahimtar irin bidiyon baya da kuka kalla, wannan fasahar Machine Learning ke aiki.
Mene ne Deep Learning?

Shi Deep learning wani bangare ne a cikin ML wanda yake amfani kamar kwakwalwar dan adam domin ya yanke hukunci kai tsaye, ana kiran deep learning da neural network saboda kamanceceniya da yadda yake lura da abubuwa masu sarkakiya kamar yadda kwakwalwar dan adam ke da sarkakiya a wurin ginawa. Mafi yawan abubuwan da muke amfani da su na na’urorin mu suna amfani da wannan kimiyyar da deep learning ke cikinsu, domin da wannan kimiyyar ce ake iya gane hoto da sauti ko maganar mutum a jikin na’urorin mu.
Misali idan kana amfani da manhajar da ke bude waya ta hanyar kallon fiskar mutum (Face Unlock) to deep learning ne ke gano furkarka har ya bude.
Mene ne Generative AI

Generative AI wani lokaci ana kiranshi da gen AI, Artificial Intelligence ne da yake kirkirar sabon rubutu, kirirar hotuna da babu su, kirkirar video ko kuma ya kirkiri surkullen kirkirar manhajojin kwamfuta ko wayoyi saboda umarni da aka rubuta mishi.
Misali ChatGPT kamar yadda ya shahara yana iya kirkirar rubutu ko kuma ya bada amsa kamar mutum, haka ana iya umurtar ChatGPT ya kirkiri hoton mutum a cikin sararin samaniya a kan rana yana shan kankara kuma yayi. To wannan gen AI ne ke yi.
Misalan Yadda AI Ke Taimakawa a Rayuwa
- Wayar hannu: AI ne ke taimakawa wajen fassara magana zuwa rubutu, lokacin da mutum yake yin magana se ya ita na’urar ta rika mayar da shi rubutu wanda a baya sai dai ya sami wani mutum ya rika yi masa. Inganta hoto, kamar a sami tsohon hoto wanda aka dauke shi shekaru masu yawa, ya lalace, ga shi babu launi a cikinshi sai AI ya gyara wannan hoton har ya saka mishi launi wani lokaci ma a saka shi ya motsa wannan hoton da sanya mutanen ciki su yi magana. Gano fuska, wannan sanannen ilimi ne ga duk mai amfani da smartphone, inda mutum ke sanyawa kwamfutarshi makulli amma yace idan ya kalli fuskarshi a jikin wayar ta bude. Sarrafa sautuka, kamar mutum ya sanya waya ta rika gane muryarshi idan ya bata umarni tayi idan ba shi bane ya bata kada ta yi.
- Gida mai wayo (Smart Home): Na’urori kamar Alexa ko Google Assistant suna amfani da AI don sauraren umarni da sarrafa fitilu, rediyo, ko TV, a irin wadannan gidaje ana saka musu irin wadannan na’urori a jikin gine ginansu, kama daga kafofin gida, fitulu da TV wanda idan mai gidan ya shigo zai magana da gidan cewa ya kunna wutar kicin kuma wutar ta kunnu ba tare yayi amfani da hannunsa ba, haka zai iya cewa TV ta tashi ko ta kashe kanta, yayi amfani da sautinsa ya kara karfin fanka ko rage ta da makamantan su, shi yasa ake kiran irin wadannna gidajen da Smart Homes.
- Gidajen Asibiti: Ana amfani da AI wajen gano cututtuka ta hoton X-ray ko MRI, wanda kafin zuwa AI ana bukatar likita a wannan fanni ya kalli wannan hoton yayi fassararsa, ya bada maganai, amma a yanzu AI zai iya gano cutar dake jikin mara lafiya, ya fadi karfinta da kuma abinda yake bukata akan lokaci.
- Aikin gona: AI na taimakawa manoma wajen gano ko amfanin gona na da lafiya ko kuma yana bukatar ruwa. Na’urorin gona da ake hada su da AI musamman masu aiki irin na IoT suna taimakawa manoma ta fannoni da dama, tun daga wurin sanin yanayi, da irin shuka da gonar take bukata, gano cututtukan kai tsaye ba tare likitan gona ba, gane cewar wannan shukar zata yi abinda ake so ko za a samu akasin haka.
- Makarantu: Ana amfani da AI don karantarwa ta intanet da tantance aikin ɗalibai cikin sauki, ta hanyar ita AI din zata iya tattara bayanai na dalibai, fitar da sakamako kai tsaye, duba kokari ko rashin kokarin malami ko dalibi (kamar Google Classroom ko Quizzes).
Yadda AI ke Hada da Rayuwarka Kullum
- Lokacin da kake amfani da Google Maps domin gano hanya mafi sauki—AI ke yi.
- Lokacin da Facebook ko Instagram ke gano fuska a hoto—AI ke yi.
- Lokacin da wayarka ke fassara magana zuwa rubutu—AI ke taimakawa.
- Lokacin da YouTube ko Tiktok ke baka bidiyon da zaka so—AI ya fahimci dandanonka.
Takaitaccen tarihin AI
Ba kamar yadda mutane da yawa suke tunanin AI y afara a cikin shekarar 2000 bane fa, idan muka koma ga kunne ya girmi kaka zamu fahimci cewar wannan fasahar ta dade sai dai ba kamar yadda take ba a wannan zamin ba.
Tunanin farko (kafin 1950s)
- Tun zamin su alu mai kauje a cikin labaran da ake bayarwa na Girkawa, dan adam ya dade da tunanin yin fasahar AI.
- A shekarar 1726 Junathan Swift ya ambaci na’urar lissafi da zata iya kirkirar rubutu, kamar dai shine farkon AI a na’urorin yin rubutu.
- A shekarar 1950 an tambayi Alan Turning Shin na’ura zata iya yin tunani? Ya bayar da jawabi da cewar idan na’ura zata iya kwaikwayon dan-adam a zance.
Haihuwar AI (1950s – 1980s)
- A shekarar 1956 John McMarthy ya fitar da wannan kalmar ta “Artificial Intelligence”
- Farkon aikin neural network (SNARC, 1951) da kuma farkon expert systems kamar DENDRAL (domin wanda ke duba datar chemical) suna daga cikin ci gaba na farko a harkar AI
- An kirkiri Lisp programming language a shekarar 1958, wanda shine mabudin bincike a AI.
AI na wannan zaman (1990’s zuwa yanzu)
- A shekarar 1997 na’urar IBM Deep Blue ta kayar da wani kwanin wasan Chess mai suna Garry Kasparov wanda ya nuna cewa lallai na’ura zata iya yin tunani da yi aiki fiye da na dan-adam.
- 2010s – 2020s AI ya gama ko’ina sabida zurfin nazarinsa da kuma aiki da manyan adanannen bayanai (big data) manhajoji irin su AlphaFold da ChatGPT sun sauya harkokin lafiya, bangaran ilimi da yadda ake mu’amala da abokanan cinikayya da fiye da haka ma.
Cigaba da koma bayan da AI ya kawo
A cikin kowane irin abu da ya shigo yana da amfani da kuma abinda ake jin tsoro, a cikin wannan harka ta kirkirar fasaha mai sarrafa kanta wato AI duk da cewar wadansu suna ganin shigowar wannan fasahar ya kawo sauki wurin wadansu al’amura wadansu kuma suna ganin akwai nakasu da tauye-tauye da wannan fasahar ta kawo.
Cigaba da AI ya samar
- Daidaito da yin komai da kansa- AI yana iya yin ayyukan da ake bukatar yinsu kowane lokaci, kamar shirya sakonnin Imel ko kuma lura da tattaunawar da aka yi da abokin kasuwanci, cikin hanzari, sauri da yinsa daidai fiye da yadda dan-adam zai yi.
- Taimako a harkar lafiya – AI yana iya gano cutar Kansa lokacin da aka nemi ta ta hanyar na’ura kuma ya dace da daidai cikin kashi 99%. Haka ana amfani da AI wurin taimakawa likitoci lokacin yin tiyata. Haka da AI yanzu ana iya fitar da figakafi cuta ko yin magani ba tare da daukar lokaci mai tsawo ba.
- Taimakaw a wurin gajiyawa dan adam – ana amfani da AI wurin taimakon masu bukata ta musamman kamar sanin me suke son su fada, ko masu matsalar gani su yi amfani da shi yana fada musu hanya da suke bi suje wani wuri.
- Daukar kwararren mataki – ana amfani da AI wuri gano masu zamba kan lokaci a harkan cinikayya, saukaka hanyar isar da abubuwan bukata wurin siye da sayarwa, haka AI na iya zama mai taimakon mutum na musamman a harkar kasuwanci ko talla a na’ura.
- Bunkasa tattalin arziki – kamar yadda aka fitar da kididdiga da kuma hasashe, amfani da AI da aka zai iya samar wa da Afrika a kalla $1.3trillion nan da shekara 20203 idan nahiyar ta saka jarinta a hanyar IT.
Koma bayan da AI ya kawo
- Rashin Aikin yi – na’urorin suna maye guraben da mutane suke yin aiki, musamman a masa’antun kere-kere da kuma aikin da dan-adam ke bayar da taimako na musamman.
- Son zuciya da nuna kyama – Idan aka horar da AI akan bayanai da suke nuna kyama, to zai kai shi da yin hukunci da bai kamata, kamar abin da ya shafin daukar aiki, da harkar police da kuma bayar da aron wani abu.
- Matsalar sirri – shi AI ya dogara ga bayanan mutane, wannan kuma yana kaiwa ga shin bayanan mutanen za a kiyayesu ba za ayi amfani da su a wurin da bai dace ba?
- Fargaba da tsoro – wane ne zai dauki alhaki idan AI ya dauki jirgi mai tuka kansa yaje yayi farmaki inda bai dace ba? Ko kuma mota mai tuka kanta idan AI ya kwace ragamar tukun ya kaiga yin hatsari? Doka da hukuncin har yanzu ba a san inda za a daura shi ba.
- Dogaro mara iyaka – a bangaran harkar lafiya, dogara kai tsaye akan AI ba tare da bin diddigin hukuncinsa ba zai iya kaiwa ga babban kuskuren da zai iya sa a rasa ran majinyaci.
Kammalawa
AI ba wani abu ba ne mai wahalar fahimta, abu ne da muka riga muka saba da shi a kullum, ko mun lura ko kuma bamu lura ba. Yana canza rayuwa a dukkan fannonin duniya daga noma, lafiya, ilimi, kasuwanci har zuwa nishaɗi.