27.1 C
Nigeria
Friday, May 9, 2025

Jagora Zuwa Ga Koyon HTML: Yadda Ake Gina Website a Hausa

Gabatarwa: Fahimtar Tubalin intanet

A wannan duniyar tamu, kusan kowane kasuwanci, da kuma kwararru a kowace irin harka, ko kasu sana’o’i da kere-kere na matukabar bukatar ganin sun kasance suna da wani gurbi intanet.  Wannan shi ne inda ilimin HTML (Hypertext Markup Language) yake taka muhimmiyar rawa.

Yana da matakukar muhimmanci ka san wane irin yare ko ilimi ake amfani da shi domin gina shafukan intanet. Idan kana kawai shiga website ne dan biyan wani bukatanka to lalle ya kamata kassan cewa akwai wani abu wanda ya ke faruwa kafin  ka iya biyan wannan bukatar taka a shafin da kake shiga na intanet, HTML ne matakin farko a ilimin da ake amfani da shi wurin gina shafukan Website. A matakin farko ilimin HTML shine ilimin da zaka koya ya baka damar gina shafukan da mutane zasu yi amfani da shi su ziyarce ka intanet.

A cikin wannan jagora ko kuma karatu zamu san abubuwa kamar haka:

  • Mene ne shi kanshi HTML din.
  • Tsarin yadda HTML din yake a aiki.
  • Wasu daga cikin ilimin tsarin da ka’idojin gina shafuka. Tags da kuma amfanin su.
  • Yaya HTML yake aiki idan aka kwatantashi da sauran fasahohin intanet . Kamar dai irin su CSS da kuma JavaScript.
  • Yanda mutun zai fara amfani da notepad wajen hada shafukan intanet wato Website da kanshi.

Mene ne HTML?

HTML wani yare ne wanda ake amfani da shi wajen tsarawa da gina shafi na intanet (website) da shi. Za ka iya kiran sa da kashin bayan intanet wato Website – tsarin da ke riƙe da dukan sassa da gidajen da muke shiga ko mu’amala a intanet. Idan babu ilimin HTML, to lalle zai yi wuya a samu shafuka da dakunan intanet (websites).

Da wannan yaren na HTML aka kowane irin abu da muka gani a cikin shafukan da muke ziya, wanda ya hada da rubutu da sauti, da bidiyo da hotuna da duk wani abu da muke gani a intanet to da wannan ilimin HTML aka yi amfani aka ajiye shi a inda ya dace.

Saboda haka duk mutumin da ke da sha’awar shima ya ga yana da wani gida a intanet kuma yana iya ajiyar rubutu ko labarai da yake son a rika karantawa ko dai ya dauko hayar wanda yake da wannan ilimin ko kuma ya koyi wannan ilimin da kansa, wanda kuma wannan darasi shine makasudin wannan karatu.

Matsayin HTML a ci gaban Intanet

Kasancewar ilimin HTML shine kashin bayan gina shafukan intanet, kuma shine ilimin da dole da shi zaka ajiye rubutu da sauran kayayyakin da kake son masu ziyartar ka su gani, amma ka sani yana da bukatar wadansu abokana nan aiki da suke taimaka masa wurin ganin hafin ya zauna da kansa, kuma rubutu ya yi kyau sosai, haka kuma wannan shafin na iya yin mu’amala kai tsaye da kayan da ke cikinsa. A wannan wuri shine inda ilimin CSS (Casecading Style Sheet) da kuma ilimin JavaScript suka shigo.

  • Shi CSS yana sawa ‘ya’yan HTML ado da kwalliya ne, kamar kara musu launuka, daidaituwar rubutu da kuma kyawun shafin intanet .
  • Shi JavaScript yana taiamakwa wurin ƙara hulda tsakanin ‘ya’yan HTML da kuma masu ziyarar shafukan mutum, yana ba ku damar ƙirƙirar abubuwa masu sarrafa kansu.

Saboda haka, hada wadannan ilimomi guda uku, HTML da CSS da JS ya zamanto abu mai matukar muhimmanci ga mutumin da yake son koyon ilimin gina shafukan intanet yake da bukatarsu. Duk da cewar ilimin HTML shine farko kuma shine ginshiki, wanda ko da babu wadancan guda biyun shafin ka zai ginu kuma abubuwa zasu fito, sai dai ba za su bayar da sha’awa ba musamman a wannan lokacin.

Tsarin yaren rubutun HTML (HTML Syntax)

Wannan bangare ne da zamu fahimci ka’idgogi da dokoki da ake bi ayi rubutu da za a ganshi a intanet. Shi wannan ka’ida idan aka karya ta to, ba dole mutum ya ga yadda yake so ba. Kamar dai tsarin ginin gida dake bukatar ginshiki kafin a fara daura masa tubali.

Abubuwan da ake bukata

Hanyoyin da mutum ke bukata domin gina shafukan intanet suna da yawa, amma kuma an kasa su kashi uku.

  1. Non-Text Editor
  2. HTML Editor
  3. Word Processing Application

Non-Text Editor

Wadansu manhajoji ne da ake amfani da su wurin gina shafukan intanet, amma kuma asalin irin wadannan manhajoji ba a yi su dan ginawa da tsara shafukan ba. Su irin wadannan manhajoji kawai ana yin rubutu a cikin su ne kawai, ba sa baka damar sawa rubutun da ak yi kwalliya, ko kara mishi girman rubutu ko kuma canza mishi launi.

Irin wadannan manhajoji wacce ta fi shahara a cikin kwamfutocin mu masu amfani da tsarin Windows sune NotePad. Wannan manhaja ce da aka yi ta domin yin rubutu kawai sai dai ana amfani da ita somin a rubuta kowane irin yaren kwamfuta, kamar HTML, CSS, JS, JAVA, C, C++ da dai makamantansu.

Idan mutum na son koyon ilimin HTML a matakin farko, muna bashi shawara da ya fara amfani da wannan manhaja ta NotePad, domin zata taimaka masa wurin sanin dukkan ‘ya’yan HTML tunda su rubutu mutum zai yi da kansa, babu wata na’ura ta musamman da zata taimaka masa wurin yin wannan rubutun.

HTML Editor

Su wadannan manhajoji ne na musamman da aka yi su domin su saukakawa mutumin da yake gina shafuka a intanet. Domin cike suke da kayan taimako na musamman game da ilimin HTML da CSS da JS wanda mutum da zarar ya fara rubutu harfi daya a cikin ‘ya’yan HTML kawai zata karasa masa.

Irin wadannan manhajoji su siyansu ake yi galibinsu, kuma suna da tsada, sai dai shafi daya da mutum zai gina da NotePad a sa’a daya, to idan da irin wadannan manhajojin ne bai wuce ya dauke shi mintuna 5 zuwa 10 ba.

E haka abin yake, sai dai bamu cika son mutumin da zai fara koyon ilimin gina shafukan intanet ya fara amfani da irin wadannan manhajoji ba, saboda ba zai fahimci kura-kurai da haddace tsarin gina-ginen ba, kasancewar komai da kanta ita wannan manhajar zata yi.

Wordprocessing Softwares

Wannan su kuma manhajoji ne da aka yi su domin yin rubutu na musamman kamar manhajojin rubuta wasiku, mukalai da zane-zanen na’ura wanda ko kadan ba a yi su domin su gina shafukan internet, amma kuma suna baka damar ka ajiye ayyukan ka a tsarin shafukan intanet.

Saboda haka irin wadannan manhajoji kamar Microsoft Word, Microsoft PowerPoint, CorelDraw da Photoshop da dai makamantansu suna baka damar idan ka gama amfani da su, aikin da ka yi sai ka ajiye shi a shafin internet.

To kwata-kwata ba a bada shawara mutum ya gina shafukan shi a irin wadannan manhajoji kasancewar yadda suke sanya HTML dinsu da ban yake da yadda aka sani a al’ada ana gina shafukan intanet.

To tunda mun fahimci cewar NotePad shi ne manhajar da tafi dacewa mu yi amfani da ita wurin gina shafukan mu yana da kyau mu yi amfani da ita gaba daya wurin koyon wannan ilimin.

HTML Tags da ka’idojin gina su

Kowane yare na kwamfuta yana da ka’idoji da ake gina tubalinsa, idan mutum zai gina shafukan intanet yana bukatar sanin wadannan tags din da kuma yadda suke aiki.

Tags sune tsarin rubutun da ake fadawa HTML cewa wannan shine danka, kai muke son ka karanta shi. To shi wannan tags din dole ya kasance wanda su masu kirkirar shafukan suka ce shine tags, wanda idan ka rubuta wani abu a cikin sa to ba zai yi aiki ba domin shafukan da suke bude rubutun HTML ba za su san me kake nufi ba.

Shi tag yana farawa da alamar “<” yana karewa da alamar “>” wanda kamar <html> wannan < da > sune alamar farko da shafukan inatent suke gane cewar wannan danmu ne. Abin da zai biyu tsakiyarsu dole ya zama wanda aka ce ya zo ne. Misalin <html> kalmar HTML da aka saka tsakanin su shine tag din.

HTML tags iri uku ne

  1. Cikakken Tag
  2. Matsakaicin Tags
  3. Karamin tags

Cikakken Tags

Su wadannan wadansu tags ne da ake bukatar idan aka bude su dole se an kulle su. Misali a ka’ida idan ka rubutu ta su to dole sai ka sake rubuta su daga karshe amma ka sa musu alamar / kafun na biyu wanda yake nuna su sau biyu ake rubuta su.

Misali <html> dole a sake rubuta wani </html> wanda zai nuna cewar an rufe shi. Kamar mutum ya rubuta <body> dole sai ya rufe shi ta hanyar sake rubuta </body>.

To wannan alamar “/” da ake sakawa shike nuna an rufe wancan na farko da aka bude. Irin wadannan tags din sun yi yawa a ilimin HTML.

Matsakaicin Tags

Su kuma irin wadannan tags din ba sa bukatar maimaita su a rufe su daga karshe, sai dai a inda aka bude su a ciki ake rufe su. Misali kamar <img> baya bukatar dai an sake rubuta </img> yin haka sabawa ka’idar gina shafukan intanet ne. Yadda aka yi da matakaitan tags kamar irin su <img /> shine a karshe kafin saka “>” ake saka alamar “/”.

Irin wadannan tags din basu da yawa kuma basu wuce a irga su a ‘yan yatsu ba.

Karamin tags

Shi kuwa wannan tags din shine wanda idan aka bude shi ba a rufe shi kuma ba ba dole sai an yi amfani da alamar “/” ba. Irin wadannan tags din sune mafi karanci a cikin tags da ake da su. Misalign <br> da irin su <hr> dukkansu basa bukatar karin irinsu ko kuma saka musu alamar “/”.

Yaya rubutun HTML ke aiki?

Kana bukatar Browser domin bude shafukan da aka kirkira da ilimin HTML. Ita kuma browser manhaja ce ta musamman da aka yi ta domin ta rika tankade HTML tags ta fito da sakamakon aikin da shi wannan tags din da yake yi.

Shi yasa browser take matsayin rariyar tace rubutun HTML, da kuma hanyar ganin duk shafukan intanet. Misalin idan aka rubuta <b>Musa Anka</b> idan ya tashi fitowa zai fito a browser “Musa Anka” wato wannan tag na “<b>” yana saka rubutu yayi kyauri.

Fandishon din ginin HTML

Wannan rubutu na kasa shine abu na farko da ak son mutum ya kiyaye kafin ya rubuta komai a ginin shafin sa,

<HTML>

<head></head>

<body></body>

</HTML>

A darasin mu zamu yi bayanin wannan ginin da kuma ci gaba da yadda mutum zai koyi yin rubutu tare da tsara shafukan intanet. Mal. Musa Anka dalibin Computer Science a Kaduna Polytechnic

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Yadda ake amfani da Google Drive

Google Drive wata ma’ajiya ce da kamfanin Google dake...

Blockchain a Gwari-Gwari

Wannan wani kirkirarriyar fasaha ce mai wuyar sha’ani da...

Fasahar AI: Kafin Musulmi yayi amfani da ita dole yasan wadannan abubuwa guda 7

Rubutawa: Salisu Hassan Webmaster GabatarwaA zamanin da na’urori ke iyan...

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img