27.1 C
Nigeria
Thursday, May 8, 2025

ICT a TikTok: DAGA GASAR RAYE-RAYE ZUWA HARKAR ICT YADDA MATASA SUKA MAYAR DA MANHAJAR TIKTOK MAKARANTAR ICT

Da zarar an ambaci manhajar Tiktok babu abinda ke fadowa mutane illa dandaline na shashanci, da raye-raye da badala da barkwanci, kai har da wurin zage-zage. Amma ba haka abin yake ba a yanzu, domin manhajar tiktok ta habaka cikin kankanin lokaci, kuma ta bunkasa a bangaren yada ilimi da karantarwa, musamman a tsakanin matasa. Yayin da miliyoyin mutane suke kallon kananun bidiyoyi a kullum. Kwararun matasa masu fasaha da kuma kirkira, wato content creators masu tasowa kamar tech savvy youth wanda yake amfani da dandamalin tiktok domin koyar da harkar ICT ko kirkiran sababbin abubuwa da hanyoyin koyarda su.

Tiktok na ba matasa damar bayar da gudunmawa da bada ilimi cikin sauki. Kuma yana da sauki wurin amfani da kayan kirkiran bidiyoyoyi. Tiktok yana bada damar samu ilimin ICT sosai musamman a yankin da akwai karanci masana kayyayaki ko wurin koyar da Ilimin ICT

Wannan manhaja ta tiktok tana ba matasa dama wurin bayar da gudunmawa na yada ilimin ICT cikin sauki, ta hanyar kirkirar kana nan bidiyoyi domin koyar da ilimin ICT.

MEYASA AKE KOYAR DA ILIMIN ICT A MANHAJAR TIKTOK

Koyar da ilimin ICT a dandamalin tiktok yana da amfani saboda yanzu kwararru a ICT suna da muhimmanci don shiga cikin harkar tattalin arziki na zamani ko amfani da manhaja (software) na ofis ko fahimtar application na coding ko gina dakunan intanet (website) ko kula da tsaron kwanfutuci ko binciken bayanan AI. Yawancin al’umma musamman a kasashen da suka cigaba dama wanda suke tasowa har yanzu suna kokarin wajan samun karin horon ilimin ICT na yau da kullum

Tiktok dandamali ne na daya  daga cikin dadalin sada zumunta  da yake bada damar kikiran kananun bidiyoyi da gyara su da kuma yadawa ga al’ummar duniya.

YADDA TIKTOK YAKE WARWARE MATSALOLI A ILIMIN ICT

  • Yana bada damar a kirkiri kananun bidiyoyi masu saukin fahimta wurin shiga koyar da ilimin ICT
  • Inganta koyar da al’umma wurin kula da koyar dasu daki daki
  • Karfafa ilimin fasaha

Matasa suna amfani da manhajar tiktok wurin koyar da darrusan ICT masu musamman masu rikitarwa zuwa masu sauki, masu alaka da darussa a aikace galibi suna amfani da bada labari ko kwatance rayuwa na gaske wurin koyarwa

ABINDA AKE BUKATA WAJAN YIN AIKIN KOYAR DA ILIMIN ICT A TIKTOK

  • Samun damar iya shiga gidan tiktok da wayoyin hannu: kayan aiki na asali kamar wayoyin hannu masu arha da tsare tsaren bayanai suna da mahimmanci don kirkira da duba abubuwan ilimi
  • Kwarewar karatu na digital: matasa suna bukatar kwarewa na asali a gyaran bidiyo, sadarwa, da batutuwan ilimin ICT da kansu don su zama masu kirkire kirkiren abubuwa ko masu koya.
  • Alu’umma masu taimakawa: karfafawa daga makarantu, kungiyoyi masu zaman kansu, iyaye, da mashawarta a fanin fasaha na taimkawa wurin tabbatar da bada gudunmawa wa masu kirkire-kirkire don cigaba da koyarwa
  • Dandamalin da yake bunkasa abubuwan ilimi: tiktok yana kara cigaba daga hashtags na ilimi kamar #LearnOnTiktok, #ICTtips, ko #CodeTok saboda abubuwan ilimi kada su buya daga bidiyoyin nishadantarwa da barkwanci

YADDA MATASA KE KOYAR DA HARKAN ICT AKAN MANHJAR TIKTOK NA HAKIKA

  1. Koyarda da coding a cikin dakika 60: akwai wani matshi dan shekara 21 a kasar Ghana yana gudanar da tashar tiktok inda yake koyar da ilimin Python ta hanyar amfani da allo da kyamarar hannu. Yana warware abubuwa masu tsauri kamar su loops, variables da functions a bayani na dakika 30. Galibi yana hada su da ka’idojin girke-girke da wasanni kallon fa.
  2. Cyber Auntie daga Kenya: wata budurwace da take aiki a matsayin innar wani wacce ta kware a mafisa ta barkwanci, amma a ciki take koyar da tsaron shafukan intanet (Cybersecurity) da yaren Swahili

Cikin daya daga bidiyoyin da ta kirkira, ta kama danta ya fada hannun  phishers da scammer ta hanyar imel na karya, shine take fada masa yadda zai kare kansa. Tana yin barkwanci sosai wannan ya sanya mutane da dama suke bibiyarta, amma kuma sakon da take isarwa lallai yana kaiwa ga inda ake so.

  • DIY Tech Repair daga Nigeria: Wasu matasa ne daga Jihar Kano a Nigeria da suke nuna hanyoyin da mutum zai bi ya gyara wayar hannunsa idan ta lalace, ya mutum zai karawa na’urarsa sauri, gyara fuskar waya idan ta lalace, da dai makarantsu. Suna amfani da yaren Hausa da Turanci wurin yin wannan shirin wanda ya sanya mutane da dama suke bibiyarsu
  • Yan mata masu coding da rawa: ‘Yan mata a kasar Afirka ta Yamma (South Africa) suke amfani da raye-raye da suke tashe sai a ciki suke koyar da ilimin HTML ko CSS bidiyoyin su yana nuna kana nun codes tare da waka mai ban sha’awa
  • Yin bayani kan AI cikin salon dariya domin ya fi sauƙin fahimta: Wani ɗan TikTok daga kasar Uganda ya kwaikwayi yadda AI irin su ChatGPT ke aiki ta hanyar wasan kwaikwayo. A cikin bidiyon nasa, yana taka rawar “na’ura mai kwakwalwa” da kuma “mai tambaya mai ruda mutane” a lokaci guda, wannan salon ya jawo hankalin mutane sosai – har mutane suka fara tambaya da tattaunawa a sharhi kan yadda za a iya amfani da AI a Afirka, musamman wajen ilimi, kasuwanci, da koyarwa. Yayin da mutane ke nishadantuwa, mutane na koya abubuwa masu muhimmanci game da fasahar zamani!

Yadda za’a inganta ilimin ICT a tiktok

  • Kirkiran hashtags da kuma jerin karatuttuka mai dogon zango
    • Karfafa masu kirkira kirkire ta hanyar amfani da tsararraen hashtags kamar #ICTTok, #codeInAfrica, ko #DigitalSkillNaija.
    • Jerin tsarirruka misali (Ranar ta 1 na koyan yadda ake tsaro yana gizo ko kwamfuta) yana taimakawa masu koya ta yadda zasu bi hanyar koya akan lokaci
  • Haduwa da kwararru da malamai a harkar ICT
    • Matasa za su iya hadin gwiwa da tsofaffin masana harkan ICT don tabbatar da fadada abubuwan sun a ilimi
    • Kuma kamfanoni da kungiyoyi masu zaman kansu (NGO) zasu iya daukan nauyi ko bada shawarwari ga masu kirkire kire
  • Amfani da yarukan gida
    • Mafi yawanci kirkire da ake da Hausa, Swahili, Yoruba, Zulu ko French yana kaiwa ga matasa masu yawa a nahiyar Afirka.
    • Yana cire shamaki ga yaruka da kara fahimtar ka’idojin ilimin fasaha
  • Karfafa masu gasar fasaha
    • Kamar gasar rawa, gasar fasaha na iya yaduwa da sauri
      • Nuna yadda kake shirya coding dinka
      • Gyara tangardar wannan laptop din
      • Kirkira shafukan internet a kwana 3
  • Bunkasa ilimin ICT da makarantun gida
    • Makarantu suna iya Karin bayani akan masu bada ilimin fasaha a tiktok a matsayin wakilai
    • Dalibai kan iya samun kwarin gwiwa wurin kirkiran abubuwa a matsayin aikin gida

Kammalawa: Koyo Cikin shafar fukar wayarka (Swipe)

TikTok ba wurin nishaɗi kawai bane a yanzu, yana zama ajin karatu na zamani ga karni mai zuwa, musamman ga masu sha’awar ICT.

Ta hanyar kirkira, saukin amfani, da hadin kai, matasa na canza tunaninsu da amfanin wayoyinsu zuwa makamin wayar da kai da koyo.

Idan aka samun karin cigaba, kulawa, da tsarin da ya dace, TikTok na iya taimakawa wajen haifar da sabuwar makarantar koyon ilimin fasaha da kera-kere, ba a Afirka kawai ba, har ma a duniya baki ɗaya.

Mu daina yin bidiyoyin mu don nishaɗi kawai – mu fara yin bidiyon domin koyo, mu raba ilimi, kuma mu zaburar da juna.

Sa’adatu Musa Wada, malamace a Duniyar Computer, tana shekarar karshenta a HNDII a Kaduna Polytechnic inda take karatun Computer Science, ta kware a fannoni masu yawa a bangaran Programming, Cybersecirity, Web Design & Development, UI/UX, Graphics & Multimedia da makamantansu.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Jagora Zuwa Ga Koyon HTML: Yadda Ake Gina Website a Hausa

Gabatarwa: Fahimtar Tubalin intanet A wannan duniyar tamu, kusan kowane...

Yadda ake amfani da Google Drive

Google Drive wata ma’ajiya ce da kamfanin Google dake...

Blockchain a Gwari-Gwari

Wannan wani kirkirarriyar fasaha ce mai wuyar sha’ani da...

Fasahar AI: Kafin Musulmi yayi amfani da ita dole yasan wadannan abubuwa guda 7

Rubutawa: Salisu Hassan Webmaster GabatarwaA zamanin da na’urori ke iyan...

Makaloli

Jagora Zuwa Ga Koyon HTML: Yadda Ake Gina Website a Hausa

Gabatarwa: Fahimtar Tubalin intanet A wannan duniyar tamu, kusan kowane...

Yadda ake amfani da Google Drive

Google Drive wata ma’ajiya ce da kamfanin Google dake...

Blockchain a Gwari-Gwari

Wannan wani kirkirarriyar fasaha ce mai wuyar sha’ani da...

Fasahar AI: Kafin Musulmi yayi amfani da ita dole yasan wadannan abubuwa guda 7

Rubutawa: Salisu Hassan Webmaster GabatarwaA zamanin da na’urori ke iyan...

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img