23.5 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

Abubuwa masu muhimmanci guda 10 a IT da suka faru a shekarar 2020

Kamar yadda muka alkawarta muku a cikin rubutun mu na baya mai taken “Duniyar Computer barka da dawowa – Abubuwan da suka kubucewa masu karatu daga shekarar 2020 – 2025” inda muka ce zamu kawowa masu karatu abubuwan da suka gabata a cikin shekarun da suka wuce daga 2020 – 2025 wanda mu ba mu samu mun gabatar ba

A wannan rubutu zamu kawo muhimman abubuwa guda 10 mafi shahara da daukar kai a shekarar 2020 da suka faru a harkar IT a cikin bayanar da kuma kawo su a daidaikun su da kuma misali a kowa abu.

2020: RAYUWA TA KOMA DIGITAL

Mahhajoji da Kayan aiki (Software & Tool): A lokacin da aka rufe garuruwa babu wata manhaja da ta samu karbuwa kamar manhajar Zoom wacce kafin zuwan Corona mutane kusan miliyan 10 suke amfani da ita a shekarar 2019, amma da wannan annoba ta bayyana sai gashi a dan kankanin lokaci sama da mutane miliya 300 suke amfani da manhajar. Wannan manhaja ce da ke ba mutane damar yin magana kowa na ganin kowa, aikawa da sako rubutu lokacin tattaunawar da dai makamantansu. Haka a wannan shekarar kamfanin Microsoft shima ya fitar da tashi manhajar ta tattauna irin wannan manhajar domin ba mutane damar yin ayyukan Office a gida mai suna Microsoft Team. Haka suma kamfanin Google suka kirkiro ta su manhajar wacce ake kira da Google Classroom wanda yake shi kuma manhaja ce wacce take mayar da hankali ga abubuwan da suka shafi makaranta da karantawa.

Manhajojin biyani kafin kayi aiki da ni SaaS (Software as a Service) suka kara samun daraja da kuma daukaka harkar kamfanonin Cloud Computing kamar AWS da Azure wanda hakan ya taimaka musu wurin ganin sun inganta ayyukansu domin samarwa da mutane damar ayyukan ba tare da wata matsala.

A dai cikin wannan shekarar ta 2020 yaren kwamfuta na Python ya kara samun tagomashi saboda amfani da ake yi dashi wurin kirkirar manhajoji masu sarrafa kansu AI (Artificial Intelligence) musamman wurin bincikowa da gano COVID, inda manhajar BlueDot tana daga cikin manhajar da aka yi da wannan programming language na Python domin ya rika gane wurin da wannan kwayar cutar ta bazu.

Karancin Hardware:  A dai cikin wannan shekaran ne aka samu karancin kayan wutar lantarki na Semiconductor, wanda hakan ya kawo tsaiko sosai a kusan komai kamar kirkirar GPU. Amma kuma Apple’s M1 (MacBook Air) ita ce wacce ta fi kowace kwamfuta kyau da karfin aiki a wancan shekarar.

Game da maganar karfin shiga internet a wannan shekarar ne aka fito da fasahar 5G a kasar China da kuma South Korea, duk da kashi 40% na gidaje a karkara a wancan lokacin basu da isasshen internet.

Ga jerin abubuwa masu muhimmanci guda 10 da suka faru a shekarar 2020

2020 – Hanzarin Dijital Saboda Annobar COVID-19

  1. Aiki daga Gida da Kayan Aikin Tattaunawa Aiki daga gida ya zama al’ada a duniya baki ɗaya.
    Misali: Yawan masu amfani da Zoom wajen tarurrukan yau da kullum ya tashi daga miliyan 10 (2019) zuwa miliyan 300 (2020).
  2. Cloud Computing – Ta zama muhimmiya don ci gaba da gudanar da kasuwanci a lokacin kulle.
    Misali: Amfani da Microsoft Azure da AWS ya karu sosai yayin da kamfanoni ke komawa ayyukan sa sosai yanar gizo.
  3. Tsaro na Intanet (Cybersecurity)– Hare-haren (Cyber attack) a yanar gizo sun karu, musamman akan na’urorin masu aiki daga gida.
    Misali: Yawaitar hare-haren phishing da aka haɗa da yaudarar masu amfani ta COVID-19.
  4. Yada 5G – An ci gaba da shimfiɗa fasahar 5G duk da annoba; wannan aikin yana da matukar muhimmanci ne domin taimakawa fasaha da internet.
    Misali: Koriya ta Kudu da China sun jagoranci shimfiɗar 5G a duniya.
  5. AI da Automation – AI ya kawo sauki sosai wurin gano matsaloli a harkokin kayan masarufi, nazarin bayanan lafiya, da kuma chatbots.
    Misali: Kamfanin BlueDot ya yi amfani da AI wajen gano alamu na farko na cutar COVID-19.
  6. Kundin Koyo ta Yanar Gizo (E-Learning Platforms) – Ilimi ya koma dijital cikin gaggawa.
    Misali: Masu amfani da Google Classroom sun karu da fiye da mutane miliyan 100.
  7. Siyayya da Biyan Kuɗi ta Intanet (E-commerce & Digital Payments) – Siyayya ta intanet ta karu sosai, musamman kayan abinci da na masarufi.
    Misali: amfani da Ribar Amazon ya karu matuka, yayin da amfani da PayPal da wallet ɗin waya ya yawaita.
  8. Fasahar Lafiya da Kiwon Lafiya ta Yanar Gizo (HealthTech & Telemedicine) – Ayyukan likitoci daga nesa sun zama dole.
    Misali: manhajar Teladoc ta kusan ninka sau biyu.
  9. Haɗa Kai Dijital (Digital Inclusion) – Banbanci wajen samun intanet ya kara bayyana.
    Misali: UNESCO ta nemi a saka jari cikin ilimin dijital a yankunan karkara.
  10. Bayanan Dijital da Ababen Sadarwa (Data & Connectivity Infrastructure) – Kamfanonin sadarwa sun yi aiki tukuru wajen inganta intanet mai sauri.
    Misali: Starlink ta fara gwaji don samar da intanet a yankunan da ke da karancin sabis.

Kirkirar Shekara: mRNA vaccine technology

Mafi Kyawun Waya: iPhone 12 Pro Max.

Mafi Kyawun Kwamfuta: MacBook Air (M1)

Mafi kyawun Programming Language: Python wanda ya jagoranci a AI da data science projects.

Wadannan shine a takaice abinda zamu iya kawo muku, akwai abubuwa dama da suka faru a wannan shekarar ta 2020, amma a harkar IT lallai wadannan sune abubuwa guda 10 mafi shahara.

Da fatan an karu! Se mun hadu a shekarar 2021

9 COMMENTS

  1. Maasha Allah, gaskiya wannan rubutu ya kayatar ya kuma tuna mana abubuwa da yawa da suka gabata musamman a 2020 bangaren Tech. Allah ya saka da alheri. Duniyar Computer lallai duniya ce.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img