23.5 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

Abubuwan da suka faru a shekarar 2022: Shekarar Kwarancewa a – AI, Cloud da Birane Masu Aikin Dabara!

Shekarar 2021 ta ci gaba da gina kan sauye-sauyen da suka faru a 2020, inda fasahar zamani ta zamo jigon rayuwar aiki da kasuwanci. Aiki daga gida da ofis lokaci guda (Hybrid Work) ya zama sabuwar hanya ta gudanar da aiki, inda kamfanoni suka zuba jari a manhajoji kamar Microsoft Teams, Slack, da sabbin kayan aikin AI da RPA (Robotic Process Automation) domin ƙara saurin aiki da rage buƙatar maimaita ayyuka da hannu.

Hare-haren yanar gizo sun ƙaru sosai, wanda ya sa kamfanoni suka mayar da hankali sosai wajen tsaron bayanai ta hanyar tsarin Zero Trust. A bangaren kayan aiki (hardware), an fuskanci karancin semiconductors, wanda ya shafi farashin kwamfutoci da wayoyi – amma duk da haka, an gabatar da sabbin kayayyaki masu ƙarfi kamar Dell XPS 13 da Samsung Galaxy S21 Ultra.

Amfani da Cloud Computing ya zurfafa, tare da inganta sadarwar 5G, biyan kuɗi ta intanet, da kuma IoT a masana’antu. A bangaren lafiya, telemedicine ta ci gaba da karɓuwa, yayin da ake amfani da AI wajen nazarin lafiyar marasa lafiya.

Wannan ci gaba da ƙoƙarin sabunta tsare-tsaren fasaha ne ya haifar da karin buƙatu ga kwararrun IT, wanda ya bar gibi a fannin ƙwararru. Wadannan abubuwa ne da suka kafa harsashi ga sabbin fasahohi da hanyoyin kasuwanci da suka bayyana a shekarar 2022.

A wannna shekarar ta 2022 kuwa, manhajojin AI sun kara samun inganci ta yadda GPT-3 zai iya rubuta kirkirarriyar waka da kuma, DALL-E zai iya zana maka manyan zane mai launuka, saboda haka kungiyar Tarayyar Turai (EU) suka fitar da dokar da zata sanya amfani da AI ya zama a bayyane ta hanyar da kowa zai san me ke faruwa ba tare da boye-boye ba, shi kuma harkar Edge Computer ta rage jinkirin akan na’urorin IoT a harkar noma, misalin AI-powered crop sensors.

Kirkire-Kirkiren Kayan Aiki (Hardware): Apple ta sake fasalta amfani da kwamfuta mai ƙarfi ta hanyar Mac Studio, yayin da wayoyin da ake nannade su kamar Galaxy Z Fold4 suka yi zarra a wannan shekarar. Quantum Computing ma ta samu ci gaba sosai — irin su IBM Osprey mai 433-qubit ya nuna yadda wannan fasahar ta kawo sauyi chanji sosai a harkar na’ura.

Sauyin Tsaro: Tsarin Cyber-Mesh da sabbin dokokin GDPR sun yi sun taimaka matuka wurin kare na’urori da hare-haren ‘yan dandatsa da kusan kashi 62% saboda karin fasahar AI da aka shigar da ingantawa a cikin lamarin.

Ga jerin abubuwa guda 10 masu muhimmanci da suka faru a shekarar 2022 a harkar IT

2022 – Fadadawar AI da Kafuwar Tsare-tsaren Fasaha

  1. Hade AI da ML cikin Ayyukan Yau da Kullum – Kamfanoni sun fara saka fasahar AI cikin ayyukansu na yau da kullum.
    Misali: Salesforce ta haɗa Einstein AI don gane hanyoyin sayar da kaya ta atomatik.
  2. Karɓuwar Edge Computing – An rage jinkiri (latency) a aikace-aikacen da ke buƙatar saurin aiki a cikinsu.
    Misali: Kamfanonin Intel da NVIDIA sun ƙaddamar da kayan aikin Edge AI don sarrafa masana’antu.
  3. Fasahar Cloud-Native da Containers – Yin amfani da microservices ya ƙara sassauci da saukin faɗaɗawa.
    Misali: Spotify ta yi amfani da Kubernetes wajen isar da sabis na kiɗa.
  4. Tsarin Tsaro na Cybersecurity Mesh – Tsarin kariya ga bayanai da kayan aikin da ke ajiye a girgijen intanet.
    Misali: Kamfanin IBM ya tallata tsarin mesh don kariyar bayanan girgije ga kamfanoni.
  5. Yawaitar Amfani da SaaS (Software as a Service) – Manhajoji na musamman ga fannoni kamar noma, lafiya da kuɗi sun ƙaru.
    Misali: AgriWebb ta bayar da manhajoji na SaaS don kula da kiwon dabbobi.
  6. Amfani da Blockchain a Kasuwanci – An fara amfani da blockchain wajen tabbatar da gaskiya a sarkar kaya.
    Misali: IBM Food Trust ta yi amfani da blockchain don gano asalin abinci.
  7. Gudanar da Bayanai da Bin Ka’idojin Dokoki – An ƙara mayar da hankali kan kariyar bayanan mutum da na kasuwanci.
    Misali: Apple ta gabatar da App Tracking Transparency (ATT) don kare sirrin masu amfani.
  8. Kayan Aikin Low-Code/No-Code – Sun baiwa wadanda ba masu shirya lamba (developers) ba damar kirkirar manhajoji.
    Misali: Airtable da Microsoft Power Apps sun ƙara shahara.
  9. Ayyukan Fasaha Masu Dorewa (Sustainable Tech) – Kamfanoni sun mayar da hankali wajen amfani da fasaha mai kare muhalli.
    Misali: Google ta gudanar da cibiyoyin bayananta ba tare da hayaƙi ba a 90% na lokaci.
  10. Birane Masu Fasaha da Ingantattun Tsare-tsare (Smart Cities) – An yi amfani da ICT wajen gudanar da wutar lantarki, sufuri da makamashi.
    Misali: Singapore ta faɗaɗa shirin ta na Smart Nation.

Kirkira Mafi Girma a Shekara: Generative AI – DALL·E da ChatGPT beta.
Mafi Kyawun Waya: iPhone 14 Pro
Mafi Kyawun Kwamfuta: Apple Mac Studio
Fitaccen Software: Figma
Salon Shirin Kwamfuta na Shekara: Rust ya fara ɗaukar hankula

5 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img