Shi dai programming language a Hausance ka iya kiranshi da yaren da ake iya yiwa kwamfuta magana dashi har ta fahimci me kake son tayi. Shi wannan yare ba irin yaren mu bane saidai mu mutane mu muka zauna muka shirya mata yadda zata rika fahimtar umarni da ake son ta gabatar da kuma yadda ake son ta gabatar baki daya.
Abinda zai baka mamaki shine yadda irin wadannan yaruka kullum ake kara kirkirosu sannan kuma ka samu irin wadannan sababbin su danne tsofaffi duk da cewar akwai wadansu yarukan da suka dade sun shahara kuma har zuwa wannan lokacin su jan zarensu bai kuma tsinke ban.
Duk da cewar zaka iya samu dalibi ya mayar da hankalinshi akan wani yaren kwamfuta wanda yake tsammanin zai iya biya masa bukata amma a zahiri yakasance ko kadan wannan yaren bashi da wani amfani a wurinshi.
Idan ana maganar biyan kudin aiki ko albashi da kuma wane programming language zan koya don in samu kudi sosai to ya danganta da shekarar da ake amfani da wannan programing din, da kuma irin abin da ake yi dashi na kawo kudi. Duk da cewar ba dole bane ace kamfanin da suka dauke ka aiki duk da iyawarka a daya daga cikin yarukan nan ace su iya biyanka albashin da wani kamfani ke biyan ma’aikatansa.
A wannan darasi zamu kawo muku programming language guda 8 wadanda aka fi samun kudi da su a shekarar 2018 da ta gabata.
Go Programming Language

Wannan programming Language ana biyan wanda ya koye shi ya samu aiki a babban kamfani suna biyan karancin albashi a shekara $110,000 (N39,710,000.00). shi wannan programming language na Go yaren wanda al’umma suka taru suka kirkireshi (open source programming language) wanda ake iya kirkirar manhajoji (software) masu sauki da masu nagarta sosai. Dalilin shaharar wannan programming language na Go saboda kamfanin Google da Facebook da Netflix da SoudCloud da Adobe da Dropbox duk suna amfani da shi wurin kirkirar manhajojin da zasu iya aiki a software dinsu. Wadannan kamfanoni suna son wannan yaren ne saboda sauki gabatar da aiki, saurin tashi, amfai da memory a lokacin da ake son ayi aiki da shi. A takaice dai wadansu ma suna ganin wannan yaren shi zai zama yaren server a nan gaba.
Objective-C

Matsakaicin albashin da ake iya biyan wanda ya koyi wannan programming language din Obhective-C shine $108,000 (N38,988,000.00) Shi wannan yaren ana amfani da shine wajen kirkiran manhajoji da suke iya in aiki a Mac OS X da kuma iOS. Wannan programming language na daga cikin yaren da yake baiwa yan kasar Amurka aiki yi da duka samun riba.
Python

Babban ma’aikacin da ya iya Phython Programming Language yana daukar albashi $105,000 (N37,905,000.00). Python yaren kwamfuta ne wanda aka fi mayar da hankali game da kirkiran manhajojin da suke iya sarrafa bayanai na data analysis, lissafe-lissafe, fahimtar ilimin karafan kwamfuta (machine learning), kirkirar shafukan intanet da dai makamantansu. Manyan kamfanonin da suke daukar masu ilimin Python sune kamfai NASA da Google. Ana kuma saka wannan yaren na python na daya a mafi shaharar yaren kwamfuta a duniya da kuma shine na biyar a neman sanin yadda ake koya a duk programing da ake da su.
Ruby on Rails

Matsakaicin albashin da wanda ya koyi yaren Ruby on Rails kuma ya samu aiki shine $89,774 (32,408,414.00) kamar yadda kamfani Glassdoor ya fada. Ruby ya samu daukaka ne bayan da ya shahara wurin amfani da shi a shafukan intanet domin kirkirar manhajoji na intanet. Ana amfani da Ruby wurin yin application masu matukar muhimmanci da kuma amfani.
C#

Kamar yadda kamfanin Quartz Media suka fada, matsakaicin albashin da ake biyan wanda ya iya C# shi ne $89,000 (N32,129,000.00). C# ya shahara kuma ya samu karbuwa tun a lokaci da kamfanin Microsoft suka kirkiro shi. Shi wannan yaren ana amfani da shi domin kirkirar application da zasu yi aiki a Desktop Computer ko a Intanet. Idan kana son ka rika kirkirar application da suyi Microsoft to ka koyi C#.
Java

Java yana daga cikin programing language da aka fi nema kuma ake biyan albashin sa daga $74,000 (N26,714,000.00) zuwa (N46,930,000.00) $130,000 ga Senior Java Developer. Baya da cewar shi yare ne da ake yin manhajoji na wayar android, haka ana kuma amfani da shi wurin kirkirar manhajoji da ake saka su a cikin motocinmu da kuma bankunan mu. Java programming language ne mai kyau da ya kamata mutum ya koya.
Swift

Kamar yadda Payscale suka ce, wanda ya iya yaren Swift yana iya samun albashi matsakaici na $78,933 (N28,494,813.00). Shi wannan yaren na Swift da shi ake amfani ake kirkiran manhajojin MacOS da iOS da watchOS da tvOS wanda dukkansu kayan kamfanin Apple suke amfani da su.
Kotlin

A fadin kamfanin Paysa, wanda ya iya yaren Kotlin yana samun matsakaicin albashin da ya kai $66,186 (N23,893,146.00) a shekara. Wannan yare Jetbrains ne ya kirkiroshi kuma yanzu haka shine halattacen yare da ake amfani da shi domin kirkirar manhajoji da zasu yi aiki a wayoyin Android.
A shekarar 2017 ne aka kirkiri wannan yaren kuma ya samu karbuwa sosai domin yana aiki tare da Java, sannan kamfanin Google ke taimaka wurin lura da gyaranshi sa, sannan samun karbuwarsa a wurin jama’a ya sa ya zama yare wanda ya kamata mutum ya koya.
Rufewa
Yana da kyau mai karatu ya sani, ba kamar yadda muka fada ba, wannan albashi ya danganci wasu irin ma’aikata ne da kuma ma’aikatar da mutum ya samu aiki, kada wani dan karamin kamfani ya dauke ka aiki ka ce ka iya wadannan programming din kuma kana bukatar sai an biyaka wannan albashi. Hasali ma manyan ma’aikata Senior Developer su ake magana a wannan mukalar.
Ina kokarin karanta c++ da Python yanzu haka ina bukatan chikeken Karin bayani Wanda zakaramin haske akay wa
Nan gaba kadan