38.2 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

An Kera Mota Mai Aiki Da Iska

Gaba daya motar da robar Lego aka kera ban da tayoyi.

An fara gwajin wata mota mai aiki da iska maimaikon man fetur ko gas, da ake kera da robar Lego a garin Melbourne na Australia inda take tafiyar kilomita 20 cikin sa’a guda.

Wani mutumin Australia ne ya kera motar tare da hadin gwiwar wani masanin kere-kere dan Romania wanda ya yi amfani da bulo na roba na wasa da ake kira Lego guda 500,000 wurin hada motar.

Motar ta na amfani ne da injina hudu dake aiki da iska.

Komai a jikin motar har da injinan an yi su ne da robobin Lego in ban da tayoyi.

Injin motar na aiki ne da iska maimakon mai ko gas

Dan Australia Steve Sammartino ya ce ta intanet ya hadu da Raul Oaida dan Romania wanda ya shaida ma sa kudirinsa na kera motar.

Ya kara da cewa ya shiga shirin ne saboda aniyarsa ta karfafawa matasa gwiwa a fagen fasahar kere-kere, sai dai kuma ba shi da kudin da zai dau nauyin aikin.

A kan haka ne ya aike da sakon twitter inda ya bukaci mutane 20 da za su sa jarin $500-$1,000 a harkar.

‘Yan Australia 40 ne suka aiko da kudinsu, abinda ya ba su damar fara aikin.

An nuna fasaha

Sai dai kera motar ya dauke su watanni 18 da kuma dimbin kudin da su ka zartar abinda suka samu da farko, in ji Sammartino.

Shi da Raul Oaida suka kera motar a Romania sannan suka aike da ita Australia inda nan ma suka sake yi mata garambawul.

Mr Sammartino ya shaidawa BBC cewa: ” Mun tukata a garin Melbourne. Injin ba shi da kwari tun da na roba ne don haka babu fargabarmu ita ce ka da ya yi bindiga ya tarwatse.”

Mataimakin editan mujallar motoci ta Autocar, Matt Saunders ya ce: “Kera wanann mota ba karamin aiki ba ne, balle a yi batun sa ta tayi tafiya. Musamman ma injin, lalle an nuna fasaha.”

“Sai dai ban ga alamar za ta yi dadin tukawa ba, kuma ba zan so in tuka ta da nisa ba. Ko kuma in yi karo da ita.”

Daga BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img